Wane tasiri rinjayen APC a Majalisar dokokin Najeriya zai yi ga dimokuraɗiyyar ƙasar?

Lokacin karatu: Minti 5

An samu hargitsi a zaman majalisar dokokin Najeriya na ranar Talata bayan ƴan majalisa na jam'iyyun adawa sun yi zargin cewa an yi musu ƙarfa-ƙarfa wajen tilasta amincewa da dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyara.

Lamarin ya kai ga cewa wasu ƴan majalisar wakilai sun fice daga zauren majalisar domin nuna adawa.

Duk da haka zaurukan majalisar biyu - wakilai da dattijai - sun amince da dokar zaɓen wadda aka yi wa garanbawul.

Wani faifan bidiyo da ke nuna yadda aka samu hatsaniya a zaurukan majalisar na ranar Talata 17 ga watan Fabarairu sun haifar da muhawara a fadin ƙasar game da gagarumin rinjayen da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta samu a baya-bayan nan.

A gyare-gyaren da aka yi wa dokokin zaɓen ƙasar, hankali ya koma kan sashe 60, sakin layi na 3 ne, wanda ke magana a kan aika sakamakon zaɓe ta lataroni kai-tsaye daga akwatunan zaɓe.

Gyara da aka yi a yanzu shi ne, "baturen zaɓen zai tura sakamakon zaɓen ta lataroni ne kai-tsaye daga akwatin zaɓe, sannan za a aika sakamakon ne bayan an cika fom ɗin EC8A, sannan baturen ya saka hannu, ya saka tambarin INEC, sannan wakilan jam'iyyu ko ƴantakara sun saka hannu."

"Amma a wuraren da babu ingantaccen sadarwa, wanda ya zama ba za a iya aika sakamakon kai-tsaye ta lataroni ba, sai a yi amfani da sakamakon da aka rubuta a EC8A, baturen zaɓe ya saka hannu da tambarin INEC, sannan wakilan jam'uyyu ko ƴan takara suka saka hannu."

Tun da farko dai an fara samun kai-komo ne bayan majalisar dattawa ta amince da gyare-gyaren da ta yi, sannan ita ma majalisar wakilai ta amince da nata.

A ƙa'ida, idan aka samu saɓani, majalisun biyu za su zauna ne domin haɗa rahotannin biyu, a fitar da guda ɗaya.

Ƙarfa-ƙarfa aka mana - Tambuwal

Da yake bayani kan bore da hargitsin da aka samu a zauren majalisar dattijai, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya da yin ƙarfa-ƙarfa wajen amincewa da wani sashe na dokar zaɓe ba tare da yin gyara ba, yana mai cewa an yi hakan ne duk da rashin amincewar ɓangaren marasa rinjaye.

A hirarsa da BBC, Tambuwal ya ce hatsaniya ta ɓarke ne a zauren majalisa sakamakon yadda aka ƙi amincewa da buƙatar 'yan adawa na a sake duba sashen dokar.

A cewarsa, abin da aka fara gabatarwa shi ne buƙatar hukumar zaɓe ta sauya kwanakin bayar da sanarwa daga kwana 360 zuwa 300 domin daidaita jadawalin da ya faɗo a lokacin azumin shekara mai zuwa.

Ya ƙara da cewa, "Karfa-ƙarfa aka mana wajen amincewa da wani sashe na dokar zaɓe," yana mai cewa bayanan da suka samu sun nuna shugabannin majalisun biyu da kwamitocin daidaito sun zauna tare da cimma matsaya inda aka fi karkata ga abin da majalisar dattawa ta amince da shi.

Tambuwal ya ce "a lokacin ne muka nuna rashin amincewa" inda ya ce dole ne a bari a yi zaɓe a fili domin kowa ya bayyana matsayarsa."

Ya kuma jaddada cewa " muna ganin hakan hakan zai ba da wata hanya ta yadda za a iya yin magudin zaɓe wanda shi ake ƙoƙarin a magance."

Shin APC na buƙatar taimakon jam'iyyun adawa?

A Najeriya, za a iya cewa jam'iyyar APC ta yi kaka-gida a zauruka biyu na majalisar dokokin ƙasar, inda zuwa yanzu APC ke da ƴan majalisa 241 da sanatoci 80.

Ana dai buƙatar kashi biyu bisa uku na yawan ƴan majalisa ne domin samun wuƙa da nama wajen ɗabbaƙawa ko tabbatar da wata doka ko buƙata da ɓangaren zarwasta ya aika majalisa.

Yanzu za a iya cewa jam'iyyar APC kaɗai ta samu biyu bisa uku a duk majalisun biyu, wanda hakan ya sa wasu ke ganin ba ta buƙatar taimakon jam'iyyun hamayya wajen aiwatar da abin da take so.

Yanzu APC tana da kujeru 241 daga cikin 360, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, duk da cewa a farkon rantsar da ƴan majalisar a ranar 13 ga watan Yunin 2023, kujera 175 kawai jam'iyyar take da su.

A farkon majalisar, jam'iyyun hamayya ne suke da kujeru 182, inda PDP ke da 116, LP ke da 35, NNPP ke da 19, APGA ke a biyar, sai ADC da SDP da YPP kowannensu ke da biyu, sai guda uku da ake kai-komo kan su a kotu.

A majalisar dattawa, yanzu APC na da kujera guda 80, PDP na da 21, LP na da uku, APGA na da biyu, sannan NNPP na da ɗaya, inda jimillar ta zama 107, sai biyu da suka rasu.

A lokacin rantsar da su a watan Yunin 2023, APC na da kujera 59, PDP na da 36, LP na da 8, NNPP na da biyu, sai SDP da APGA da take da sauran.

Barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya

Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano ya ce boren da aka samu ya nuna akwai matsala.

Ya ce abin da ake iya gani a majalisar na nuna cewa masu nuna rashin amincewa suna da yawa, "shi ya sa tun farko wasu ke ganin bai kamata a riƙa zaɓe a majalisa da murya ba."

Sufi ya ce za a iya samun amon muryar ya zama ɗaya ko kuma waɗanda ba su amince ba ma su fi yawa, "amma idan shugabancin majalisar sun fi kartata kan amincewa, sai su buga su ce an amince," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa hakan na barazana ga dimokuraɗiyya.

Ya ƙara da cewa, "yawanci mutane suna gani idan an zo abu mai muhimmanci irin wannan, zai fi kyau a yi ƙuri'ar kai da halinka maimakon zaɓen murya, domin abin da ya faru jiya, muryar rashin amincewa ta fi yawa."

A game da yadda jam'iyyar APC take da adadin ƴan majalisar da suka haura biyu bisa uku a dukkan majalisun, Kabiru Sufi ya ce samun rinjaye ba matsala ba ne, matsalar ita ce danne jam'iyyun hamayya.

"Adawa dai na da muhimmanci a siyasa, ko da jam'iyya mai mulki na da rinjaye, idan samun rinjayen ya yi yawan gaske har ya zama za su iya aiwatar da komai ba tare da fargabar fuskantar wani ƙalubale ba, wanda kuma hakan nakasu ne ga dimokuraɗiyya."

Ya ce da a ce zaɓen ƙada ƙuri'a aka yi, wasu ƴan jam'iyyar mai mulki za su iya kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa, "musamman idan aka yi ƙuri'ar a cikin sirri," in ji Kabiru Sufi a zantawarsa da BBC.

Masanin harkokin siyasar ya ce wata babbar barazanar da ake fuskanta ita ce yadda ɓangaren zartaswa ke katsalandan kan harkokin majalisa da ɓangaren shari'a a Najeriya.

"A zahirin gaskiya abin da ya nuna ke nan, kuma ba haka ya kamata ba. Kamata ya yi kowane ɓangare ya ci gashin kansa wato majalisa da shari'a da zarwarsa. Idan ya zama zarwatsa na danne sauran ɓangarorin, to lallai an samu matsala."

Sufi ya ce ganin yadda ɓangaren zartaswa ke katsalanda a majalisa da shari'a, "da kuma irin ƙarfin da zarwatswa ke da shi, za a iya cewa dimokuraɗiyyar Najeriya ta samu babban tasgaro musamman idan aka yi nazarin yadda ake yi a duniya, da yadda take a Najeriya."