Wane ɗan siyasa ne zai iya lashe ƙuri'un Arewa a 2027?

Ƴan takara
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
  • Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin da ƙurar siyasar Najeriya ke tashi, musamman batun babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027, hankali ya fara komawa kan yadda manyan ƴan siyasar ƙasar ke rububin ƙuri'un sassan ƙasar.

A tarihin siyasar Najeriya, ƴan siyasa suna tsare-tsare da bibiyar sassan ƙasar domin jan hankalin mutane su zaɓe su a zaɓe, inda yawanci a kan samu haɗakar ɓangarorin ƙasar domin samun nasara a zaɓe.

A Najeriya, akwai arewa da kudu, sannan akwai yankunan arewa maso yamma da maso gabas da tsakiya, sannan a kudancin ƙasar ma akwai kudu maso kudu da kudu maso gabas da kudu maso yamma, inda wasu lokutan ƴan siyasa sukan tsara yadda za su jawo ƙuri'un yankunan domin lashe zaɓe.

Sai dai yankin arewacin ƙasar ce ta fi tarin jama'a da tarin ƙuri'u, wanda hakan ya sa yawancin ƴan takarar shugaban ƙasar ke rububin ƙuri'un yankin domin samun nasara a zaɓen, duk kuwa da cewa babu wani yanki daya tilo da zai iya bai wa dan takara nasara.

Wannan ya sa ƴan Najeriya suke tafka muhawara musamman a kafofin sadarsa kan wane ɗan siyasa ne zai fi samun ƙuri'un arewacin Najeriya?

Akalar ƙuri'un arewa

A game da yadda ake tunanin akalar ƙuri'un yankin za ta juya, Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna, KASU kuma mai nazarin kimiyyar siyasa a ƙasar ya ce akwai wahala a yanzu a iya gane wanda zai fi samun ƙuri'un yankin a zaɓen mai zuwa.

"Amma bisa la'akari da yanayin da yankin ke ciki a yanzu, ina ganin ƴan yankin za su fi mayar da hankali ga duk mutumin da zai tabbatar musu da tsarin tabbatar da adalci da inganta aikin gona saboda idan aka lura za a ga yankin na shiga cikin wani hali mara kyau a ɓangaren noma," in ji shi.

Ya ce ƴan yankin za su fi mayar da hankali ne kan wanda suke ganin zai magance musu matsalolin da suke fuskanta, sannan suka gamsu da manufofinsa da tare-tsarensa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce akwai hanyoyin da aka gyara a yankin, amma "duk da akwai hanyoyin da aka gyara, amma misalin mutumin Kaduna zuwa Jos, zai faɗa maka matsalar hanya, da hanyar Noman zuwa Jalingo da sauran hanyoyin yankin da suke cikin matsala. Ina ganin waɗannan su ne abubuwan da za su sauya akalar ƙuri'un."

A nasa ɓangaren Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano ya ce kowane ɗansiyasa na da damar yagar abin da zai iya yaga daga ƙuri'un yankin a zaɓe mai zuwa.

"Tun bayan saukar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ake hasashen ba za a sake samun dunƙulewar ƙuri'un arewa a wuri guda ba. An fi hasashen ƙuri'un arewa za su barbazu ne, ba su taru a guri guda ba kamar yadda ya faru a zaɓen 2023," in ji shi.

Sufi ya ce an fi tunanin irin haka za a samu a zaɓe mai zuwa, na barbazuwar ƙuri'un zuwa ga ƴan siyasar yankin.

A cewarsa, "akwai ƴan arewa da suke son mulki, akwai kuma waɗanda ba ƴan arewa ba, kuma dukkansu kowa na da wani ƙarfi da yake da shi a arewa, da kuma wani rauni. Don haka akwai yiwuwar abin da ya faru a babban zaɓen 2023 ne za a maimaita."

"Don haka zuwa yanzu ba za a gane ba sai nan gaba ko idan an samu wa dunƙulewa zai yi wahala ƙuri'un arewa su haɗe guri ɗaya kamar na 2015 da 2019. Za su cigaba da barbazuwa shi ya sa kowa yake ta ƙoƙarin yagar abin da zai iya yaga."

Abubuwan da za su juya akalar ƙuri'un

A game da yadda ake tunanin akalar ƙuri'un yankin za ta juya, Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna, KASU kuma mai nazarin kimiyyar siyasa a ƙasar ya ce akwai wasu muhimman abubuwa da yake tunanin za su yi tasiri matuƙa wajen samun ƙuri'u daga arewacin Najeriya, kamar yadda ya shaida wa BBC Hausa:

  • Rashin tsaro
  • Inganta harkokin tsaro
  • Gyara hanyoyin yankin

Farfesa Abdulƙadir ya ce idan ƴan yankin suka samu wanda suke tunanin zai inganta musu waɗannan abubuwan, za su fi mayar da hankali wajen zaɓen shi.

Sai dai ya ce gwamnati mai mulki tana da damar samun ƙuri'ar yankin, "idan ta tunkari matsalolin da yankin ke fuskanta kai-tsaye ba tare da farfaganda ba," in ji shi.

Yankin arewa dai na fama da wasu matsaloli musamman rashin tsaro, wanda ya shafi harkokin noma da kiwo da rashin sauran ababen more rayuwa, wanda hakan ya sa wasu ƴan yankin suke ganin ana barin su a baya wajen sharɓar romom dimokuraɗiyya, duk da ɗimbin ƙuri'un da suke da su.