Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Jum a'a 20 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Birtaniya ta amince da shirin tsaro na jirage marasa matuƙa da kawayenta na EU

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Biritaniya za ta shiga yarjejeniya ƙirkiro sabbin dabarun kariya ta sama tare da manyan ƙasashe huɗu masu karfin soja na ƙungiyar EU.

    Aikin zai ƙunshi gayyato masu ƙere-ƙere daga Birtaniya da Jamus da Farans da Italiya da Poland don gabatar da shirye-shiryen ƙera makamai masu linzami masu rahusa da jirage marasa matuƙa.

    Ƙawancen ƙasashen sun yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa na ƙera makaman tare, sakamakon jiragen da Ukraine ta ƙera masu arha don daƙile hare-haren da Rasha ke kai wa.

    Ma'aikatar tsaro ta Birtaniya (MoD) ta ce shirin zai fi mayar da hankali kan makamai "marasa nauyi kuma masu araha".

  2. Har yanzu akwai yiwuwar za mu kai wa Iran hari - Trump

    ...

    Shugaba Trump ya sake jaddada cewa yana duba yiwuwar kai wa Iran harin soji a wasu wurare, idan har ta kasa cimma matsaya kan shirinta na nukiliya.

    Kalaman nasa na zuwa ne jim kaɗan bayan ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran za ta yi daftarin shawarwarin cimma yarjejeniya a cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

    Rukuni na biyu na jirgin ruwa da ke ɗauke jiragen sama yaƙin Amurka ya na tekun baharum a tafiyar da ya ke yi domin haɗewa da sauran sojoji da ke shirin kai wa Iran farmaki.

    Wakiliyar BBC ta ce jirgin shi ne jirgin yaƙi mafi girma a dunya kuma yanzu ya wuce tekun Gibraltar ya na tekun baharum

  3. Gwamnatin Birtaniya na tunanin cire Andrew daga jerin masu gadon sarauta

    ...

    Asalin hoton, PA Media

    BBC ta fahimci gwamnatin Birtaniya ta na tunanin gabatar da doka don cire Andrew Mountbatten-Windsor daga layin waɗanda ka iya gadon sarautar ƙasar.

    Matakin, wanda zai hana Mountbatten-Windsor zama Sarki, zai zo ne bayan kammala binciken ƴan sanda.

    Dan uwan ​​Sarkin ya ci gaba da zama na takwas jerin masu iya gadon sarautar duk da cewa an ƙwace masa mukamansa, da suka haɗa da na "yarima", a watan Oktoban da ya gabata sakamakon matsin lamba kan alaƙarsa da Jeffrey Epstein.

    A ranar Alhamis, ƴan sanda sun saki Mountbatten-Windsor bayan kama shi bisa zarginsa da aikata rashin ɗa'a a ofishin gwamnati.

    Ya dai ci gaba da musanta aikata wani laifi.

  4. Gwamnatin Kebbi ta bai wa iyalan mutanen da aka kashe gudumawar kuɗi

    Kebbi

    Asalin hoton, Kebbi State Government

    Gwamnatin jihar Kebbi ta ba da tabbacin tsaro ga al’ummomin yankunan da ke cikin mawuyacin hali a duk sassan jihar sakamakon matsalar rashin tsaro.

    Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Umar Tafida wanda ya bada wannan tabbacin a madadin gwamna Nasir Idris yayin da ya kai ziyarar jajantawa mazauna ƙauyukan da suka samu raunuka a hare-haren baya-bayan nan a garuruwan Mamuni da Awashaka da Kurin-Naida da Tungar Tsoho da Danmairago da kuma Makargara- dukkansu, ya ce gwamnatin jihar na daukar lamarin da muhimmanci.

    Ya ce gwamnatocin jihohi da na tarayya suna aiki tare don shawo kan lamarin ta hanyar zakulo wuraren da za a kara zuba jari a gine-ginen tsaro tare da yin taka-tsan-tsan wajen kai wa ‘yan bindigar hari a maboyarsu.

    Mataimakin gwamnan ya yi kira ga jama’a da su ƙara bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar samar da bayanai masu amfani kan harkar ƴan bindiga.

    Wasu daga cikin mazauna ƙauyen da suka yi jawabi yayin ziyarar Mataimakin Gwamnan, sun yabawa sojoji bisa ɗaukin gaggauwa da suka kawo yi a lokacin da aka kai harin, inda suka ce yin hakan ya ceci rayuka da dama.

  5. Rasha ta musanta shigar da ƴan Kenya cikin yaƙinta da Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Rasha da ke Nairobi ya musanta cewa ya ɗauki ƴan ƙasar Kenya aikin soji domin su taimaka mata a yaƙinta da Ukraine, yana mai yin alla-wadai da abin da ya kira “farfaganda mai cike da hatsari da yaudara” da ke faruwa a cikin kafafen yaɗa labarai na Kenya.

    Wannan bayanin na zuwa ne bayan wani bincike da hukumar leƙen asiri ta Kenya ta gudanar ya gano cewa sama da ƴan ƙasar 1,000 ne ke aiki tare da sojojin Rasha.

    Akasarin ƴan ƙasar da ke taya Rasha yaƙin an yaudaresu ne da alƙawurran biyansu albashi mai tsoka da kuma ba su izinin zama ƴan ƙasashen waje.

    "Hukumomin gwamnatin Rasha ba su taɓa shiga aikin ɗaukar ƴan ƙasar Kenya aiki ba bisa ƙa'ida ba a cikin rundunar sojojin Tarayyar Rasha," in ji ofishin jakadancin.

    Ta ƙara da cewa, ba ta taɓa bayar da biza ga ƴan ƙasar Kenya da ke neman zuwa Rasha musamman don fafatawa a yaƙin da ake yi da Ukraine ba.

    Ofishin jakadancin dai ya yi bayanin cewa dokokin ƙasarsa sun bai wa baƙi da ke zaune bisa doka a Rasha damar shiga cikin sojojinta bisa son ran su.

  6. Kotun soji a Kamaru ta ɗaure sojoji uku kan kisan fararen hula 21

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotun soji a Kamaru ta yankewa sojoji uku da wani ɗan ƙungiyar sa-kai hukuncin ɗaurin kurkuku bisa samunsu da laifin kashe akalla fararen hula 21 a yankin Arewa maso Yamma mai rinjayen masu magana da Turanci.

    Lamarin ya faru tun watan Fabrairun 2020 a ƙauyen Ngarbuh, amma shari’ar ta shafe kusan shekara shida ana yi kafin yanke hukunci.

    An same su da laifukan kisa da ƙone dukiya da lalata kadarori, inda aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari tsakanin shekara biyar zuwa goma.

    Wannan hari na daga cikin lokuta kaɗan da gwamnati ta amince dakarunta sun aikata laifi, domin a farko hukumomi sun musanta hannu a lamarin kafin daga bisani suka amince bayan matsin lamba daga ƙasashen duniya.

    Lauyoyin waɗanda abin ya shafa sun bayyana rashin gamsuwarsu da hukuncin, suna cewa girman laifin da aka aikata ya kamata a zartar da hukunci mafi tsauri fiye da haka.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun sha zargin ɓangarorin biyu, wato ’yan aware da dakarun gwamnati, da aikata ta’asa tun bayan ɓarkewar rikicin yankunan masu magana da Turanci a 2017.

    A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane dubu shida tare da raba sama da rabin miliyan da muhallansu.

  7. Miliyoyin mutane na cikin haɗarin fuskantar yunwa mai tsanani a Somaliya - WFP

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shirin abinci na Duniya (WFP) ya bayyana cewa miliyoyin mata, maza da yara a Somalia na cikin haɗarin fuskantar yunwa mai tsanani sakamakon ƙarancin abinci da rikici da rashin tsaro, da kuma ƙarancin tallafin abinci da ake samu.

    Wannan matsalar na iya kai wa ga bala’i idan ba a samu taimakon gaggawa ba.

    Daraktan Shirye-shiryen Gaggawa da Ayyukan Bincike na WFP, Ross Smith ya ce: “Yanzu muna ganin kashi ɗaya bisa huɗu na al’umma kimanin mutane miliyan 4.4 kenan na cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki.

    Daga ciki akwai kusan mutum miliyan ɗaya da ke fama da yunwa mai tsanani, yayin da yara kusan miliyan biyu ke fama da ƙarancin abinci ciki har da fiye da 400,000 da ke cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki”

    Rashin kuɗaɗen tallafi ya sa WFP ya rage yawan tallafin abincin da yake bayarwa.

    Binciken WFP ya nuna cewa a cikin watanni biyar da suka gabata, kimanin mutane dubu 500 sun rasa matsugunansu sakamakon rikici da yanayin rashin tsaro.

  8. Mun kashe kwamandan Boko Haram - Sojojin Najeriya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya sun sanar cewa dakarunsu sun kashe wani kwamandan Boko Haram mai suna Abdullahi Mafa a yayin hare-haren da suke ci gaba da kai wa ƙungiyar a jihohin Borno da Adamawa.

    Mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kashe Mafa ne a yankin kogin Visik da ke ƙaramar hukumar Madagali, inda suka kuma ƙwace bindigar AK-47 da alburusai

    Sanarwar ta ce dakarun sun kama wani da ake zargi mai suna Dauda Usman Gubula wanda ake zargin yana samar wa ‘yan ta’adda jirage marasa matuƙa da suke gyarawa su riƙa amfani da su wajen kai hari.

    An same shi da jirage marasa mayuka guda biyu da kayan haɗinsu da kuma na'urar bayar da wuta ta hasken rana guda 20.

  9. 'Hamas na zaɓen sabon shugaba a asirce'

    Hamas na gudanar da zaɓen sabon shugaban rikon ƙwarya a fadin Gaza da yanki na gaɓar yamma da Kogin Jordan da kuma tsakanin mambobin Hamas a asirce kamar yadda wani jami’i ya shaida wa BBC.

    Sakamakon zaɓen na iya nuna wane irin shugabanci ƙungiyar ke shirin ɗauka, musamman yayin da Amurka da wasu masu shiga tsakani ke tattaunawa kan yadda za a gudanar da Gaza bayan yaƙi a nan gaba.

    Zaɓen na zuwa ne bayan mafi yawan manyan shugabannin Hamas sun rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila bayan harin Hamas na 7 ga Oktoba, 2023 a kan Isra’ila, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutum 1,200 da kuma sace wasu 251.

    Mutane a Gaza sun riga sun kaɗa ƙuri'unsu a asirce, in ji majiyar, amma ba a fayyace ko an kammala aikin zaben a wasu wurare ba.

    Za a sanar da sabon shugaban nan gaba, wanda zai riƙe mukamin na tsawon shekara guda.

  10. Fiye da mutum miliyan 1.5 ne suka karɓi katin zaɓe gabanin zaɓen Abuja- INEC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bayyana cewa fiye da masu zaɓe miliyan 1.5 ne suka karɓi katin zaɓe a duk faɗin babban birnin tarayya, Abuja kafin zaɓen majalisar kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu, 2026.

    Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta nuna cewa har zuwa ƙarshen karɓar katunan a ranar 10 ga Fabrairu, an yi rajistar masu zaɓe 1,680,315 a Abuja, inda mutum 1,587,025 suka karɓi katin zaɓe, yayin da katunan 93,290 suka rage ba a karɓa ba.

    Hukumar ta jaddada cewa waɗanda suka yi rajistar zaɓe kuma suka ansa kati ne kawai za su samu damar kada kuri’a a ranar zaɓe.

    INEC ta ce ta shirya dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zaɓe mai gaskiya.

  11. Mun bai wa Iran kwana 10 ko su amince da yarjejeniya ko su gani a ƙwaryarsu - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka ta bai wa Iran wa’adin kwanaki 10 don su amince da yarjejeniya kan shirinta na nukiliya, in ba haka ba Amurka za ta ɗauki matakin soja, kuma duniya za ta san abin da zai faru.

    A taron farko na shirin samar da zaman lafiya da ya jagoranta a Washington DC, Trump ya ce a tattaunawar da ake yi da Iran: “Dole ne mu cimma yarjejeniya mai ma’ana, in ba haka ba abubuwa masu muni za su faru.”

    A ‘yan kwanakin nan, Amurka ta ƙara tura sojoji zuwa Gabas ta Tsakiya, yayin da aka samu rahotanni na ci gaban tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da Iran a Switzerland.

    ‘Yan majalisar dokoki na jam’iyyar Democrats da wasu na jam’iyyar Republicans sun nuna rashin amincewa da duk wani matakin soja a Iran ba tare da izinin majalisa ba.

    Gwamnatin Iran ta shaida wa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya cewa za ta ɗauki sansanonin soja na Amurka a yankin a matsayin wuraren hari idan kai hari kan Iran.

  12. Gobara ta sake tashi a wata kasuwa a Kano

    ...

    Wata gobara ta sake tashi a Kasuwar Fatima Bread Kwalema da ke unguwar Dakata a birnin Kano

    Gobarar ta cinye shaguna fiye da 50 da injinan sarrafa man girki da robobi.

    Har yanzu dai ba a san abun da ya haddasa gobarar ba.

    ...

    Wannan lamari na zuwa ne 'yan kwanaki bayan gobarar da ta tashi a kasuwar Singer da ke jihar, wacce ta lalata shaguna da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira inda gwamnatin tarayya ta bayar da naira biliyan 5 domin tallafa ‘yan kasuwar Singerda gobarar ta shafa.

    ...

    Kano ita ce jihar da ta fi yawan al'umma a arewacin Najeriya kuma jiha mai daɗaɗɗen tarihin hada-hadar kasuwanci a yammacin Afirka.

    ...

    A lokutan hunturu, wanda ke farawa daga ƙarshen shekara zuwa farkon sabuwar shekara ana yawan samun faruwar gobara a arewacin Najeriya sanadiyyar kaɗawar iska.

  13. Sojojin Najeriya sun kama mai ƙerawa Boko Haram jirage marasa matuƙa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wasu mutane da ke aiki tare da Boko Haram da kuma wani mai samar da jirage marasa matuƙa yayin da suke ci gaba da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda a jihohin Adamawa da Borno.

    Cikin wani saƙo da rundunar sojin ta wallaf a shafinta na X, ta ce an samu nasarar kamen ne bisa haɗin kai masu gadi da mafarauta.

    Sojojin sun ce a ranar Alhamis, sojojin sun kama Ismail Muhammed, mai shekaru 28, a yankin Visik na ƙaramar hukumar Hong, inda aka samu bindiga da sauran makamai da kayan soji da abinci iri-iri ttattare da shi.:

    Rundunar ta ce ta tsare shi a gidan yari domin ci gaba da bincike.

    Sojojin sun kuma ce a wani aiki daban a ƙaramar hukumar Madagali, an hallaka Abdullahi Mafa, wani kwamadan Boko Haram yayin da ake kai hari a layin Kogin Visik.

    ''Haka kuma, dakarun sun kama wani Dauda Usman Gubula, mai shekaru 64, wanda ke samar da jirage marasa matuƙa ga ‘yan ta’adda domin kai hare-hare kan sojoji'', in ji sanarwar.

    Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kuma daƙile wani hari da yanbindiga suka shirya kai wa a Ngamdu, Jihar Borno, sannan sun hallaka wani mai bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda da ke ƙoƙarin ƙetare shingen tsaro.

  14. Jami'ai za su ci gaba da binciken gidan Andrew Mountbatten-Windsor bayan sakinsa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran jami’an ‘yan sandan Biritaniya za su ci gaba da binciken tsohon gidan Andrew Mountbatten-Windsor, da ke kusa da birnin London, bayan sakinsa a ranar Alhamis.

    Ana tuhumar yariman - wanda ƙani ne ga Sarkin Ingila - da zargin cewa a lokacin da yake jakadan cinikayya na Biritaniya fiye da shekaru goma sha biyar da suka wuce, ya raba wasu takardun gwamnati ga marigayi Jeffrey Epstein wanda aka kama da laifin cin zarafi ta hanyar lalata.

    Toshon yariman ya musanta duk wani laifi da ake tuhumarsa da shi a baya.

    Kamun da aka yi masa ya haifar da ƙarin kiraye-kirayen da ake yi a Amurka ga jami’an ƙasar su ɗauki matakai masu tsauri kan duk wanda ke da alaƙa da Epstein.

    Hukumomin Biritaniya sun ce binciken zai ci gaba har sai an kammala gano duk wasu bayanai da suka shafi zargin

  15. Za mu kai hari kan sansanonin soji a Gabas ta Tsakiya idan aka kawo mana hari - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta shaida wa Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres cewa zata ɗauki sansanonin soji a yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin wuraren da za ta kai wa hari muddin aka kai mata hari.

    Shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Iran ya ce take-taken shugaba Trump, na nuna alamun zai iya kai hari a kowanne lokaci, to amma kuma Iran 'ba ta son yaƙi'.

    Tun da farko, Trump ya keɓe wa'adin kwanaki 10 zuwa 15 ga Iran domin ta cimma yarjejeniya akan shirinta na nukiliya.

    Trump ya ce idan har ta gaza hakan to abin da zai biyo baya ba zai mata dadi ba.

  16. Shugabar Venezuela za ta yiwa fursunoni afuwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar gwamnatin riƙon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, ta sanya hannu kan wani ƙudurin yin afuwa wanda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam suka ce matakin zai kawo sauƙi ga daruruwan fursunonin siyasa a ƙasar.

    Fursunonin siyasa a Venezuela an kiyasta cewa sun kai 600, amma babu tabbas kan waɗanda za a saki.

    Masu fafutika sun ce matakin afuwar bai shafi fursunonin da aka samu da jagorantar tawaye ba, da laifin rashawa da kuma wallafa saƙonni na adawa ga gwamnati a kafofin sada zumunta.

    Wannan kuma zai iya shafar shugabar adawar ƙasar wadda ta lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya, Maria Corina Machado, wadda jam’iyya mai mulkin ƙasar ta zarga da neman ɗaukin ƙasashen duniya, matakin da ya kai ga hambarar da Shugaba Nicolas Maduro.

  17. Jami’an ICPC sun bincika gidan El-Rufai da ke Abuja

    ...

    Asalin hoton, Muyiwa Adekeye/X

    Jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC sun binciki gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Abuja a ranar Alhamis.

    Mai bai wa tsohon gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

    A cewarsa, j"ami’an hukumar sun isa gidan El-Rufai inda nan take suka fara binciken dukkan sassan gidan.

    Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya yi Allah wadai da matakin, yana mai cewa "binciken da jami'an suka yi ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saba wa dokoki da haƙƙoƙin ɗan Adam.”

    Tun a ranar Laraba hukumar ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannunta dangane da wani bincike da take yi.

    Hukumar ba ta bayar da cikakken bayani kan irin binciken da ake yi a kansa ba.

  18. Jihohin Najeriya da suka fi yin kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

    ....

    Asalin hoton, Social media handles

    Yayin da aka shiga wata na biyu a shekarar 2026, tuni gwamnonin jihohin Najeriya suka fara gudanar da wasu daga cikin ayyukan da suka tsara cikin kasafin kuɗin shekarar.

    A wanann shekarar jihohin sun ƙara kuɗaɗe masu yawa cikin kasafinsu na shekarar da muke ciki, wani abu da ke nuna yadda jihohin ke samun ƙarin kuɗaɗe daga tarayya.

    Jihohi da dama sun kafa hujja da burin gudanar da manyan ayyukan ci gaba wajen ƙara yawan kuɗaɗen da za su kashen a 2026.

    Haka ma wasu jihohin sun ce ƙaruwar hauhwar farashin kayyaki da raguwar darajar kuɗin na daga cikin dalilan da suka kasafin kuɗaɗen nasu ya ƙaru.

    A wannan shekarar jihohin ƙasar da dama ne suka yi kasafin da ya haura naira tiriliyan ɗaya, kamar yadda wasu bayanai da ƙungiyar BudgIT mai nazari kan kasafin kuɗi a ƙasar suka nuna.

  19. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.