Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ministocin Buhari da EFCC ke bincika
Rahotanni na nuna cewa EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya na tsare da tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige.
Ɗaya daga cikin tsofaffin masu magana da yawunsa, Fred Chukwuelobe, ya tababatar da cewa Ngige na hannun hukumar.
Sai dai EFCC ba ta tabbatar da tsarewar ba, sannan kakakin hukumar Dele Oyewole bai amsa saƙonnin da manema labarai suka aike masa ba game da batun.
Mista Ngige ne na baya-bayan nan da EFCC ke bincike cikin tsofaffin ministoci da manyan jami'an gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari game da cin hanci da rashawa.
Wannan maƙala ta duba huɗu daga cikinsu.
Abubakar Malami
Malami ne tsohon antoni janar kuma ministan shari'a na baya-bayan nan, wanda EFCC ke bincike game da zargin ɓatan wasu kuɗaɗe.
Kakakin hukumar Dele Oyewole bai taɓa magana a fili kan bincken Malami ba, amma tsohon ministan da kansa ya sha bayar da bayanai game da gayyatar da EFCC ke yi masa tare da musanta zarge-zargen.
A cewar Malami, zargin nasa ya samo asali ne daga batun dala miliyan 346 da ƙasar Switzerland ta mayar wa gwamnatin Najeriya, wanda ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha ya sace.
Malami ya ce EFCC na zargin sa ne da yin amfani da wasu kamfanonin shari'a wajen biyan su kuɗaɗe masu yawa domin taimaka wa yunƙurin dawo da kuɗaɗen duk da cewa yana sane gwamnatin da suka gada ta kusa kammala shirin gaba ɗaya.
A gefe guda, ya ce EFCC na zargin sa da halasta kuɗin haram. Ya musanta dukkan zarge-zargen.
Daga baya kuma Malami ya musanta zargin "ɗaukar nauyin ta'addanci" wanda ya ce wasu kafofin yaɗa labarai na yaɗawa.
"Na sha bayyanawa ƙarara cewa ba a zargi na ba, ko gayyata ta, ko bincika ta, ko tuhuma ta daga wata hukumar tsaro ba a Najeriya ko a wajen ƙasar game da ɗaukar nauyin ta'addanci ko wani abu mai kama da haka," in ji Malami cikin wata sanarwa.
A ranar Talata kuma Malami ya amsa gayyatar EFCC, inda ta tsare shi tsawon yini biyu, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.
Timipre Sylva
Timipre Sylva tsohon gwamnan Bayelsa ne da ke kudu maso kudancin Najeriya, kuma ya riƙe ɗaya daga cikin ma'aikatu mafiya muhimmanci a gwamnatin Buhari.
Shi ne ƙaramin ministan man fetur daga watan Agustan 2019 zuwa 2023, yayin da Buhari da kansa ya riƙe muƙamin ministan mai tun daga 2015 har zuwa 2023.
Duk da cewa Buhari ne babban minista, Mista Sylva ne ke kula da ayyukan ma'aikatar na yau da kullum, wadda ita ce babbar hanya mafi girma sosai ta samun kuɗin shiga a Najeriya.
A ranar 10 ga watan Nuwamban shekarar nan ne EFCC ta ayyana shi a matsayin wanda take nema bisa zargin almundahar kuɗi fiye da dala miliyan 14 - kwatankwacin naira biliyan 21.
A cewar hukumar, wata babbar kotun jihar Legas ce ta bayar da umarnin kama shi ranar 6 ga watan Nuwamba, kuma ta nemi 'yan Najeriya da su ba ta bayanan inda za ta iya kama shi.
Tun daga lokacin har zuwa yanzu babu tabbas game da inda tsohon ministan yake. Sai dai mai magana da yawunsa Julius Bokoru ya faɗa cikin wata sanarwa cewa EFCC ba ta taɓa gayyatar mai gidan nasa ba ballantana ta ce ya ƙi zuwa.
Wannan ne karo na biyu da Mista Sylva ke fuskantar bincike bayan musanta zargin hannunsa a yunƙurin juyin mulki.
Hadi Sirika
Hadi Sirika, shi ne tsohon ministan sufurin jiragen sama.
'Yan Najeriya ba za su manta da batun kamfanin NIgeria Air da Sirika ya ƙaddamar ba saura 'yan kwanaki wa'adin gwamnatinsu ya ƙare. Cecekucen da ya biyo bayan lamarin ya sa gwamnatin Tinubu ta soke kwantaragin kafa kamfanin.
"Babu wani abu mai suna Nigeria Air, maganar gaskiya kenan. Kawai sun yi wa jirgi fenti ne. Jirgin Ethiopian Airlines suka so su yi amfani da shi a madadin namu," a cewar Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo.
Yanzu EFCC ta gurfanar da Sirika a kotu game da kamfanin jirgin mallakar gwmnatin Najeriya.
Ta zarge shi da yin amfani da ofishinsa wajen yi wa 'yarsa Fatima da mijinta Jalal Hamma alfarmomi ta hanyar ba su aikin bayar da shawarwari a Nigeria Air, da kuma ba su kwangilar gina wani ɓangare na filin jirgi a Katsina.
Kotu ta bayar da belin tsohon ministan kan naira miliyan 100 kuma har yanzu batun na gaban kotu.
Godwin Emefiele
Emefiele ba minista ba ne, amma matsayinsa na gwamnan babban banki CBN yana cikin mafiya girman muƙami a fannin tattalin arzikin Najeriya.
Tun bayan barinsa ofis, lamarinsa na gaban kotu bisa zarge-zargen da suka shafi rashawa, da mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba, da halasta kuɗin haram.
A watan Disamban 2024 ne wata babbar kotu ta bayar da umarnin ƙwace wani rukunin gidaje mai gida 753 daga hannun Emefiele, waɗanda EFCC ke zargin ya gina su ne da kuɗin haram.
Har yanzu batun na gaban kotuna a Legas da Abuja.