Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane horo sojojin Najeriya za su samu daga dakarun Amurka?
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Karo biyu a cikin wannan wata na Fabarairun 2026 aka tabbatar da isar dakarun Amurka a Najeriya.
A farkon watan ne shugaban dakarun Amurka da ke a nahiyar Afirka (Africom), Dagvin Anderson ya tabbatar da cewa Amurka ta tura wata kwarya-kwaryar tawagar sojin Amurka zuwa Najeriya.
Sai kuma ga shi a ranar Litinin shalkwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar da isar sojojin Amurka 100 zuwa Najeriya.
Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar ta hannun daraktan yada labaranta Manjo Janar Samaila Uba, ta ce tuni rukunin farko na sojojin Amurkan da ya ƙunshi dakaru 100 suka sauka a filin jirgin sama da ke Bauchi a arewa maso gabashin ƙasar.
A makon da ya gabata ne Amurka ta sanar da ahirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da dakarun ƙasar dabarun yaƙi da ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya.
Kawo yanzu dai hukumomin Najeriya da na Amurka ba su bayyana irin horon da sojojin na Amurka za su bai wa takwarorin nasu na Najeriya ba.
To amma masana tsaro a ƙasar na ganin akwai fannonin da suka kamata a bai wa fifiko a horon da za a bai wa dakarun Najeriyar, domin ƙarfafa su a ƙoƙarin da suke yi na murƙushe ƙungiyoyin ƴanbindiga a ƙasar.
Cikin wata hira da BBC, Kabir Adamu, Shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligece Limited ya bayyana wasu bangarori da ya ce sojojin na Najeriyar ke buƙatar a horas da su a kai.
Amfani da AI wajen tattara bayanan sirri
Kabiru Adamu ya ce yanzu fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI na kan gaba wajen hanyoyin tattara bayanan sirri, kuma ƙasar Amurka na da ƙwarewa a wannan fanni.
''Amfani da fasahar AI da kuma horas da fasahar ta AI wadda ake kira 'Machine learning' za su taimaka matuƙa wajen ƙarfafa rundunar sojin Najeriya,'' in ji masanin tsaron.
Sai dai ya ce sojojin Najeriya za su iya samun wannan horo ne kawai idan an yi yarjejeniyar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
''Ma'ana dole ita ma rundunar sojin Amurka ta buƙaci wani abu daga Najeriya, wato dai abin da Hausawa ke cewa ban gishiri in ba ka manda, kamar yadda aka saba yi a alaƙar yaƙi tsakanin ƙasashe,'' in ji shi.
Ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri
Dokta Kabiru Adamu ya ce hanyoyin tattara bayanan sirri da tantance shi sun sauya daga yadda aka san su a baya.
Ya ce a baya ana amfani da ɗan'adam wajen tattara bayanan, amma yau an wayi gari akwai dabaru masu yawa da ake amfani da su wajen tattara bayanan sirri da tantance su.
''Akwai dabaru 12 da ake amfani da su wajen tattara bayanan sirri, kuma sojojin Najeriya na buƙatar horon ƙwarewar amfani da su, kuma su sojojin Amurka na da ƙwarewa mai karfi a wannan fanni''.
Masana tsaro na ganin cewa Amurka ce ƙasa ta biyu a duniya bayan Isra'ila wajen ƙwarewar tattara bayanan sirri.
Don haka Dokta Kabiru Adamu ke cewa dakarun Najeriya na buƙatar amfani da wannan dama wajen samun horo a wannan fanni.
Horon dabarun yaƙin sunkuru/sari-ka-noƙe
Matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta galibi hare-hare ne na sari-ka-noƙe ko yaƙin sunƙuru.
Yaƙin sunƙuru ko sari-ka-noƙe nau’i ne na hare-hare da ƴanbindiga ke shiryawa su kai, don kashe mutane ko sace su, sannan su gudu su koma maɓoyarsu.
Don haka ne Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai buƙatar sojojin Najeriya su samu horo kan yadda za su magance hakan.
''Yau kusan shekara 15 Najeriya na fama da ire-iren wannan matsalar kuma har yanzu ba su iya magance ta ba, don haka tana buƙatar sabbin dabarun magance hakan,'' in ji shi.
Dabarun yaƙin ƙundunbala
Yaƙin ƙundunbala shi ne aika sojoji zuwa wani wuni mai sarƙaƙiya, kamar cikin dazuka da tsaunuka ko cikin ruwa domin gudanar da yaƙi.
Galibi ƙungiyoyin ƴanbindigar da ke addabar Najeriya na da mafaka ne cikin dazuka ko tsaunuka ko ma cikin tafki, kamar Tafkin Chadi da ake tunanin Boko Haram da ISWAP na ciki.
Masanin harkokin tsaron na Najeriya ya ce dakarun Najeriya na buƙatar horon da za su yi amfani da shi wajen shiga irin waɗannan wurare masu sarƙaƙiya.
''Rundunar sojin Amurka na da ƙwarewa sosai a wannan fanni, domin mun ga yadda suka shiga wurare masu sarƙaƙiya suka kuma yi nasara''.
''Idan ka duba a watan da ya gabata dakarunta na kundunbala sun shiga fadar gwamnatin Venezuela suka ɗauke shugaban ƙasar da matarsa ba tare da tangarɗa ba,'' in ji shugaban kamfanin na Beacon Security.
Ya ci gaba da cewa a shekarun da suka gabata an taɓa sace wani Ba'amurke a Nijar, amma sojojin ƙundunbalan ƙasar da suka samu bayanan sirrin inda suke, suka je suka ɗauke shi suka tafi.
Dabarun yaƙi cikin dare
Galibi hare-haren da ƴanbindiga ke kai wa a Najeriya, musamman Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane kan yi hakan ne a cikin dare.
An ga lokuta da dama da mayaƙan Boko Haram ke far wa sansanonin soji ko garuruwa cikin dare tare da yi musu lahani mai yawa
Dokta Kabiru Adamu ya ce ba lallai ba ne rundunar sojin Najeriya na da kayan aiki da ƙwarewar yaƙin cikin dare.
''Don haka suna buƙatar wannan horo ƙwarai da gaske, kuma ita rundunar sojin Amurka na da ƙwarewa sosai a wannan fanni don haka za su iya taimaka wa Najeriya da wannan horo,'' in ji shi.
Dabarun tsaron intanet
Wata matsala da ke kawo wa fannin tsaron Najeriya cikas ita ce tsaron sadarwar intanet.
A shekarar da ta gabata an samu rahotonnin yadda mayaƙan ISWAP suka yi kutse a sadarwar wani babban kwamandan soji da dakarunsa, suka gano inda yake tare da sake kama shi.
Haka a kwanan nan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya yi iƙirarin satar jin wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro.
Don haka Kabiru Adamu ya ce dakarun tsaron Najeriya na buƙatar horo sosai a fannin tsaron intanet.
''Kuma su sojojin Amurka na da ƙwarewa sosai a wannan fanni,” in ji masanin tsaron.
'Wannan ya dogara ne ga muradun ƙasashen biyu'
Dokta Kabiru Adamu ya ce duka nau'ukan horon da dakarun Amurka za su yi wa sojojin Najeriyar za su samu ne kawai la'akari da muradun ƙasashen biyu.
''Ya danganta da irin yarjejeniyar diflomasiyya da ƙasashen biyu suka cimma'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
''Ba haka kawai za su bai wa sojojin Najeriyar ba, sai ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya ko ba ni gishiri in ba ka manda,''.
Masanin tsaron ya kuma ce Najeriya za ta amfana da horon ne kawai idan ta yi gyare-gyare musamman a fannonin tsaron intanet ɗinta.
''Don ita Amurka ba za ta yarda ta riƙa bayar da bayanan da wasu abokan gabarta na duniya za su riƙa saurara suna ji ba,” in ji shi.