Abin da ya kamata ku sani kan zaɓen Abuja da ake yi yau

Lokacin karatu: Minti 3

A yau Asabar, 21 ga Faburairun 2026 ne hukumar zaɓen Najeriya, wato INEC, za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi shida na yankin Abuja, babban birnin tarayya kasar, inda za a zaɓi ciyamomi da mataimakansu, da kuma jimillar kansiloli 62.

Wannan ne dai karon farko da INEC za ta gudanar zaɓe ƙarƙashin sabuwar dokar zaɓen Najeriya, wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu ƴan kwanakin da suka gabata.

Zainab Aminu Abubakar, jami'a a sashen yaɗa labarai na hukumar INEC ta shaidawa BBC cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da zaɓen, inda ta ce ''Kamar yadda yak e tsari za a buɗerumfunan zaɓen ta misalign ƙarfe takwas da rabi na safe. Za a rufe zaɓe karfe biyu da rabi na rana, amma fduk waɗanda suke kan layi kafin lokacin, to ko ƙarfe biyu da rabi ya yi za a basu dama su kaɗa ƙuri'arsu. ''

Ta kuma bayar da tabbacin cewa an yi tanadi na musamman domin samar da tsaro mai inganci a lokacin zaɓen ''jami'an tsaro sun bayar da tabbacin samar da tsaro yadda ya kamata a dukka runfunan zaɓe da kuma wuraren tattara sakamakon zaɓe, kafin zaɓen da lokacin gudanarwa da kuma bayan an kammala.''

Dangane da aikewa da sakamakon zaɓe kai tsaye ta hanyar na'ura kuwa, sai Zainab Aminu ta ce ''Kamar yadda ya ke al'ada, dama hukumar zaɓe tana ɗaukar hoton takardar sakamakon zaɓen kowacce runfa, bayan an gama zaɓe an ƙirga ƙuri'u, an cike takardar, jami'an tsaro da wakilan jam'iyyu sun sa hannu, za a ɗauki hoton takardar sai a ɗora ta a yanar gizo.''

Ta ƙara da cewa har yanzu wannan tsari yana nan, kuma za a yi amfani da shi a zaɓen ƙananan hukumomin birnin tarayya Abuja na ranar Asabar 21 ga watan Faburairun 2026.

Ana dai kallon zaɓen na babban birnin tarayya Abuja, a matsayin wani zakaran gwajin dafi ga jam'iyyun adawa da tagomashin jam'iyyar APC da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da kuma hoɓɓasar hukumar zaɓen ƙasar wajen gudanar da zaɓe mai inganci ƙarƙashin sabon shugabanta, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a badi.

Masana harkar siyasa irin su Farfesa Abubakar Umar Kari na jami'ar Abuja na ganin cewa zaɓen ba zai zamo zakaran gwajin dafi ga jam'iyyun adawa ba, musamman ta la'akari da cewa ''har yanzu jam'iyyun adawar nan suna neman bakin zaren ne, wao ba su gama kafuwa ba, musamman ma jam'iyyar ADC. Saboda haka sakamakon wannan zaɓe, ba zai kasance manuniya ga abin da zai faru a babban zaɓe ba.

To amma kuma zaɓen zai iya kasancewa zakaran gwajin dafi ga hukumar zaɓe, zai nuna cewa ko ta shirya ko bata shirya ba. Sannan kuma, ko gwajin da za ta yi, na wasu na'urori musamman ma na'urorin zaɓe, kamar yadda sabon shugaban hukumar ya ce, za a samu nasara ko ba za a samu nasara ba.''

Fiye da mutum miliyan 1.5 ne suka karɓi katin zaɓe gabanin zaɓen Abuja- INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bayyana cewa masu zaɓe fiye da miliyan ɗaya da rabi ne suka karɓi katin zaɓe a duk faɗin babban birnin tarayya, Abuja kafin zaɓen majalisar kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga Faburairun 2026.

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta nuna cewa har zuwa ƙarshen karɓar katunan a ranar 10 ga Fabrairu, an yi rajistar masu zaɓe 1,680,315 a Abuja, inda mutum 1,587,025 suka karɓi katin zaɓe, yayin da katunan 93,290 suka rage ba a karɓa ba.

Hukumar ta jaddada cewa waɗanda suka yi rajistar zaɓe kuma suka ansa kati ne kawai za su samu damar kada kuri'a a ranar zaɓen.

INEC ta ce ta shirya dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zaɓe mai gaskiya.