Waɗanne ƙasashe ne suka taɓa yin gwajin makamin nukiliya?

Lokacin karatu: Minti 6

Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya bayyana wasu bayanai da ya ce suna tabbatar da zargin ƙasarsa cewa China ta yi gwajin makamin nukiliya a asirce.

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, Christopher Yeaw ne ya bayyana haka, inda ya ce wata na'ura ce a Kazakhstan ta gano fashewa mai ƙarfin 2.75 da ta auku a kudancin China a ranar 22 ga wata Yunin 2020.

Sai dai ofishin jakadancin China da ke Washington ta musanta zargin, inda ta ce magana ce kawai mara tushe.

Ƙungiyar hana gwaje-gwajen makamin nukiliya ta ce babu cikakken bayanin da zai tabbatar da zargin na Yeaw.

A watan Nuwamba ne Shugaba Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Trust cewa ya buƙaci jami'an tsaron ƙasar da "su fara gwada makamin nukiliya" da suka yi daidai da ƙarfin abokan gwada ƙwanjin ƙasar.

Wannan ya sa BBC ta yi nazari kan yadda ake gwajin makamin nukiliya.

Gwajin sararin samaniya

Amurka ta yi gwajin makamin nukiliya na farko ne da ake kira da Trinity a ranar 16 ga watan Yulin 1945 a New Mexico.

Wata biyu baya ne kuma ƙasar ta jefa makaman nukiliya biyu a Japan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a biranen Hiroshima da Nagasaki.

Masu sa ido kan gwajin makamin nukiliya sun ce an gudanar da gwajin sau aƙalla 528 a sararin samaniya.

A shekarar 1980 ce kuma China ta aiwatar da gwajin sararin samaniya na ƙarshe.

Gwajin ƙarƙashin ƙasa

Gwajin makamin nukiliya a ƙarƙashin ƙasa yana hana tashin alamun makamin, wanda hakan ya sa ake yi a asirce.

Amma duk da haka tashin bam ɗin yana fitar da wasu sinadarai da ke gurɓata ruwa da ƙasa.

Ana aiwatar da irin wannan gwajin ne a can ƙarƙashin ƙasa, kuma a kan tafi wuri mai nisa daga idon mutane.

Ana saka makamin ne a can cikin ƙasa, inda ake haƙa rami mai zurfin tsakanin mita 200 zuwa 800, kuma mai faɗin gaske.

Sai a saka wata na'urar bibiya a cikin ramin, sai kuma a saka duwatsu da ƙasa su zama tamkar kankare a gefe da gefe domin rage motsin ƙasa.

Sai a tayar da makamin daga wani wajen daban.

Ƙasashen da suka taɓa gwaja makamin nukiliya?

Ƙungiyoyin sa ido kan makamin nukiliya sun ce an aiwatar da gwajin aƙalla sau 2,000 a gomman cibiyoyi a faɗin duniya.

A shekarar 2017, Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin, wanda ake tunanin shi ne na baya-bayan nan da aka yi.

Ƙasar ce ta sanar da gwajin, wanda daga bisani ta bayyana cewa ta samu nasarar aiwatarwa.

Wasu bibiya sun ce fashewar ta kai ƙarfin tan kilo 100-150, wanda hakan ke nufi ya ninka da wanda ƙasar ta yi a baya kusan sau 10.

Tarihin gwajin nukiliya

Shekara ɗaya bayan harin makamin nukiliya na Amurka a Japan a 1945 ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a kawo ƙarshen amfani da makamin baki ɗaya.

Amma a watan Agustan 1949, Tarayyar Soviet ta yi gwajin makamin da ta kira First Lightning a Kazakhstan.

A watan Oktoban 1952, Birtaniya ta yi gwajin makamin na farko a Tsibirin Montebello da ke kusa da gaɓar shiga kudancin Australia. Sannan daga baya ta sake gudanar da wasu gwaje-gwajen a Maralinga da Emu da ke kudancin Australia.

Bayan wata ɗaya ne kuma Amurka ta yi gwajin makaminta na sinadarin hydrogen a Tsibirin Islands. Bam ɗin ya fi wanda ta jefa a Japan ƙarfi da kusan ninki 500.

A shekarar 1960 ce Faransa ta bi sawu, inda ta zama ƙasa ta huɗu da aiwatar da gwajin nukiliya.

Bayan shekara ɗaya ne kuma Tarayyar Soviet ta yi gwaji makami mafi girma a lokacin da aka saka wa suna Tsar Bomba a arewacin Rasha.

Yarjejeniyar hana gwajin

A 1963 aka shiga yarjejeniyar hana gwajin makamin nukiliya da aka kira Limited Test Ban Treaty (LTBT), lamarin da aka tsara taƙaita gwaje-gwajen makaman a sararin samaniya.

Amma sai China ta yi gwaji makaminta a shekarar 1964, kimanin shekara ɗaya bayan yarjejeniyar.

Amma a lokacin, an riga an tabbatar da cewa Amurka da Tarayyar Soviet da Birtaniya da China suna da makamanin na nukiliya.

Wannan ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙirƙiri wata sabuwar yarjejeniyar da za ta hana yaɗuwar makamnin da ta kira Non-Proliferation Treaty (NPT).

An fara amfani da yarjejeniyar ne a shekarar 1970, amma har yanzu wasu ƙasashe ba saka hannu ba.

India ta shiga cikin ƙasashen masu nukiliya ne bayan ta harba nata a karon farko a 1974.

A shekarar 1998 ce ita ma Pakistan ta harba makamin a karon farko domin gwaji.

Duka ƙasashen biyu ba sa cikin yarjejeniyar taƙaita yaɗuwar makamin nukiliya ta NPT.

Isra'ila dai an kasa gane gabanta da bayanta, inda ta ƙi bayyana ko tana da makamin nukiliya ko ba ta da shi.

Koriya ta Arewa da farko ta shiga yarjejeniyar, amma ta fice a shekarar 2003.

Amurka ta yi ikirarin cewa China ta yi gwajin makamin a shekarar 2020, wanda shi ne karon farko da aka samun labarin tayar da makamin tun daga tsakanin shekarun 1990s.

Yarjejeniyar haramta gwaji

Bayan gwajin Rasha a 1991 da na Amurka a 1992 ne aka fara tsara yarjejeniyar hana gwajin makamin da aka kira Comprehensive Test Ban Treaty (CTBT).

Yarjejeniyar ta CTBT ce ta haramta dukkan wani gwaji na makamin nukiliya, sannan ta kafa cibiyoyin sa ido da bibiya.

Ƙasashe 187 ne suka sa hannu a yarjejeniyar, sannan ƙasashe 178 suka tabbatar.

Sai dai ba za a tabbatar da yarjejeniyar ba sai ƙasashe 9 manya, wato China da India da Pakistan da Koriya ta Arewa da Isra'ila da Iran da Masar da Rasha da Amurka sun sa hannu.

A shekarar 2023 ce Rasha ta ce ta janye daga yarjejeniyar.

Editan da ya tace labarin: Andrew Webb