Yaron da ya ciji maciji har ya mutu

    • Marubuci, Situ Tiwari
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reporter
    • Aiko rahoto daga, Bihar, India
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wani yaro ɗan shekara ɗaya a Indiya ya zama jarumi kuma abin alfahari bayan rahoton da ya bayyana cewa ya gartsa wa wani maciji nau'in gamsheƙa cizo har ya mutu a ranar 24 ga watan Yuli.

Yaron mai suna Govind Kumar yana wasa ne a lambun gidansu a ƙauyen Mohchi Bankatwa da ke jihar Bihar a Gabashin Indiya, kusa da iyakar Nepal, lokacin da ya hango macijin.

A lokacin da lamarin ya faru, "mahaifiyar yaron tana aikin lambu a baya," in ji kakarsa, Matisari Devi.

"Ya kama macijin ya gartsa masa cizo da haƙoransa. Sai daga baya muka gane cewa macijin gamsheƙa ne" kamar yadda ta yi ƙarin bayani.

Kakar yaron ta ƙara da cewa bayan ya ciji macinjin nan take Govind ya fita daga hayyacinsa, lamarin da ya sa iyayensa suka garzaya da shi asibitin ƙauyen.

"Lokacin da aka shigar da shi asibiti, fuskarsa ta kumbura musamman a wajen bakinsa," in ji Dr Kumar Saurabh, wanda ya kula da Govind a wani asibitin gwamnati a babban birnin Bihar, Bettiah.

Likitan ya bayyana cewa a rana daya aka kawo wani yaro daban da macijin gamsheƙa ya sara wanda ya fi samun rauni idan aka kwatanta da Govind, wanda shi ne ya ciji macijin.

Likitan ya kuma ce dukkan yaran biyu suna cikin ƙoshin lafiya yanzu.

Dr Saurabh ya bayyana cewa duk da cewa duka biyun – yaron da ya ciji maciji da kuma wanda macijin ya sara – sun fuskanci hatsari iri ɗaya, ɗaya dai ya fi muni ga ɗan'adam.

"Idan maciji gamsheƙa ya sari mutum, gubarsa na shiga jininsa, ta haddasa matsala ga jijiyoyin jiki, wanda zai iya kai wa ga mutuwa," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Amma idan mutum ne ya ciji maciji, gubar tana shiga hanjin mutum ne, wanda jikin ɗan'adam zai iya shawo kanta, inda gubar za ta wuce ta hanyar narkewar abinci," in ji Dr Saurabh, yana mai cewa lamarin zai fi muni idan akwai rauni ko ciwo a cikin hanjin yaron, misali, gyambon ciki.

Indiya na da nau'ikan macizai kusan 300, fiye da 60 daga cikinsu na da guba, inda gamsheƙa ke cikin mafiya haɗari.

Ana kuma kiran ƙasar Indiya "babban birnin saran maciji na duniya," saboda adadin mace-macen da ake samu sakamakon sarar maciji na ƙaruwa musamman a lokacin damina.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta cewa mutum 81,000 zuwa 138,000 na mutuwa a duniya duk shekara sakamakon sarar macizai.

A cewar WHO, daga shekarar 2000 zuwa 2019, mutane kimanin 58,000 ne suka mutu a Indiya duk shekara sakamakon sarar macizai.

Sai dai adadin mutanen da ke mutuwa saboda sarar maciji a ƙasar bai bayyana sosai ba, saboda rashin samun kulawar lafiya da gaggawa a yankunan da lamarin ke faruwa, in ji Ma'aikatar Lafiya da Walwalar Jama'a ta Indiya.