Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani kan kama ƙanin Sarkin Ingila, Andrew Mountbatten-Windsor
- Marubuci, Edited by Stephen Hawkes and Andrew Webb
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 13
An kama Andrew Mountbatten-Windsor bisa zargin aikata rashin ɗa'a a ofishin gwamnati.
Kamen dai na zuwa ne a ranar da tsohon yariman ya cika shekaru 66 a duniya.
An kama shi a wani gida Sandringham, a Norfolk, inda yake zaune tun lokacin da aka umarce shi da ya bar gidan masarauta na Windsor.
Jami'ai na ci gaba da gudanar da bincike a gidajen biyu.
Tsohon yariman ya fuskanci tuhume-tuhume da dama kan alaƙarsa da mutumin nan da aka samu da laifin lalata da ƙananan yara, Jeffrey Epstein, amma kama shi da aka yi yanzu ba ya da alaƙa da tuhume-tuhumen da suka shafi lalata.
Hakan na zuwa ne bayan ƴan sandan yankin Thames Valley sun ce suna bincike kan zargin fallasa bayanan sirri da tsohon yariman ya yi wa Epstein, yayin da ya kasance wakilin kasuwanci.
Andrew Mountbatten-Windsor ya sha musanta aikata wani laifi dangane da alaƙarsa da Epstein; kuma bai amsa buƙatar BBC na yin tsokaci kan zarge-zargen da ke da alaƙa da sakin kundin bayanai da suka shafi Epstein a watan Janairun 2026 ba.
Sarki Charles III ya ce ya "samu labarin da ya jefa shi cikin matuƙar damuwa" game da kama Andrew, yana mai cewa "dole ne doka ta yi aikinta".
Wane ne Jeffrey Epstein, kuma mene ne alaƙarsa da Andrew?
Epstein wani mai hada-hadar hannayen jarin kamfanoni ne wanda ya mutu a cikin 2019 yayin da yake kurkuku yana fuskantar tuhumar yin safarar mata da nufin lalata da kuma haɗa baki. Likitan gwamnatin jihar New york ya yanke hukuncin cewa ya kashe kansa ne.
A cikin 2005, iyayen wata ƴar shekara 14 sun shaida wa ƴan sandan Florida cewa Epstein ya yi lalata da ƴarsu a gidansa na Palm Beach. Wani bincike da ƴan sanda suka gudanar ya gano hotunan ƴan mata a wuarre daban daban a cikin gidan.
An yanke wa Epstein hukuncin ɗaurin watanni 18 a gidan yari kuma an sake shi bayan wata 13.
A watan Yulin 2019 aka kama Epestein a birnin New York bayan ya koma daga Paris a cikin jirgin saman da ya mallaka.
A watan Augusta aka same shi ya mutu a cikin dakinsa da ke gidan yarin birnin New York, inda ake tsare da shi yayin da yake jiran shari'a kan wasu tuhume-tuhume da gwamnatin tarayya ta gabatar.
An zargi Epstein da biyan ƴan mata da ba su kai shekara 18 ba domin ya yi lalata da su a gidajensa da ke Manhattan da kuma Florida a tsakanin shekarun 2002 da 2005.
Ya musanta aikata ba daidai ba, kuma ya ƙi amsa duk wani laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
Andrew ya shaida wa shirin BBC na Newsnight a shekarar 2019 cewa ya yanke duk wata alaƙa da tsohon abokin nasa a watan Disamban 2010 bayan sun haɗu a wani wurin shaƙatawa a birnin New York.
Amma Saƙonni Email sun nuna cewa Andrew ya tuntuɓi Esptien a asirce cikin wasu watanni bayan hakan inda ya yi alƙawarin ''ci gaba da wasa nan ba da jimawa ba''.
Wasu sabbin bayanai sun fito kan alaƙar da ke tsakanin tsohuwar matar Andrew, Sarah Ferguson da Epstein.
Ƙungiyar bayar da agaji da Ferguson ta ƙirƙira mai suna Sarah's Trust, ta bayyana cewa za ta dakatar da ayyukanta na ''wani tsawon lokaci'' bayan sakonnin Email sun nuna cewa ta ci gaba da zumunci da Epstein a lokacin da ake tsare da shi a gidan yari bisa samunsa da laifin lalata da ƙananan yara.
Ya aka yi yarima Andrew ya koma Mr Windsor?
Sarkin ya tuɓe wa ɗan'uwansa sarautar, ''yarima" a watan Oktoban 2025.
A lokacin, fadar Buckingham ta ce "tunanin Sarki da matuƙar tausayawarsa sun kasance, kuma za su ci gaba da kasancewa tare da waɗanda wannan lamarin ya shafa da waɗanda suka taɓa fuskantar kowane irin nau'in cin zarafi".
Andrew ya yi murabus daga muƙamansa na sarauta, da suka haɗa da 'Duke of York', a farkon watan Oktoban 2025, bayan Virginia Giuffre ta wallafa wani tarihin rayuwarta wanda aka fitar bayan mutuwarta mai suna 'Nobody's Girl', ta maimaita zargin cewa ya yi lalata da ita sau uku a lokuta daban-daban, lokacin tana matashiya. Andrew dai ya sha musanta wannan zargin.
Da suke mayar da martani ga kalaman fadar, dangin Misis Giuffre sun ce ta "ga bayan wani yariman Biritaniya da gaskiya da kuma jajircewarta". Ms Giuffre ta kashe kanta ne a farkon wannan shekarar.
A ina Andrew ya ke zama?
A cikin shekarar 2003, Andrew ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar haya a masaukin baƙin masarauta ta Royal Lodge - gida mai ɗakuna 30, wanda ke kusa da fadar Windsor Castle.
A watan Fabrairun 2026 ya koma wani gida mai zaman kansa wanda sarki ke ɗaukar nauyi a ungwar Sandringham Estate.
Me ya sa har yanzu Andrew ke cikin jerin magadan sarki?
Andrew ya kasance na takwas a jerin waɗanda ka iya gadon kujerar sarautar Ingila - inda ƴaƴansa mata, Gimbiya Beatrice, ke biye da shi a mataki na tara, sai kuma Gimbiya Eugenie, a mataki na 12.
Amma bayanai daga ɗakin karatun majalisar wakilai na nuna cewa ƙudurin majalisar na iya suya hakan.
An taɓa samun lamari irin wannan a baya. Doka ta shekarar 1701 ta sanya an cire Yarima Michael na Kent daga jerin magadan sarki lokacin da ya auri mai bin ɗariƙar Katolika, a shekarar 1978 - ko da yake, an maido da shi shekaru 37 bayan haka, lokacin da aka ƙaddamar da dokar fayyace magadan sarauta kuma yanzu shi ne na 53 a jerin masu gadon sarauta.
Amma cire Andrew daga jerin magada na buƙatar sahhalewar sauran ƙasashe 14 da sarki Charles ke mulki:
- Antigua and Barbuda
- Australia
- The Bahamas
- Belize
- Canada
- Grenada
- Jamaica
- New Zealand
- Papua New Guinea
- Saint Kitts and Nevis
- Saint Lucia
- Saint Vincent and the Grenadines
- Solomon Islands
- Tuvalu
Waɗanne zarge-zarge Virginia Giuffre ta yi kan Andrew?
A wata shari'a da aka yi a shekarar 2021, ta zargi Andrew da cin zarafin ta ta hanyar lalata.
A cikin takardun kotu, ta ce ta kasance wadda aka yi safarar ta domin yin lalata da ita, kuma ta fuskanci cin zarafi a hannun Jeffrey Epstein tun tana da shekaru 16 - kuma wannan ya haɗa da bayar da ita "rance" ga wasu manyan mutane irin su Andrew, wanda ta ce ya yi lalata da ita a lokuta uku daban-daban kafin ta cika shekaru 18.
Andrew ya sha musanta duka zargin da Ms Giuffre ta yi a kansa kuma ya shaida wa shirin Newsnight na BBC cewa bai tuna cewa ya taɓa haɗuwa da ita ba.
Ɓangarorin biyu sun cimma matsaya ba tare da shiga kotu ba, a shekarar 2022, inda Andrew ya biya Ms Giuffre wasu kuɗaɗen da ba a bayyana adadinsu ba kuma ba tare da ya amsa aikata laifi ba.
Mene ne ke ƙunshe a cikin littafin Virginia Giuffre?
Ms Giuffre ta yi fargabar cewa za ta "mutu a matsayin baiwa" a hannun Epstein da jama'arsa, kamar yadda littafin tarihin rayuwarta mai suna 'Nobody's Girl' da aka fitar a bayan mutuwarta ya bayyana.
Haka kuma, wata da ke da hannu dumu-dumu cikin wannan zarge-zarge na cin zarafin ita ce tsohuwar budurwar Epstein, Ghislaine Maxwell, wadda a halin yanzu take zaman gidan yari na shekaru 20 bayan samun ta da laifin safarar yara domin karuwanci.
Shekaru da dama bayan haka, Ms Giuffre ta tuna yadda take tsoron su duka biyun. Kuma akasarin littafin ya ƙunshi bayanai masu ban tsoro, yayin da ta ke bayar da cikakken bayani game da cin zarafi ta hanyar jima'i da Epstein ya yi mata , wanda ya sanya ta shiga wani mawuyacin hali ''da har ya kai ga ina fatan in sume''.
Me ne ne littafin Virginia Giuffre ya ce a kan Andrew?
A cikin watan Maris ɗin 2001, Maxwell ta tashi ta daga barci inda ta fada ma ta cewa "rana ce ta musamman" kuma "kamar Cinderella" za ta haɗu da wani "basarake mai kyau", in ji Ms Giuffre.
Lokacin da suka haɗu, ta ba da labarin cewa Maxwell ta tambayi Andrew, wanda a lokacin ya ke da shekara 41, cewa ya canki shekarunta.
Ya "canki daidai - 17", in ji Ms Giuffre, inda ya ƙara da cewa: Da kaɗan ki ka girmi ƴaƴana mata (Gimbiya Beatrice da Gimbiya Eugenie)."
A wannan daren, ita, da Epstein da Maxwell sun je gidan rawa na London Tramp tare da Andrew, wanda "ya yi gumi sosai," in ji Ms Giuffre.
Sa'an nan, yayin da su huɗun suke komawa gidan Maxwell, Maxwell ta ce mata: "Idan muka isa gida, za ki yi masa abin da kike yi wa Jeffrey."
Ms Giuffre ta ce "Ya kasance mai fara'a sosai, amma duk da haka yana ji da kansa - kamar dai ya na ganin cewa yin lalata da ni haƙƙinsa ne," in ji Ms Giuffre.
"Washegari da safe, na tabbata cewa Maxwell ta tattauna da basaraken abokinta saboda ta ce da ni, 'Kin yi ƙoƙari. Yarima ya ji daɗi sosai."
Ms Giuffre, ''ba ta ji daɗi ba ko kaɗan'' ta rubuta, inda ta ƙara da cewa "Ba da daɗewa ba, Epstein zai ba ni dala 15,000 don yi wa mutumin da ake kira 'Randy Andy' hidima - kuɗi ne mai yawa."
Bayan kusan wata guda, in ji ta, ta yi lalata da Andrew a karo na biyu, a gidan Epstein da ke New York.
Lokaci na uku da ake zargin Andrew da yin lalata da Giuffre ya kasance ne a tsibirin Epstein, a wani ɓangare na abin da Ms Giuffre ta bayyana a matsayin "Biki na baɗala".
"Epstein, Andy da ni da wasu ƴan mata kusan takwas mun yi lalata a tare," in ji ta.
"Akwai alamun cewa sauran ƴan matan duk ƴan ƙasa da shekara 18 ne, kuma ba sa jin Turanci sosai.
"Epstein ya yi dariya game da yadda ba za su iya yin maganar da ake iya fahimta ba, yana mai cewa su ne ƴan mata mafi sauƙin kai."
Yayin da take magana kan sasantawar da aka yi a wajen kotu a shekarar 2022, Ms Giuffre ta rubuta cewa: "Na amince da umarnin ƙin yin magana na shekara guda, wanda ya zama mai muhimmanci ga yariman saboda ya tabbatar da cewa bikin cikar mahaifiyarsa shekara 70 kan karagar mulki bai fuskanci wani ƙarin barazana ba."
Wata majiyar fadar Buckingham ta shaida wa BBC cewa jami'an gidan sarautar sun yi la'akari da cewa wallafa littafin na iya nufin "karin kwanaki masu cike da dambarwa a nan gaba".
Mene ne Andrew ya ce a shirin Newsnight na BBC a shekarar 2019
Andrew ya yi amfani da hirar da BBC Newsnight ta yi da shi a shekarar 2019 don musanta cewa ya yi lalata da Ms Giuffre, yana mai cewa ya kai Gimbiya Beatrice zuwa gidan cin abinci na Pizza Express da yammacin ranar.
Ya kuma dage da cewa ba zai iya zama mutumin da Ms Giuffre ta bayyana a matsayin "mai tsananin gumi ba".
"Ban yi gumi ba a lokacin, saboda ina fama da wani abin da zan kwatanta a matsayin yawan sinadarin adrenaline a yakin Falklands, lokacin da aka harbe ni," Andrew ya shaida wa Newsnight.
"Kusan ba zai yiwu in yi gumi ba."
Jaridu daga baya sun wallafa hotunan da aka ɗauka a daidai lokacin Andrew wanda suka ce ya nuna yana zufa.
Mene ne ƴan sandan Birtaniya ke bincike a kai?
Ƴan sandan birnin Landan suna "bincike a hankali" kan rahoton jarida da ke cewa Andrew ya nemi wani jami'in da aka ba shi a matsayin mai gadi "ya nemo bayanai" kan Ms Giuffre a 2011.
Rahoton, a cikin jaridar 'Mail on Sunday', ya ce Andrew ya ba mai gadin na sa ranar haihuwarta da lambar zama ƴar ƙasarta don ƙoƙarin gano ko ta taɓa aikata wani laifi ko kuma wani bayani da zai iya cutar da ita.
A lokacin, majiyoyin sarauta sun ce ana ɗaukara wannan tuhumar da ake yiwa Andrew a matsayin abu mai janyo "damuwa sosai kuma ya kamata a bincika ta hanyoyin da suka dace".
Andrew ya daina zama basarake mai aiki a cikin 2019 - kuma don haka Fadar Buckingham ba ta iya shiga tsakani a madadinsa ba a cikin ƴan shekarun nan.
Daga ina sunan Mountbatten-Windsor ya samo asali?
Sunan Mountbatten-Windsor ya haɗa da sunayen dangin marigayiya Sarauniya Elizabeth II da na , Yarima Philip.
An ƙirƙire shi ne a cikin 1960, don amfanin zuriyarsu, Andrew ya yi amfani da shi don yin rajistar aurensa da Sarah Ferguson a hukumance .
A cikin 1917, lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, sarki mai mulki, George V, wanda ke jin tsoron ƙiyayyar Jamusawa a Burtaniya, ya sauya sunan danginsa daga sunan Jamusanci na Saxe-Coburg da Gotha zuwa Windsor.
A halin yanzu, a gefen mahaifin Andrew, kakarsa, Gimbiya Alice na Battenberg, ta sauya sunan danginta, zuwa Mountbatten.
Mene ne kuma ya taimaka wa faɗuwar Andrew?
Takardun sirri da ke bayyana alaƙar Andrew da wani ɗan leƙen asirin ƙasar China sun fito fili a watan Afrilun 2025, bayan da BBC da wasu kafafen yaɗa labarai suka matsa ƙaimi kan kotuna da su sake su.
Sun bayyana yadda Andrew ya yi imanin cewa zai iya samun ƙasaitaccen matsayi ta hanyar neman damar kasuwanci a ƙasar China tare da taimakon ɗan kasuwa Yang Tengbo.
Takardun sun kuma bayar da cikakkun bayanai game da "hanyar sadarwa" da Andrew ya ƙaddamar da shugaban China Xi Jinping, wanda ya haɗa da aikewa da wasiƙar zagayowar ranar haihuwar shekara shekara, da kuma yadda jami'an tsaron Burtaniya, MI5, suka shiga tsakani don yin gargaɗi kan duk wata hulɗa da Mista Yang.
Shaidar ta Mista Hampshire kuma ta bayyana cewa:
- An tattauna dangantakar Andrew da Mista Yang a tarurruka biyu da Mista Hampshire da Sarki, inda aka shigar da Andrew Windsor Castle a asirce don kaucewa ƴan jarida.
- Tashin hankali tsakanin masu taimaka wa Andrew ya sa aka cire sakatarensa daga wasu tarurruka game da tsare-tsaren kasuwancinsa.
Andrew ya ce ya daina hulɗa da Mista Yang bayan ya samu shawarwari daga gwamnati. Dukkan tarurrukan sun kasance "a hukumance", kuma "babu wani abu mai mahimmanci da aka taɓa magana akai".
Mista Yang ya ce siffanta shi da aka yi a matsayin ɗan leƙen asiri ba gaskiya ba ne.