Yadda 'yanbindiga suka tilastawa wasu 'yan Najeriya tserewa zuwa Benin

Lokacin karatu: Minti 2

Daruruwan al'ummar jihar Neja da ke Najeriya, sun tsere zuwa Jamhuriyar Benin domin neman mafaka, sakamakon hare-haren da 'yanbindiga ke kai wa a yankunan.

Rahotanni sun ce an kai wani sabon hari a baya-bayan nan wasu ƙauyukan kananan hukumomin Borgu da Agwara , inda aka ƙone gidaje da dama.

Harin ya bar al'ummar yankunan rasa tudun dafawa, hakan ne ya sa suka yanke shawarar neman mafaka a Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa, da suka shiga da farko sai mutanen garuruwan suka ji tsoro suka gudu sannan kuma suka bar kayayyakinsu kamar kayan amfanin gona da tufafi da dai sauransu, hakan ne ya sa 'yanbindigar suka sake komawa garin tare da kona shi duka.

"Da suka koma garin ba su samu kowa ba, shi ne suka kone shi, kuma mutanen garin da suka tsere zuwa Jamhuriyar Benin yanzu haka suna cikin kwanciyar hankali domin gwamnatin can tana yakar 'yanbindigar." In ji shi.

" Ko a shekaranjiya a garin Gine, an kashe kusan mutum 100, don haka a yanzu muna cikin halin tsoro sosai." In ji shi.

Injiniya Abdurrahman Bala Gambo, danmajalisar da ke wakiltar karamar hukumar Bargu da kewaye, ya tabbatar wa da BBC afkuwar lamarin, in da ya ce sun shiga garin Konkoso, sun kora mutane amma ba su kashe kowa ba saboda mutane sun fita sun bar garin.

"Yawancin mutanen sun tsere Jamhuriyar Benin domin yawanci suna da 'yan'uwa a can shi ya sa suka koma domin neman mafaka, kuma fushin 'yanbindigar sun koma garin ba su ga kowa ba ne ya sa suka kona garin." In ji danmajalisar.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a Najeriya duk da isowar sojojin Amurka a arewacin kasar don tallafawa dakarun Najeriyar wajen kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar.