Me ya sa ake zanga-zanga a Turkiyya kuma su wane ne ke yin ta?

Masu zanga-zanga sun kunna wuta a lokacin zanga zangar ranar 23 ga watan Maris na 2025 a Ankara, babban birnin Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Lara Owen & BBC News Turkish journalists
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 9

Kama Ekrem Imamoglu - Magajin garin Istanbul wanda shi ne birni mafi girma a Turkiyya, kuma babban ɗan takarar shugaban ƙasa - ya janyo zanga-zanga mai girma a faɗin ƙasar, ya kuma tayar da ƙura a duniya kan matsayin dimokradiyya a ƙasar.

Me ya sa ake zanga-zanga a Turkiyya?

A matsayinsa na jagora a jam'iyyar adawa ta Republican People's Party (CHP), kuma magajin garin Istanbul, an daɗe ana kallon Imamoglu a matsayin babban ɗan adawar shugaba Recep Tayyip Erdogan.

A ranar 23 ga watan Maris ne aka tuhume shi a hukumance da laifin cin hanci da rashawa da kuma taimaka wa ƙungiyar ta'addanci.

Waɗanda suka bazama kan tituna na ganin cewa kama Imamoglu ba komai ba ne face siyasa.

A kafafen sada zumunta, Imamoglu ya wallafa cewa: '' Wannan take haƙƙin ƴancin mutane ne.''

"Ɗaruruwan ƴansanda sun iso gidana. Na barwa alumma amanar kai na,'' in ji shi.

Wani mai zanga-zanga sanye da abin kulle hanci a yayin da ƴansanda ke fesa abu mai yaji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga sanye da abin kulle hanci a yayin da ƴansanda ke fesa abu mai yaji

Alkalai sun yanke hukuncin ƙin gabatar da takardar izinin kama shi kan zargin laifin taimaka wa ƙungiyar PKK, wata ƙungiyar Kurdawa da ke yaƙar Turkiyya tun shekarun 1980.

Turkiyya da Amurka da Birtaniya na kallon ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda kuma sun haramta ta.

Magajin garin Istanbul Ekrem Imamoglu ya na jawabi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Magajin garin Istanbul Ekrem Imamoglu ya na jawabi

Su wane ne masu zanga-zangar?

Wata mai zanga-zanga da ta kulle fuskarta ɗauke da takarda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mai zanga-zanga riƙe da takarda da aka rubuta 'No Recep No Cry'

Tun bayan kama Imamoglu, dubun dubatar masu zanga-zanga sun bijire wa haramcin da gwamnati ta yi na gudanar da duk wata zanga-zanga.

A ranar litinin, Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya ce an kama aƙalla mutane 1,133.

Akasarin masu zanga-zangar ɗalibai ne waɗanda ba su san mulkin kowa ba illa na shugaba Erdogan.

Ya shafe shekara 22 yana mulki, a matsayin Firaminista da kuma shugaban ƙasa.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya na magana a kan dandamali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya musanta zargin cewa kama Imamoglu saboda siyasa ne

Sun ci gaba da fita zanga-zangar duk da barazanar kama su da kuma arangama da ƴansanda.

Da ya ke magana game da kundin tsarin mulki, Yerlikaya ya ce zanga-zangar da aka yi a kwanakin bayan nan sun saɓa dokokin yin zanga-zanga, inda ya zargi masu yin zanga-zangar da ''ƙoƙarin haddasa husuma da kuma kai hari kan ƴansanda''.

Ƴansanda sun hana masu zanga-zanga zuwa dandalin Taksim ba tare da neman umurni ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴansanda sun hana masu zanga-zanga zuwa dandalin Taksim ba tare da neman umurni ba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An gudanar da zanga-zanga a aƙalla larduna 55 cikin 81 da ke Turkiyya, ko kuma fiye da kashi biyu cikin uku na ƙasar, a cewar alƙaluman kamfanin dillancin labaran faransa AFP.

''Muna da damar zaɓen duk wanda mu ke so ya mulke mu, amma shugaban Erdogan na ƙoƙarin ƙwace ikon mu na yin hakan a yau,'' kamar yadda wata mai zanga-zanga ta shaida wa BBC.

''Muna son tsarin dimokuraɗiyya,'' wani matashi ya bayyana. ''Muna son mutane su zaɓi wanda suke so. Kuma muna son ƴancin zaɓen wanda muke so ba tare da an kama shi ba.''

An soma gudanar da zanga-zangar cikin lumana, inda masu zanga-zangar ke ɗauke da takardu da ke yi wa shugaban izgili ko kuma buƙatar adalci.

Sai dai daren Lahadi ya samu ƙaruwar tashin hankalin da aka shafe fiye da shekara goma ba a samu ba irinsa ba.

Jam'ian tsaro sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye da yajin da ake fesawa da harsasai na roba kan masu zanga-zangar.

Akasarin masu zanga-zangar sun sanya abin rufe hanci na N95 ko kuma ɗankwali kan fuskokinsu domin kare kansu.

Me ya sa aka kama Ekrem Imamoglu?

Wani mai zanga-zanga sanye da hoton fuskar Imamoglu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga sanye da hoton fuskar Imamoglu

Masu sanya ido sun ce zaɓen fidda gwani na jam'iyyar adawa da ke kusantowa shi ne ya sa aka kama Imamoglu.

An shirya yin zaɓen jam'iyyar CHP a ranar 23 ga watan Maris. Ana sa ra zaɓen Imamoglu a matsayin ɗan takarar jam'iyyar adawa domin yin takara da shugaba Erdogan a shekarar 2028.

Zuwa daren Lahadi, mutane miliyan 15 sun hau kan layi suna jiran su kaɗa ƙuri'a na goyon bayan Imamoglu domin tabbatar da shi. Duk da yana can ana riƙe dashi gabanin zaman shari'a.

Duk da haka akwai buƙatar a hukumace a tabbatar da zaɓensa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Shugaban jam'iyyar CHP Ozgur Ozel (a hannun hagu) yana jawabi ga magoya bayan Imamoglu.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar CHP Ozgur Ozel (a hannun hagu) yana jawabi ga magoya bayan Imamoglu.

Da ya ke jawabi a wani gangami a istanbul, shugaban jam'iyyar CHP Ozgur Ozel ya ce aƙalla ƙuri'u miliyan ɗaya da dubu ɗari shida sun zo ne daga ƴan jam'iyyar, yayin da sauran kuma an kaɗa su ne bisa nuna haɗin kai.

Sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da waɗannan alƙaluman ba.

Wani mutum yana jefa takardarsa cikin akwatin zaɓe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴayan jam'iyyar CHP da waɗanda ba sa jam'iyyar sun kaɗa ƙuri'a

An sake zaɓen Imamoglu a matsayin magajin garin Istanbul a zaɓen yanki a bara, karo na biyu a jere yana cin zaɓe a birni mafi girma a Turkiyya.

Wasu masu fashin baƙi sun ce wannan ne matakin farko na ƙoƙarin jagorantar CHP.

Jam'iyyar ta soki kama shi inda ta ce '' ƙoƙarin juyin mulki ne kan shugaban ƙasa na gaba''.

Gwamnatin shugaba Erdogan ta musanta cewa kama imamoglu siyasa ce, inda ta nanata cewa kotunan Turkiyya na cin gashin kansu.

Ofishin mai gabatar da ƙara ya ce kotun ya yanke hukuncin kama Imamoglu ne bisa dogon jerin zarge-zarge, wanda suka haɗa da gudanar da ƙungiyar da ke aikata laifuka, karɓar cin hanci, tatsar mutane da saura.

A ranar Asabar, cikin wata sanarwa, Imamoglu ya musanta zarge-zargen da aka yi mishi, inda ya ce wa ƴan sanda kamashi ya yi tasiri mai muni kan mutuncin Turkiyya a idon duniya.

Shin Imamoglu zai iya ci gaba da zama ɗan takarar Shugaban ƙasa?

Hoton fuskar Ekrem Imamoglu

Asalin hoton, Reuters

Kama Imamoglu ba zai hana shi takara ba ko zama shugaban ƙasa.

Sai dai idan an kama shi da laifin ɗaya daga cikin laifuka da ake zarginsa da su, to ba zai iya takara ba.

A ranar 18 ga watan Maris, Jami'ar Istanbul ta soke digirin sa, wani mataki da idan aka tabbatar da shi, zai hana shi takara a zaɓen shugaban ƙasa.

A cewar kundin tsarin mulkin Turkiyya, wajibi ne shugaban kasa ya kammala karatun gaba da sakandire kafin ya iya riƙe muƙamin.

Ƴan sanda sun kama wani mai zanga-zanga a Ankara ranar 22 ga watan Maris

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ƴan sanda sun kama wani mai zanga-zanga a Ankara ranar 22 ga watan Maris

Matakin da jami'ar Istanbul ta ɗauka ya janyo damuwa ga ɗalibai game da makomarsu, a cewar wani ƙwararre a sashen BBC na Turkiyya Selin Girit.

Majalisar koli kan zaɓe na Turkiyya ce za ta yanke hukuncin ko Imamoglu ya cike ƙa'idar zaman ɗan takara.

Erdogan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa karo na uku a 2023.

Bisa kundin tsarin mulki, ba zai iya kasancewa shugaban ƙasa ba bayan 2028. Sai dai masu sharhi na cewa akwai yiwuwar zai sauya kundin tsarin mulkin wanda zai bashi damar ƙara wa'adi kan mulki.

An shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a 2028, sai dai ana hasashen yin zaɓen kafin nan.

Zanga-zanga a wajen Istanbul ranar 19 ga watan Maris

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zanga-zanga a wajen Istanbul ranar 19 ga watan Maris

Su wane ne kuma aka kama a Turkiyya?

Ana kallon kamen da aka yi a baya bayan nan a mastayin ta'azarar murƙushe ƴan adawa da kuma dakushe muryoyin su.

A ranar Litinin, ƴan sanda sun kama lauyoyi da ƴan jarida da dama a wani samame da suka kai biranen Istanbul da Izmir.

A cewar wata ƙungiyar kare ƴancin ƴan jarida na Turkiyya MLSA, an kama ƴan jarida 10 a samamen waɗanda ke ɗaukar rahotanni kan zanga zangar, ciki har da fitaccen mai ɗaukar hoto Bulent Kilic da mai ɗaukar hoto na AFP Yasin Akgul.

23 Maris 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Waɗanda ake zargi da aka kama a bincike rashawa da ta'adanci ciki har da Ekrem, an aika su gidan yari

Hukumomin kafar yaɗa labaran Turkiyya sun buƙaci kafafen yaɗa labarai su dogara kan sanarwa da hukumomi ke fitarwa kawai, suna gargadinsu kan cewa rashin yin hakan laifi ne da ka iya kai wa ga ƙwace lasisinsu.

A ƙarshen makon da ya gabata, shafin sada zumuna na X ya ce zai ɗaukaka ƙara kan dokar da kotun Turkiyya ta bayar na rufe shafuka 700, inda suka ce matakin ya 'saɓa doka'.

A ranar Litinin, shugaban jam'iyyar adawa ta CHP ya wallafa a shafinsa na X cewa:

''A yau suna ƙoƙarin daƙile shafukan sada zumunta,''

''Ka amince Mista Tayyip cewa ba za ka iya danne muryoyin mutane ba.'' in ji shi.

A wani wurin kuma ya yi kiran a ƙauracewa shafukan sada zumunta da suka ƙi yin labari kan zanga-zangar.

Me ya sa aka kai Imamoglu gidan yarin Marmara?

Jerin motoci da ke hanyar zuwa gidan yarin Marmara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An aika mutane 51 gidan yari a ranar 23 ga watan Maris a lokacin bincike kan zargin rashawa da ta'addanci

Gidan yarin da aka kai Imamoglu mai suna Marmara, a baya an san shi ne da sunan gidan yarin Silivri.

Akan bayyana shi a matsayin gidan yari mafi girma a Turai, wanda aka tsara domin ya kwashi fursunoni 11,000.

Sai dai a cikin wani rahoto kan gidan yarin da hukumar bincike kan haƙƙin biladama na Majalisar Turkiyya ta fitar a 2019, ya ce gidan yarin na ɗauke da fursunoni 22,781.

A tsakanin matasa da kuma a wasu kafafen sada zumunta, kalmar ''Silivri na da sanyi' ana amfani da ita wajen tsokana, ma'ana kamar wani gargaɗi ne ga waɗanda ke sukar gwamnati.

A shekaru goma da suka gabata, a lokuta da dama an aika jam'ian sojin Turkiyya masu manyan muƙamai, da ƴan jarida da kuma ƴan majalisa gidan yarin.

Lauya Hüseyin Ersöz na da mutanen da ya kare da suke gidan yarin Silivri tun shekarar 2008.

Ya shaidawa BBC cewa waɗanda ake tuhumar su da manyan laifuka ana sa su a ɗaki na 9, inda ake sanya fursunoni aƙalla uku a ciki.

Me ake faɗi a yanzu?

Wani mai zanga zanga yana karanta littafin Erdogan a gaban shingen ƴansanda a yayin da masu zanga zanga ke ƙoƙarin isa dandalin Taksim

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga yana karanta littafin Erdogan a gaban shingen ƴansanda a yayin da masu zanga-zanga ke ƙoƙarin isa dandalin Taksim

Shugaba Erdogan ya fitar da wata sanarwa da ya karanto a kafar talibijin bayan taron muƙarraban gwamnati a yammacin Litinin.

Ya yi alla wadai da zanga-zangar da ake ta yi, kuma ya zargi jam'iyyar CHP da 'cutar da ƙasar da suka yi''.

A gefe guda kuma, jagoran jam'iyyar CHP Ozgur Ozel ya zargi Erdogan da cin zarafin ba Imamoglu kaɗai ba har ma da miliyoyin ƴan Turkiyya. Jam'iyyar ta kuma zargi gwamnati da ƙoƙarin 'yin juyin mulki''.

Ƙawayen Turkiyya na ƙasashen yammaci ba suyi magana sosai ba kan tashin hankalin.

Shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado Olaf Scholz, ya bayyana damuwarsa kan kama Imamoglu, inda ya bayyana hakan a matsayin '' kawo cikas da dimokraɗiyya a Turkiyya''.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce matsalar cikin gida ce, kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

Hukumar Tarayyar Turai ta buƙaci Turkiyya ta 'tabbatar da tsarin dimokraɗiyya'' a matsayinta na ƙasar da ke majalisar Turai kuma mai neman shiga ƙungiyar Tarayyar Turai.