Wace illa takarar Jonathan a PDP za ta iya yi wa ADC?

Asalin hoton, AFP
Masu fashin baƙi a Najeriya na ta tattauna batun da ke jan hankali a siyasar ƙasar na bayanai da ke nuna babbar Jam'iyyar adawa ta PDP na lallamin tsohon shugaban ƙasar, GoodLuck Jonathan domin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Mista Jonathan ya ja baya a harkokin siyasa tun da ya fadi zabe a 2015, kuma jam'iyyar PDP ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da shi domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa don kalubalanar shugaba Bola Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Wasu masana na ganin cewa wannan mataki ne na gurgunta tafiyar haɗakar wasu manyan yan'adawar ƙasar kamar jam'iyyar Haɗka ta ADC.
Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja na ganin cewa idan dai har Goodluck Jonathan ya amince zai yi takarar kuma ƴan jam'iyyar suka ba shi ba tare da hamayya ba sannan aka gwama shi da mataimaki daga arewacin ƙasar to hakan alamu ne cewa za a yi karan-batta a zaɓen 2027.
''Idan har Goodluck ya yi takara kamar ya sake fesa rai ne ga jam'iyyar PDP wadda ga dukkan alamu ta yi dogon suma. Haka nan kuma ina ganin takarar Goodluck Jonathan za ta zamo cikas ga masu yunƙurin yin haɗaka saboda har zuwa yanzu su ne suke tunanin cewa za su zama tunga ta adawa.''
Akwai kuma wasu rahotannin na daban da ke cewa wasu jagororin jama'iyyar hamayyar ta PDP suna ta ganawa da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin zawarcin shi zuwa jama'iyyar, don ya yi takarar tare da Jonathan a matsayin mataimaki.
Me ya sa PDP ke zawarcin Jonathan?
Majiyoyin sun shaida wa BBC cewa jam'iyyar ta PDP a hukumance, da kuma a matakin wasu jiga jigan ta, ciki har da gwamnoni ne ke wannan yunkuri na zawarto tsohon shugaban Najeriyar, Good Luck Ebele Jonathan dominn ba shi takara a jama'iyyar a zaben 2027.
Malam Ibrahim Abdullahi, wanda shi ne mataimakin sakataren yaɗa labaran jam'iyyar ta PDP, ya kuma tabbatar da wannan yunƙuri yana mai cewa tsohon shugaban Najeriyar ya nuna yiyuwar amincewa da wannan buƙata.
Ya ce yunƙurin nasu na bai wa Jonathan takara amsa kiran da ƴan Najeriya suka yi masu ne na dawowa da tsohon shugaban ƙasar saboda a yanzu an yi walƙiya kuma jama'a sun fahimci kuskuren da suka tafka a baya na ƙin zaɓen Jonathan.
''Abubuwan da shi wannan bawan Allah ya yi a lokacin da yake mulki shi ya sa muke ganin babu laifi, tunda yana PDP har yanzu to a sake nemo shi, tunda ƴan Najeriya sun fahimci abubuwan da suka faru baya ba laifin shi ba ne har suna ba shi haƙuri cewa don Allah ya zo ya cece su, kuma sun gane cewa mutum ne mai tausayi.
''Mu kuma da yake muna biyayya ne ga ƴan Najeriyar kuma su muke son mu kyautata wa, sai muka ga ya kamata abin da suke kira mu ma mun saurare shi kuma an yi kira gare shi,'' In ji Malam Ibrahim Abdullahi.
Ko Janathan zai amince?

Asalin hoton, @GEJonathan
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa wasu jiga jigan jama'iyyar ta hamayya ta PDP ne suka bi Mista Jonathan har ƙasar Gambia a makon da ya gabata, duk dai domin neman shawo kansa ya amince ya yi masu takara a 2027 domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu.
Kuma Malam Ibrahim Abdullahi, ya ce tsohon shugaban Najeriyan ya nuna alamun amincewa da wannan buƙata tasu, har ma ya gindaya wasu sharuɗɗa.
''Ya fara sauraron mutanen kuma ya fara bayar da sharuɗɗa da suka shafi ko za a haɗa shi takarar sharar fage tare da wasu, ko kuma da gasken ake an fahimci ingancinsa na tsayawa zaɓe sannan kuma yana tuntuɓar mutanensa da ke ba shi shawara.'' In ji Malam Ibrahim.
Ko ƴan Najeriya za su yi maraba da Jonathan?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, ƴan Najeriya da dama har ma da ƴan arewacin ƙasar musamman matasa ke ta yin kiraye-kiraye a kafafen sada zumunta cewa a "dawo musu da Jonathan ɗinsu", sakamakon tsananin rayuwa da ƴan Najeriyar suka shiga a lokacin.
Mutane da dama na yi wa Goodluck Jonathan kallon mai tausayi idan aka kwatanta shi da sauran shugabannin da suka biyo bayansa.
Wani abu da ya ƙara wa tsohon shugaban farin jini a tsakanin ƴan Najeriya shi ne halin dattako da ya nuna kasancewarsa shugaban Najeriya na farko da ke mulki wanda ya amince da shan kaye sannan kuma ya miƙa mulki cikin sauƙi.
Ana ganin babban dalilin da ya sa PDP take son fito da Jonathan a PDP domin ƙalubalantar shugaba Tinubu shi ne kasancewarsa daga kudancin Najeriya, yankin da shi ne zai fito da shugaban ƙasa na gaba bisa tsarin karɓa-karɓa.
Wani ƙarin batun kuma da ka iya ba shi damar kama zukatunsu kasancewarsa wa'adi ɗaya zai yi tunda ya yi a baya kuma abin da hakan ke nufi shi ne idan ya kammala zai miƙa mulki ga Arewacin yankin.











