Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ya kamata mai azumi ya yi buɗe-baki
Musulmai a faɗin duniya sun fara gudanar da ibadar azumin watan Ramadana, ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci biyar wanda ke buƙatar mutum ya ƙaurace wa cin abinci ko shan ruwa daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana.
Duk da ɗimbin alfanun da azumi ke da shi ga lafiya, mutane da dama kan sha wahala sanadiyyar sauyin da ake samu wajen cin abinci a tsawon watan.
Wasu sukan fuskanci gajiya da kasala sanadiyyar rashin cin abinci da shan ruwa na tsawon lokaci, wasu kuma da ke fama da lalura, kamar ciwon suga ko hawan jini kan iya fuskantar matsaloli.
Masu azumi kan yi ƙoƙarin tanadar abinci kala daban-daban a kowace rana idan aka zo yin buɗe-baki, ko da kuwa mutum bai kasance mai ƙarfin tattalin arziƙi ba.
Wannan ya samo asali ne daga al'adar watan, inda mutane kan so su taimaka wa junansu, wanda hakan na sanyawa kusan kowa ya samu abinci kala-kala.
Hakan na ingiza mutane su ci abinci fiye da yadda suke buƙata, kuma ba da jimawa ba suke jin tasirin abin.
Hakan na iya haifar da matsaloli kamar ciwon ciki, kumburin ciki, kasala da jiri. Matsalar kan yi ƙamari ga wasu, inda take iya haifar da hawan jini ko kuma hauhawar yawan sukari da ke jikin ɗan'adam.
Kwanakin farko na Ramadan sun fi wahalarwa, "domin jiki na fara amfani da kitse a matsayin hanyar samun kuzari ne bayan kwana huɗu" ana azumi, in ji masani kan abinci, Fadi Abbas, a tattaunawarsa da BBC.
Abbas ya ce ya kamata a raba abin buɗe-baki zuwa kashi uku, kuma a riƙa cin kowane kashi bayan minti shidda-shidda, kuma haka ma ya kamata a yi a lokacin sahur.
Ya yi bayani kan cewa ƙwaƙwalwa na buƙatar minti 18 kafin ta tabbatar da cewa nutun ya ƙoshi ko a'a.
Ya ce: "Ana bai wa mutane shawarar su fara da shan ruwa, su kurɓa sau uku yayin da suke zaune. Bayan minti shida, sai mutum ya fara ci ko shan wani abu mai sukari domin jiki ya maye gurbin kuzarin da ya rasa da rana, ana son mutum ya ci abincin da ba a sarrafa ba, kamar dabino ko kuma kayan itatuwa".
Ya ƙara da cewa: "Bayan wasu mintuna shida, ana bai wa mutum shawara ya ci salak domin taimaka wa cikinsa ya saki. Dussar da ke cikin ganyayyakin za su taimaka wa jiki da sinadaran gina jiki da kuma hana ɗaurewar ciki ko atini.
"Bayan salak, sai mutum ya ci abinci ɗaya ko biyu wadanda suka ƙunshi sinadaran gina jiki da kuma na samar da kuzari."
Misali, mutum zai iya cin dankali ko taliya ko shinkafa ko burodi, wadannan duk abinci ne masu auke da sinadaran ara kuzari, "saboda haka za a ci nau'i ɗaya na wannan abincin za a haɗa da abinci mai gina jiki "kamar wake da ƙwai da nama ko madara), kuma a riƙa lura da lokacin da ake kwashewa ana tauna abinci, wato sakan 30 ga abinci mai laushi ko kuma sakan 60 ga abinci mai tauri (kamar nama da gyaɗa)."
Duk da cewa jiki na buƙatar ruwa sosai, shan ruwa da yawa ta yadda bai kamata ba, zai iya kawo matsala ga ayyukan ƴaƴan hanji da kuma ƙoda.
Saboda haka, "ya kamata a bi tsari mai kyau, kuma bai kamata a sha fiye da kofin ruwa biyu ba a lokaci ɗaya cikin awa ɗaya da yin buɗe-baki.
"Kada a sha ruwa sai mutum ya ji ƙishi, ko kuma bayan awa ɗaɗɗaya ko awa ɗaya da rabi, mutum na iya saita ƙararrawar tunatarwar agogo da za ta riƙa tunatar da shi tsawon lokacin da zai kwashe kafin ya sha ruwa," kamar yadda Abbas ya bayar da shawara.