Atletico Madrid na son Gomes, Everton da Nottingham Forest na zawarcin En-Nesyri

Lokacin karatu: Minti 3

Atletico Madrid na sha'awar dan wasan tsakiyar kungiyar Wolves da Brazil Joao Gomes, mai shekara 24, bayan da kungiyar ta Sifaniya ta sayar da dan wasan Ingila Conor Gallagher ga Tottenham a ranar Laraba (Marca )

A wani labarin kuma dan wasan tsakiyar kungiyar Wanderers da Zimbabwe, Marshall Munetsi, mai shekara 29, zai koma Paris FC a matsayin aro. (L'Equipe)

Everton ta tuntubi Fenerbahce ta Turkiyya da ta sayar mata da dan wasan Moroko mai kai hari Youssef En-Nesyri, mai shekara 28. Bangarorin biyu na tattaunawa da juna a kan bada aron dan wasan da kuma zabin siyansa kan fam miliyan 17. (Fabrizio Romano)

Ita ma Nottingham Forest na son ta sayi En-Nesyri sai dai Fenerbahce na ganin kamar ya fi son ya koma Everton. (Florian Plettenberg)

Everton na kuma zawarcin dan wasa mai kai hari Callum Wilson, mai shekara 33, wanda ke tattaunawar kawo karshen kwantaraginsa da West Ham. (Athletic)

Haka kuma Everton da Werder Bremen da kuma Ajax, na bibiyar dan wasan Ukraine Yukhym Konoplya. Kwantaragin dan wasan mai shekara 26 da Shakhtar Donetsk zai kare a bazara. (Florian Plettenberg)

West Ham za ta yi wani taro da masu ruwa da tsaki a karshen mako domin su tattauna kan rage yawan kudin da suka nemi a biya domin sayar da dan wasan tsakiya Lucas Paqueta, mai shekara 28, wanda kungiyar Flamengo ta Brazil wadda ita ce mahaifarsa ke son ta siya. (ESPN)

Ana sa ran dan wasan Santos, Souza, mai shekara 19 zai yi gwajin lafiyarsa a Tottenham a Landan a ranar Alhamis yayin da Spurs ta kammala cinikin dan wasan na Brazil a kan fam miliyan13. (Sky Sports)

Ita ma Brentford ta kusan kammala cinikin dan wasan Lazio da Italiya Matteo Cancellieri, mai shekara 23. (Gazzetta dello Sport)

Crystal Palace na tattaunawa da kungiyar Angers na Ligue 1 kan dan wasan gaban Faransa Sidiki Cherif. Dan wasan mai shekara 19, wanda zai iya buga wasa ta tsakiya da gefe , yana da sauran shekaru biyu da rabi a kwantiraginsa.(Sky Sports)

Roma za ta biya Aston Villa fam miliyan 2 domin a ba ta aron Donyell Malen, mai shekara 26, inda a karkashin yarjejeniyar tana da zabin siyan dan wasan kasar Netherlands kan fam miliyan. (Fabrizio Romano)

Bournemouth na sane da cewa sai ta yi da gaske wajen ci gaba da rike dan wasan tsakiyar Ingila Alex Scott, mai shekara 22, a wannan shekara, sakamakon zawarcin da kungiyoyin Firimiya suke masa wadanda suka hada da, Manchester United, da Manchester City, da Aston Villa da kuma Newcastle United. (Teamtalk)