Wane ne Ekrem Imamoglu - babban abokin hamayyar Erdogan da aka kama kan rashawa?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Cagil Kasapoglu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
An tsare ɗaya daga cikin fitattun ƴansiyasar Turkiyya, Ekrem Imamoglu kan tuhume-tuhumen rashawa da kuma tallafa wa ƙungiyar ta'addanci. Babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar ta soki kamen da aka yi wa Imamoglu inda ta kira hakan a matsayin "yunƙurin juyin mulki ga shugaban ƙasa na gaba."
Imamoglu ya kasance jigo a jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party (CHP) kuma magajin garin Istanbul. An daɗe ana kallon shi a matsayin babban abokin hamayyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Imamoglu ya bai wa Shugaba Erdogan da jam'iyyarsa ta Justice and Development Party (AKP) mamaki lokacin da ya ci gaba da jan ragamar Istanbul a zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi bara, bayan da ya sake yin nasara karo na biyu jere a birni mafi girma na Turkiyya.
Masu sharhi kan al'amuran siyasa a Turkiyya sun bayyana hakan a matsayin "shan kaye mafi muni da Erdogan ya gani".
Babbar jam'iyyar hamayya CHP ba wai kawai ta samu nasarar doke AKP mai mulki a birnin da ke kusa da cibiyar Erdogan a 2024, amma jam'iyyar ce ta samu ƙuri'u mafi yawa a ƙasar tun 1977, nasarar da galibi ake alaƙanta wa da irin tasirin Imamoglu a Turkiyya da kuma yadda jam'iyyun hamayya suka kafa haɗaka domin mara masa baya.
Rashin nasarar da ya samu a Mayun 2019, ta zo wa da jam'iyyar AKP da mamaki kuma Imamoglu ya fuskanci ƙalubale kan nasarartasa.
Hukumar zaɓe ta soke zaɓen tare da tilasta wa Imamoglu ya yi murabus bayan da AKP ta yi zargin an tafka maguɗi a zaɓen. An kuma bayar da umarnin a sake gudanar da zaɓe.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan sanar da cewa za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen Instanbul, Imamoglu ya yi wa dandazon magoya bayansa jawabi a wani gangami inda ya ɗage hannun rigarsa tare da cire jaket da nek tayin da ke wuyansa, yana kira ga magoya bayannasa da su karkatar da hankulansu ga yadda za su sake samun nasara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Komai zai tafi daidai," in ji shi, kalaman da suka zama takensa kuma ake yawan furtawa. Kuma a zahiri, komai ya tafi daidai ga Imamoglu musamman a zagaye na biyu na zaɓen inda ya samu kashi 55 cikin 100 na kuri'un, babban koma-baya ga Shugaba Erdogan. A yanzu, sau biyu ke nan Imamoglu na doke Shugaba Erdogan - a baya jam'iyyar AKP da waɗanda ta gada masu kishin Islama sun tsaya takarar mulkar Instanbul tsawon shekara 25.
A Instanbul Erdogan ya girma, inda yake sayar da burodi mai kantu kafin ya tsunduma siyasa a shekarun 1970. Ya fara daga ƙasa har ya kai muƙamin magajin garin Instanbul, ya zama Firaiminista sannan kuma ya zama shugaban Turkiyya.
Rashin nasararsa a birnin ta yi masa ciwo sannan ba ta yi wa jam'iyyarsa daɗi ba: Instanbul gida ne ga kashi ɗaya bisa biyar na al'ummar Turkiyya kusan miliyan 85 sannan ita ce ke bayar da gudummawa mai tsoka ga tattalin arzikn Turkiyya, har da ɓangarorin kasuwanci da yawon buɗe ido da kuma kuɗi.
Masana da dama sun yi hasashen irin wannan ɗaukaka ga Imamoglu bayan da ya sake cin zaɓe a Instanbul a 2024. Ga wasu, ya soma zama barazana ga muƙamin Ergogan a matsayin shugaban ƙasa.
A 2023, Erdogan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa karo na uku sannan a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar, ba zai iya wuce shekarar 2028 yana shugaban kasa ba. Sai dai masu suka sun ce wataƙila ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar domin ya kara neman zarcewa a matsayin shugaban ƙasa. A shekarar 2028 ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gaba.

Asalin hoton, EPA
An haifi Imamoglu a Akcaabat cikin shekarar 1971. Ya koma Instanbul da zama tun yana matashi ya kuma karanta fannin kasuwanci sannan kuma ya yi aiki a kamfanonin ƙere-ƙere.
Duk da ƴanuwansa sun kasance ƴan conservative, Imamoglu ya ce ya rungumi tsarin zaman lafiya a dimokraɗiyya a lokacin da yake jami'a".
Imamoglu ya kasance mai son kwallo kamar Shugaba Erdogan inda a lokacin da yake matashi ma ya buga ƙwallo kuma ya yi fice kan goyon bayan da yake nuna wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta garinsu Trabzonsor.
Bayan harkar kasuwancin da ya yi a ɓangaren ƙere-ƙere, Ekram Imamoglu mai shekara 53 a duniya ya yi tashe a matsayin magajin garin Lardin Beylikduzu na Instanbul, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin babbar jam'iyyar hamayya ta CHP.
Ya gamu da ɗaukaka mai cike da faɗi-tashi. Kuma zuwa yanzu babu tantama shi ne babban abokin hamayyar Erdogan.

Asalin hoton, Getty Images
A lokutan da yake yakin neman zaɓe, ya sha yabo kan yadda yake tafiyar da siyasar shi cikin natsuwa da ban dariya, abin da ya sha bamban da sauran ƴansiyar Turkiyya.
A ƙoƙarinsa na faɗaɗa CHP, Imamoglu ya samu yin kira ga wasu daga ƴan ƙasar da suka saba zaɓen jam'iyyar AKP ta Shugaba Erdogan, ya ziyarci masallatai kuma a baya-bayan nan ya sanar da farfaɗo da masallaci mai daɗaɗɗen tarihi da ke Lardin Karakoy a Instanbul.
Mai ɗakinsa Dilek Imamoglu ita ma ta shahara kasancewarta babbar ma'abociyar kafafen sada zumunta ce, tana tafiyar da ayyukan taimako ga mabuƙata kuma tana bayyana a kusa da mai gidanta inda take mara masa baya a lokutan yaƙin neman zaɓe. A yanzu, tana yin digiri na uku ne. Ma'auratan sun haifi ƴaƴa maza biyu da mace guda.

Asalin hoton, Getty Images
An tsara gudanar da zaɓen fitar da gwani a babbar jam'iyyar hamayyar ranar 23 ga Maris inda ake sa ran jam'iyyar za ta tsayar da Imamoglu a matsayin wanda zai mata takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2028.
A ranar 18 ga Maris ne, jami'ar Instanbul ta soke karatun da ya yi, matakin da idan aka tabbatar da shi, zai kawo cikas ga takararsa. A cewar kundin tsarin mulkin Turkiyya, dole ne a ce shugaban ƙasa ya kammala karun jami'a kafin ya riƙe muƙami. Imamoglu ya kira matakin mara tushe inda ya ƙara da cewa dole ne jami'oi su tsame kansu daga shiga harkokin siyasa su kuma himmatu a batun ilimi".
Washegari, a ranar 9 ga Maris kuma, gomman ƴansanda suka kai samame a gidansa da ke Instanbul domin tsare shi a wani ɓangare na binciken da ake kan zarginsa da rashawa.
Imamoglu ya wallafa wani bidiyo da ke nuna shi yana cewa "ba za a rufe bakin ƴan Turkiyya ba inda kuma ya yi alkawarin ya tsaya wa al'ummar Turkiyya tare kuma da yin riƙo da tsarin dimokraɗiyya da adalc a duniya."
Jam'iyyarsa ta CHP ta bayyana kama Imamoglu a matsayin "yunƙurin juyin mulki" domin "hana ƙasar zaɓen shugaban ƙasarta na gaba".











