Ana zaɓen magadan gari a Turkiyya

Mata magoya bayan Erdogan a Turkiyya

Asalin hoton, NECATI SAVAS/EPA-EFE

A Turkiyyya ana fara jefa ƙuri'a a zaben shugabannin manyan birane na ƙasar, inda jam'iyar shugaban kasar ke fatan sake samun nasarar da ta rasa shekara biyar da ta gabata.

Hankali ya fi karkata ga birnin Istanbul wanda ke da kusan kashi biyar na yawan al'ummar kasar, kusan miliyan 85.

Ana kuma takara ne tsakanin magajin garin na yanzu, dan hamayya, Ekrem Imamoglu da kuma wani tsohon minista, Murut Kurum.

Miliyoyin masu kada kuri'a da ke zaben na Lahadi za su samar da shugabannin da za su jagoranci manyan biranen kasar, tare kuma da nuna cewa ko Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai sake karbe iko daga hannun ‘yan hamayya.

Idan har ‘yan hamayya suka yi nasara to ana ganin hakan zai sanya kasar ga wata sabuwar alkibla.

Kuma hakan zai zama babban kalubale ga Shugaba Erdogan da jam'iyyarsa ta AK, wadda shekara da shekaru ta kankane iko.

Zaben ya fi daukar hankali a birni mafi yawan al’umma Istanbul, inda daga nan ne shi kansa Erdogan ya yo fice a fagen siyasar kasar, bayan ya zama magajin garin a shekarun 1990 inda daga bisani likkafarsa ta yi gaba ya zama shugaban kasa.

A yanzu ya tashi haikan wajen ganin dan takarar jamiyyarsa ta AP Murat Kurum, tsohon ministan muhalli da birane mai shekara 47, ya kayar da magajin garin mai-ci, Imamoglu, wanda nasararsa a wancan zaben shekara biyar baya, ta daburta lissafin kaka-gidan da Mista Erdogan ya dade yana yi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Saboda haka ne a yanzu Shugaba Erdogan wanda haifaffen birnin ne mai mutum miliyan 16, inda nan ya taso yana tallar burodi kafin ya fada siyasa a shekarun 1970, yake son ganin jam'iyyarsa ta sake dawo da ikon birnin mai matukar tasiri a siyasar kasar hannunta.

Sakamakon zaben na Istanbul zai kasance wani madubi ko manuniya kan ko 'yan hamayya za su iya ci gaba da zama barazana ga Mista Erdogan da jam'iyyarsa a zaben shugaban kasa na gaba shekara hudu mai zuwa.

Babbar jam'iyyar hammaya ta CHP na son ganin ta yi nasara a zaben ba a Istanbul ba kadai har da Ankara babban birnin kasar da birnin yawon bude idanu na Antalya.

A shekarar da ta gaba ne Shugaba Erdogan ya yi nasara a zabensa na wa'adi na uku, wanda shi ne wa'adinsa na karshe a bisa tanadin kundin mulkin kasar, domin ba zai wuce 2028 ba.

Kuma har yanzu bai bayyana magajinsa ba, wanda masana ke ganin abu ne mai wuyar gaske.

Saboda haka ne wasu ke ganin shugaban zai so jam'iyyarsa ta karbe iko da Istanbul domin ya samu damar sauya kundin tsarin mulkin don ya kara takara.

Tun lokacin da Erdogan ya kama mulki a Turkiyya shekara 20 da ta gabata, farko a matsayin firaminista, sannan ya zama shugaban kasa, yana ta nuna sha'awar mu'amulla da kasashen Afirka.