'Ina sana'ar jari bola ne domin samun kuɗin zuwa makaranta'
Umar Harun, yaro mai shekara 16 a Kaduna da ke Najeriya ya zaɓi yin sana'ar jari-bola domin taimaka wa iyalinsa da abin da za su ci.
Ya ce ya ajiye karatu saboda matsi na tattalin arziƙi.
Misali ne na miliyoyin yara da ke gararamba a titunan Najeriya ba tare da zuwa makaranta ba saboda rashin ƙarfin iyayensu.
Umar ya ce tun da asubahi yake fita tare da abokan sana'ar tasa domin shafe tsawon kilomitoci wajen neman ƙarafuna a gefen titi domin ya rufawa kansa da iyayensa asiri.
Ya ce da wannan kuɗi ne muka cin abinci da sauran bubuwan buƙatun rayuwa.
''Sai mun fita mun samo sannan ake samun abin da ake dafawa a gidanmu, duk ranar da ban fita wannan sana'a ba, to ba za a ci komai ba a gidanmu'', in ji shi.
Yaron ya ce mahaifinsa ya shefe fiye da shekara 10 yana fama da jinya, haka ma babban yayansa, don haka dole ɗawainiyar gidan ta koma kansa.
''Ƙannena su yara ne abin da nake kawowa idan yayi saura da shi ake biya musu kudin makarantar islamiyya, kodayake ta boko ma ta gwamnati suke zuwa'', in ji Umar.
Yaron ya ƙara da cewa h alin da gidansu ke ciki ne ya sa ya haƙura da karatu ya koma nema wa iyalinsa abin da za su ci su kuma biya sauran buƙatun rayuwa.
Umar ya ce a duk lokacin da ya fita sana'arsa ya kuma ci karo da yaran da ke zuwa makaranta sai ya ji yana sha'awar hakan, inda zuciyarsa ke cike da burin watarana shi ma ya samu ya koma makaranta.
''Bana jin daɗi a zuciyata idan na ga abokaina suna zuwa makaranta ni kuma babu halin hakan'', in ji shi.
''A halin yanzu idan na ce zan koma makaranta to za mu rasa abin da za mu ci a gidanmu''.
Umar ya ce ya kafin ɗawainiyar gidansu ta hau kansa ya samu kammala makaratar Firamare.
Ya ƙara da cewa idan da zai samu dama zai koma makaranta, domin cika burinsa na kammala digiri domin zama babban injiniya.












