Bowen: Mulkin Iran na samun rauni a hankali, amma tana da sauran ƙarfi

    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ta yaya mulkin kama-karya ke rugujewa? Kamar yadda sanannen marubuci Ernest Hemingway ya faɗi game da karyar arziki - ya kan fara ne a sannu a hankali, sai kuma daga baya ya zo kamar ba zato ba tsammani.

Masu zanga-zangar a Iran da magoya bayansu a ƙasashen waje suna fatan cewa gwamnatin Musulunci ta Tehran ta kai matakin 'ba zato ba tsammani'. Alamun su ne, idan har ta kama hanyar rugujewar, yana kan matakin 'sannu a hakali' ne.

Tashe-tashen hankula na makonni biyun da suka gabata na haifar da wani babban barazana ga gwamnatin. Ɓacin rai da takaicin ƴan Iran sun kai wani mataki da ya haifar da fitowar mutane kan tituna, amma wannan tarzomar ta baya-bayan nan ta zo ne bayan hare-haren sojin da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran a cikin shekaru biyu da suka wuce.

Amma mafi mahimmanci ga Iraniyawa waɗanda ke gwagwarmayar ciyar da iyalansu shi ne mummunan tasirin takunkumai.

A cikin sabon koma baya ga tattalin arzikin Iran, duk takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙaƙaba a ƙarƙashin yarjejeniyar nukiliyar da ta mutu a shekarar 2015 da Birtaniya da Jamus da Faransa suka yi a watan Satumba. A cikin 2025 hauhawar farashin kayan abinci ya wuce kashi 70 cikin. Kudin ƙasar, Rial, ya yi faɗuwar darajar da ba a taɓa gani ba a cikin watan Disamba.

A yayin da gwamnatin Iran ke fuskantar matsin lamba, alamu su na nuna cewa ba ta kusa rugujewa ba.

Abu mafi muhimmanci shi ne, jami'an tsaro suna kasancewa masu aminci. Tun bayan juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1979 mahukuntan Iran sun kashe lokaci da kuɗi wajen samar da kuma fayyace hanyar tilastawa da danniya mara tausayi.

A cikin makonni biyun da suka gabata, sojojin gwamnatin sun yi biyayya ga umarnin da aka ba su na harbe ƴan ƙasarsu a kan tituna. Sakamakon haka shi ne an kawo ƙarshen zanga-zangar da aka yi a makonnin baya-bayan nan - daga abin za mu iya gani a ƙasar da mahukuntan ƙasar ke ci gaba da daƙile duk hanyoyin sadarwa.

A sahun gaba wajen murƙushe zanga-zangar ita ce rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), wadda ita ce ƙungiya ɗaya mafi muhimmanci a ƙasar.

Tana da wani aiki na musamman na kare aƙida da tsarin gwamnatin juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979, kuma tana aiki ne a ƙarƙashin jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei. An ƙiyasta cewa IRGC tana da kimanin dakaru 150,000 da ke ɗauke da makamai, waɗanda ke aiki kafaɗa da kafaɗa a asalin rundunar sojin Iran. Har ila yau, ta na takamuhimmiyar rawa a fannin tattalin arzikin Iran.

Rundunar ta IRGC tana da wata runduna mai taimaka mata, ƙungiyar mayaƙa ta Basij ta ƴan sai-kai wadda ke iƙirarin tana da miliyoyin mambobi. Kodayake wasu ƙasashen yamma sun yi ƙididdigar cewa ta na da mayaƙan da ke aiki da suka kai kimanin dubban ɗaruruwa, duk da haka dai suna da yawan gaske. Ƴan Basij taka muhimmiyar rawa a yunƙurin gwamnati na murƙushe masu zanga-zangar.

Na ga IRGC da Basij suna aiki a Tehran a shekara ta 2009, yayin da suka gudanar da aiki murƙushe babbar zanga-zangar da ta biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa mai cike da taƙaddama. Masu aikin sa kai na Basij ne suka yi jerin gwano a kan tituna ɗauke da kulake na katako.

A bayansu akwai wasu mutane sanye da kayan sojoji dauke da bindigogi masu sarrafa kansu. Tawagar mayaƙa a kan babura sun yi ta sintiri a manyan titunan birnin Tehran, inda suka yi ta aukawa kan ƙungiyoyin da ke ƙoƙarin yin zanga-zanga. A cikin ƙasa da makonni biyu zanga-zangar da ta lakume tituna ta ragu zuwa ƙananan gungun dalibai da ke rera taken neman ƴanci da cinnawa shara wuta.

Da alama tsayin daka na jami'an tsaro na cikin gida ba ya nufin cewa jagoran addinin ko muƙarrabansa na iya kwantar da hankulansu. Shugaban Amurka Donald Trump na barazanar ɗaukar mataki. Miliyoyin Iraniyawa masu son ganin rugujewar gwamnatin a halin yanzu dai sun kasance cikin bacin rai.

A Tehran, ga dukkan alamu gwamnati da jagoran addinin na neman hanyoyin rage raɗaɗin matsin lambar da suke fuskanta. Kuma har yanzu akwai maganganun hukuma da ke ƙushe da tayin ci gaba da tattaunawa da Amurka.

Yana da wuya a ga yadda ɓangarorin biyu za su cimma matsaya kan shirin nukiliyar Iran da shirin makamai masu linzami da suka shafe tattaunawar da aka yi a baya. Sai dai tattaunawar za ta iya samo wa Iran lokaci, musamman ma idan Trump ya gamsu cewa akwai yiwuwar ƙulla yarjejeniyar, duk da cewa hakan zai yi wuya.

A wani ɓangare na matsin lambar da ya ke yi mu su, Trump ya ce zai ɗora harajin kashi 25 cikin 100 kan kayayyakin duk wata ƙasa da ke kasuwanci da Iran. Duk da cewa dai, yana da wuya a ga yadda hakan zai iya aiki. China ce ke sayen akasarin man fetur ɗin Iran.

Trump da shugaban China Xi Jinping sun amince da daga ƙafa a yaƙin kasuwancin da ke tsakanin ƙasashensu a kakar da ta gabata, inda za a gudanar da taron ƙoli a birnin Beijing cikin watan Afrilu. Taron dai zai tunkari manyan batutuwan da manyan ƙasashen duniyar biyu ke fuskanta. Shin Trump zai so kawo cikas ko hargitsa taron don kawai ya ci gaba da matsin lamba kan Iran?

A birnin Tehran babban abin da ke gaban Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei shi ne kiyaye tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sake tayar da zanga-zangar na iya fuskantar martani mai tsanani.

Wani fa'ida ga gwamnatin shi ne rashin shugabanci na gari tsakanin masu zanga-zangar. Babban ɗan Shah da juyin juya halin Musulunci ya hamɓarar da shi kusan rabin ƙarni da ya gabata yana ƙoƙarin zama shugaban da masu zanga-zangar ke buƙata. Da alama dai tarihin danginsa da alaƙarsa da Isra'ila na iya rage masa farin jini a idon al'umma.

Wani darasi ɗaya da ka iya damun malamai da sojoji a Tehran ya fito ne daga tsohon abokin tarayyarsu, tsohon shugaban Siriya Bashar al-Assad. Alamu sun nuna kamar ya yi nasara a yaƙinsa, kuma a hankali Saudiyya da haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ke neman yi wa mutuncinsa gyaran fuska, a lokacin da ya fuskanci hare-haren ƴan tawaye a ƙarshen shekarar 2024.

Duka Rasha da Iran, manyan ƙawayensa biyu ba su iya su iya ceto shi ba. A cikin ƴan kwanaki, Assad da iyalinsa suna tafiya gudun hijira a Moscow.

Mulkin kama-karya yana fara wargajewa ne a hankali, kafin daga baya ya faru kwatsam kamar ba zato ba tsammani. Lokacin da mulkin Assad ta ruguje a Siriya, ya faru ne cikin ƙanƙanin lokaci. Wani misali da za a yi nazari a Tehran shi ne faɗuwar Shugaba Ben Ali na Tunisiya a shekara ta 2011, lokacin da sojoji suka yi yunƙurin kare masu zanga-zangar daga jami'an tsaron cikin gida.

Faɗuwar Ben Ali ta sa Hosni Mubarak na Masar ya yi murabus. Mai yiwuwa zai iya tsira daga gagarumar zanga-zangar da aka yi masa da sojoji ba su yanke shawarar cewa tafiyarsa ce za ta tabbatar ceton matsayinsu ba.

Shin hakan zai iya faruwa a Iran? Wataƙila. Amma tukuna dai.

Masu adawa da gwamnatin Musulunci za su yi fatan samun ƙarin matsin lamba a cikin gida da waje da kuma samar da sahihin jagoranci, ta yadda wargajewar za ta zo da sauri, daga sannu a hankali zuwa kwatsam.