Kuɗaɗe da kadarorin da kotu ta ƙwace daga tsohon gwamnan CBN, Emefiele

Lokacin karatu: Minti 3

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas, kudu maso yammacin Najeriya ta yanke hukunci na ƙarshe, inda ta ƙwace tare da miƙa wa hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya, EFCC, kuɗaɗe da kuma wasu kadarorin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Emefiele, wanda ya shafe shekara tara yana jagorancin Babban Bankin na Najeriya ya fara shiga tasku ne tun a watan Yunin shekara ta 2023, lokacin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sallame shi daga aiki.

A lokacin da take yanke hukunci, mai shari'a Yellim Bogoro ta amince da buƙatar da EFCC ta shigar ta hannun mai wakiltar ta, Bilkisu Buhari-Bala, bayan watsi da buƙatar da ɓangaren Emefiele ya shigar na dakatar da sauraron ƙarar.

A yanzu kotu ta mallaka wa EFCC kuɗin da aka ƙwace daga wurin Emefiele, dala miliyan 4.7 da naira miliyan 830, sai kuma wasu kadarori da dama.

Kuɗin da kotun ta mallaka wa EFCC, suna ajiye ne a bankuna daban-daban, da suka haɗa da First Bank, da Titan Bank, da kuma Zenith Bank ƙarƙashin sunayen wasu mutane da kuma kamfanoni.

Kadarorin da kotu ta ƙwace

Mafi yawan kadarorin da kotun ta miƙa wa hukumar EFCC suna a jihar ta Legas ne, waɗanda suka haɗa da:

  • Gini mai hawa 11 - Ikoyi, Legas
  • AM Plaza, mai hawa 11, Lekki Peninsula 1, Legas
  • Imore Industrial Park, Ƙaramar hukumar Amuwo Odofin, Legas
  • Mitrewood and Tatler Warehouse, Ibeju-Lekki, Legas
  • Gine-gine buda biyu da ke Lakes Estate, Lekki, Lega

Yadda Emefiele ya faɗa cikin rikici

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sallami Tinubu daga iki ne ƙasa da mako biyu bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya naɗa Emefiele a matsayin shugaban CBN a shekara ta 2014.

Ya ci gaba da zama shugaban babban bankin na Najeriya har ƙarshen wa'adin mulki na biyu na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sai dai wasu matakai da ya ɗauka gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023 ya janyo cece ku-ce mai yawa a ƙasar.

Batun sauya fasalin kuɗi da bankin ya ƙaddamar ya haifar da ƙarancin kuɗi a hannun al'umma, wani abu da ya janyo wahalhalu da dama.

Sai dai Emefiele ya ce sauya fasalin kuɗin wani yunƙuri ne na yaƙi da rashawa da matsalar tsaro da kuma ɗabbaƙa tsarin rage amfani da tsabar kuɗi tsakanin al'umma.

Amma lamarin bai yi wa Bola Tinubu daɗi ba, wanda a lokacin yake takarar shugaban ƙasa.

Wasu daga cikin na kusa da shugaban na yanzu sun yi zargin cewa sauya fasalin kuɗin wani yunƙuri ne na yin zagon-ƙasa ga nasararsa a zaɓen.

Bayan dakatar da shi ne hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) ta kama tsohon gwamnan babban bankin, sannan daga baya ta gurfanar da shi a gaban kotu.