Birtaniya ta amince da shirin tsaro na jirage marasa matuƙa da kawayenta na EU
Biritaniya za ta shiga yarjejeniya ƙirkiro sabbin dabarun kariya ta sama tare da manyan ƙasashe huɗu masu karfin soja na ƙungiyar EU.
Aikin zai ƙunshi gayyato masu ƙere-ƙere daga Birtaniya da Jamus da Farans da Italiya da Poland don gabatar da shirye-shiryen ƙera makamai masu linzami masu rahusa da jirage marasa matuƙa.
Ƙawancen ƙasashen sun yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa na ƙera makaman tare, sakamakon jiragen da Ukraine ta ƙera masu arha don daƙile hare-haren da Rasha ke kai wa.
Ma'aikatar tsaro ta Birtaniya (MoD) ta ce shirin zai fi mayar da hankali kan makamai "marasa nauyi kuma masu araha".