Manyan iftila'in mahaƙar ma'adinai 8 da suka gigita Afirka

    • Marubuci, Mariam Mjahid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
  • Lokacin karatu: Minti 4

A cikin wannan makon ne aka samu wani mummunan iftila'i a wata mahaƙar ma'adinai da ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 40 a jihar Filato da ke arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru bayan da ake zargin masu haƙar ma'adinan sun shaƙi iskar gas ta sinadarin carbon wace take da guba mai ƙarfi yayin da suke hakar ma'adinan.

Shaidu sun cen lamarin ya faru ne kafin fitowar ranar Alhamis a wani wuri a wajen garin Wase, wanda kamfanin ma'adinai na Solid Unity Nigeria Ltd, ke gudanarwa.

Ana ganin cewa guba mai ƙarfi ta sinadarin ta taru a cikin ramin ƙasa da iska ba ya samun shiga sosai, wanda ya sa ma'aikatan suka faɗi a ƙasa kafin su kammala aikin dare.

Waɗanda suka je aiki da safe ne suka tarar da gawawwakin.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka tatar da gawarwakin sun ce sun samu wasu da ransu kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

Hatsari a wurin haƙar ma'adina wani mummunan bala'i ne da ke salwantar da rayukan al'ummar Afirka.

Galibi hakan na faruwa ne sakamakon rashin bin ƙa'idojin haƙar ma'adinan da kuma rashin amfani da ingantattun hanyoyin kariya.

Harkar ma'adinan ta kasance babban ginshiƙin hanyar samun kuɗin shiga ga ƙasashen Afirka.

A wannan muƙala za mu duba wasu lokuta bakwai da aka samu mummunan iftila'i a wurin haƙar ma'adinai a nahiyar Afirka, mai ɗimbin arzikin Ma'adinan.

Mutuwar fiye da mutum 200 a DR Kongo (Jan 2026)

Fiye da mutum 200 ne suka mutu a ƙarshen watan Janairun da ya gabata bayan ruftawar wata mahaƙar ma'adinai a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Mahaƙar - wadda ke ke garin Rubaya - ta rufta ne sakamakon mamakon ruwan sama, kamar yadda Lumumba Kambere Muyisa, kakakin gwamnan ƴan tawayen lardin arewacin Kivu ya shaida wa manema labarai.

Cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su har da matya da ƙananan yara.

Mahaƙar da yi fice wajen haƙar ma'adinin coltan, wani abu da ake amfani da shi wajen ƙera kayayyakin laturoni irin su manyan wayoyi da kwafutoci.

A lokacin faruwar iftila'in tsohon mai kula da mahaƙar ya shaida wa BBC cewa ba a kula da mahaƙar yadda ya kamata, lamarin da ke sa wahalar aikin ceto idan wani iftila'i ya auku.

Mutum 437 a Coalbrook – Afirka ta Kudu (1960)

Iftila'in ruftawar mahaƙar ma'adinan kol ta Coalbrook a Afirka ta Kudu na ɗaya daga cikin mummunan bala'in da ya faru a mahaƙar ma'adinai a nahiyar Afirka.

Masu haƙar ma'adinai 437 ƙasa da danne suka mutu bayan ruftawar mahaƙar.

Wanna bala'ion ya sa gwamnatin Afirka ta kudu ta sauya dokokinta game da haƙar ma'adinai a ƙasar.

Mutum 34 a Marikana – Afirka ta Kudu (2012)

Wannan lamari ana yi masa laƙabi da kisan kiyashin Marikana, wanda ya rusa da masu haƙar ma'adinin platinum, ko kuma farin zinari.

Fiye da mutum 34 ne ƴansanda suka kashe bayan wani mummunan hari da suka kai mahaƙar saboda buƙatarsu ta neman ƙarin albashi.

Wannan al'amari ya girgiza ƴan Afirka ta Kudu da ma duniya baki ɗaya.

Harin - wanda ya auku ranar 16 ga watan Agustan 2012 - an yi imanin shi ne mafi muni tun bayan kawo ƙarshen wariyar launin fata a 1994.

Mutum 40 a Kamoto – ​​DR Congo (2019)

Zaftarwar mahaƙar Kamoto da ake haƙar ma'adinan copper da cobalt ta yi sanadiyyar kisan fiye da mutum 40, mafi yawancinsu matsakaityan masu haƙar ma'adinai.

Lamarin ya nuna irin hatsarin da masu haƙar ma'adinai ke shiga, galibi waɗanda ba su da rajistar aiki, ko suke haƙa ba bisa ka'ida ba.

Mahaƙar zinaren Siaya - Kenya (July 2024)

A shelarar 2024 ne mahaƙar zinare da ke gundumar Siaya da ke ƙasar Kenya ta rufta tare da kashe masu haƙar ma'adinai bakwai da raunata wasu da dama.

Jami'an tsaro da masana sun ce masu haƙar ma'adinan na aiki ne cikin hatsari ba tare da ɗaukar matakan kariya ba.

Mahaƙar zinaren Simiyu Tanzaniya (2024)

A 2024 ne wata ƙaramar mahaƙa da ake aiki ba bisa ƙa'ida ta rufta tare da kashe aƙalla mutum 22 a arewacin Tanzaniya.

Da dama cikin waɗanda suka jikkata sun buƙaci manyan kayan aiki domin zaƙulo su daga ƙarƙashin ƙasa.

Galibi waɗanda lamarin ya shafa matasa ne waɗanda shekarunsu suka kama daga 24 zuwa 32.

Lamarin ya faru ne bayan da masu haƙar ma'adinan suka fara aiki ba tare da bin matakan kariya ba.

Wa ke da alhakin iftila'in?

Masu sharhi na ci gaba da nuna damuwa kan iftila'in da ake yawan samu a mahaƙar ma'adinan Afirka.

Masanan sun yi imanin cewa ci gaban Afirka ya dogara kan ma'adinan da ake haƙawa.

Masu shairhin sun ce akwai buƙatar gwamntocin Afirka su yi ƙoƙarin inganta harkar haƙar ma'adinai domin kare rayukan al'umma.

"Mafi yawan masu haƙar ma'adinai a Afirka na aiki ne wurare masu hatsari ba tare da ingantattun hanyoyin kariya ba..', a cewar ƙungiyar Amnesty International.