Champions League: Ƙungiyoyin da suka kai zagayen 16 da waɗanda suka gaza

Zakaru

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A yau Juma'a, 30 ga watan Janairu ne za a tsara jawadalin wasannin cike-gurbin tsallakawa wasannin ƴan 16, wato zagaye na biyu gasar cin kofin zakarun turai ta kakar bana.

A ranar Laraba da ta gabata ce aka fafata wasan ƙarshe na wasan rukuni ne gasar zakarun turai ta bana.

Babban wasa da ya ja hankali a dare shi ne wasan Benfica da Real Madrid, inda ƙungiyar da Jose Mourinho ke horaswa ta doke Madrid.

Benfica na neman nasara ne a wasan da ƙwallaye da yawa, kuma abin da suka samu ke nan, inda ƙungiyar ta Benfica ta doke Madrid da ci huɗu da biyu.

Amma babban abin da ya ja hankali a wasan shi ne yadda mai tsaron gidan Benfica, Anatoly Trubin ya zura ƙwallo ta huɗu, wadda ta ba ƙungiyar nasarar tsallakawa wasannin cike-gurbi.

A ɓangaren Madrid kuwa, wannan rashin nasarar ce ta hana ƙungiyar samun tikitin tsallakawa zagaye na gaba kai-tsaye.

Lokacin da mai tsaron ragar Benfica Anatoliy Trubin ya zura ƙwallo a ragar Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da mai tsaron ragar Benfica Anatoliy Trubin ya zura ƙwallo a ragar Real Madrid

Ɗayan wasan da ya ja hankali shi ne Napoli da Chelsea, inda Chelsea ta doke Napoli da ci uku da biyu.

A daren na Laraba ne ƙungiyoyin Ingila suka nuna ƙwanji, inda ƙungiyoyi guda biyar cikin shida suka samu tikitin zuwa zagaye na gaba kai-tsaye.

Arsenal ce ta farko a teburin, sai Liverpool da take ta uku, da Tottenham a ta huɗu sai Chelsea da take ta shida, da Manchester City da ta ƙare a ta takwas. Sannan maki ɗaya ne kawai ya hana Newcastle ya tsallakawa, inda ta faɗa wasannin cike-gurbi bayan kunnen doki da PSG ta Faransa.

Idan Newcastle ta samu nasara a wasan cike-gurbin, zai zama dukkan ƙungiyoyin Ingila guda shida sun tsallaka zagayen wasannin ƴan 16, wanda kuma zai zama shi ne na farko a tarihi.

Ƙungiyoyin da suka tsallaka kai-tsaye

Tottenham Hotspur ta ƙara wasannin rukuni a matsayin ta huɗu a teburi duk da cewa ita ce ta 14 a teburin Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tottenham Hotspur ta ƙara wasannin rukuni a matsayin ta huɗu a teburi duk da cewa ita ce ta 14 a teburin Premier

Ƙungiyoyin da suke tsallaka kai-tsaye su ne:

  • Arsenal
  • Bayern Munich
  • Liverpool
  • Tottenham Hotspur
  • Barcelona
  • Chelsea
  • Sporting Lisbon
  • Manchester City

Ƙungiyoyin da za su buga wasannin cike-gurbi

Teburi

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Ƙungiyoyi 16 da suka ƙare a tsakanin mataki na 9 zuwa 24 a teburin ne za su fafata da juna domin cike-gurbin ƙungiyoyin da za su buga wasannin zagayen ƴan 16. Ƙungiyoyin su ne kamar haka:

  • Real Madrid
  • Inter Milan
  • Paris Saint German
  • Newcastle United
  • Juventus
  • Athletico Madrid
  • Atalanta
  • Bayer Leverkusen
  • Borussia Dortmund
  • Olympiacos
  • Club Brugge
  • Galatasaray
  • Monaco
  • Qarabag
  • Bodo Glimt
  • Benfica

Za a tsara jawadin wasannin cike-gurbin ne a ranar Juma'a 30 ga watan Janairun 2026.

Yadda za a fatata wasannin shi ne, ƙungiyoyin da suka ƙare tsakanin mataki na 9 zuwa na 16 za su kasance a rukuni ɗaya, sannan waɗanda suke mataki a 17 zuwa 24 suna wani rukunin.

Sai a fafata tsakanin rukunin farko da na biyu. Misali, ƙungiyoyi na 15 da 16 za su fafata da ƙungiyoyi na 17 da 24.

Sai dai rukunin farko za su buga wasanninsu na biyu ne a gida.

Me zai biyo baya?

Bayan kammala wasannin cike-gurbin guda takwas, sai a haɗa su da sauran ƙungiyoyi 8 ɗin da suka tsallaka kai-tsaye.

Daga nan ne za a fafata wasannin ƴan 16, zuwa matakin kwata fainal sai wasan gab da na ƙarshe sai kuma wasan ƙarshe bi da bi.