Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin Kwara: 'Sun kashe kowa' sai wanda Allah ya tseratar
- Marubuci, Makuochi Okafor
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 5
’Yan bindiga fiye da 100 ɗauke da makamai, kuma sanye da kayan soji ne suka shiga ƙauyukan Woro da Nuku, waɗanda akasari Musulmi ne a ciki, da ke jihar Kwara kan babura - domin ɗaukar fansa.
''Sun zo da yawan su da sunan yaɗa addini, sai kuma daga bisani suka zaɓi kashe mutanenmu'', kamar yadda Abdalla Umar Usman, wani tsohon malami kuma mazaunin Woro ya shaida wa BBC, yana bayyana yadda aka kai harin, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum aƙalla 75.
An kai harin ne da yammaci kafin rana ta faɗi a ranar Talata, a yayin da mutanen ƙauyukan, waɗanda akasari manoma ne ke komawa gidajensu daga gonakin su inda suke noman doya da masara da kuma gero.
Mayaƙan sun tafi kai tsaye gidan wani basarake Umar Bio Salihu, saboda tun a baya sun aika masa wasiƙu suna neman izinin zuwa yin wa'azi kan abin da ake gani tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci ne, sai dai al’ummar kauyukan sun ƙi amincewa.
Salihu ba ya gidansa na Woro a wannan lokacin, saboda haka sai suka ƙona gidansa tare da kashe ƴaƴansa biyu.
''An kashe yaran basaraken biyu, waɗanda ɗalibai ne da ke koyon aikin likitanci a gaban gidansu kafin a cinna wa gidan wuta,'' In ji Usman.
Daga nan sai ƴan bindigar suka ci gaba da kashe mutane har cikin dare.
''Sun kashe kowa. Lamarin ya yi muni,'' in ji Mohammed Dauda.
Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Amnesty International ta ce an gano gawarwaki da hannayensu da ƙafafunsu a ɗaure, wasu an yanka maƙogwaronsu, wasu kuma an harbe su.
Da ƴan bindigar suka tafi da safiya, sun tafi da mata da yara 38, ciki har da sauran iyalin basaraken ƙauyen.
''Sun kashe ƴaƴana biyu, kuma sun yi garkuwa da matata da ƴarana uku,'' a cewar Salihu.
Ƴan bindigar na so mazauna ƙauyen su barranta daga gwamnatin Najeriya da kundin tsarin mulkinta, a maimakon hakan su bi koyarwarsu, a yunƙurinsu na kafa tasu gwamnatin a yankin.
Wannan ya ''saɓa wa koyarwar Qur'ani,'' in ji Salihu.
Gwamnatin Najeriya ta ɗora alhakin harin kan ƙungiyar Boko Haram - sai dai ƙungiyar ba ta fitar da sanarwa ba game da hakan.
Ƙungiyar, wadda ta ja hankalin duniya a 2014 bayan da ta sace ƴan mata fiye da 200 a Chibok, har yanzu ta na aiki a yankin arewa maso gabashin ƙasar wadda tuni ta rarrabu.
Ɗaya daga cikin ɓangaren ƙungiyar, Mahmuda, a yanzu ta na tafka ta'asa a ƙauyuka da dama na Kwara da kuma jihar Neja mai makwaftaka.
A cewar ƙungiyar Amnesty, mayaƙan sun yi ta aika wasiƙa ga ƙauyukan biyu tsawon watanni biyar da suka gabata.
'' An yi ta aike wa ƙauyukan takardu, suna buƙatar su su bi tsauraran ra'ayoyinsu da koyarwarsu,'' kamar yadda Isa Sanusi, shugaban ƙungiyar Amnesty International ya shaida wa shirin Newsday na BBC.
''Bayan sun fuskanci turjiya daga mutanen, sai suka fara aika musu da gargaɗi,'' in ji shi.
Maganar shi ta yi daidai da bayanan Usman - na cewa an aike wa ƙauyukan gargaɗi kwanaki kafin kai harin.
Wani ɗan majalisa a jihar Saidu Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa an aika wa Salihu wasiƙar ƙarshe, wanda ya shaida wa jami'an tsaro.
Sojoji sun je yankin na ɗan gajeren lokaci domin yin bincike, amma bayan sun tafi, sai ƴan bindiga suka ƙaddamar da harin, in ji shi.
Amnesty ta ce hakan na nuna gazawar jami'an tsaro.
''Muna mamakin yadda aka bari aka samu wannan giɓin a fannin tsaron, yadda hukumomi suka kasa ɗaukar mataki, '' a cewar Sanusi.
Ya bayyana yadda aka shafe sa’o'i ba a kai wa ƴan ƙauyen ɗauki ba, har ƴan bindigar suka ci karensu babu babbaka.
"Har massalaci ma suka je suka yi sallah. Sun kuma tilasta wa wasu mutanen zuwa su ji wa'azinsu. Wanda hakan ke nufin sun samu lokaci mai tsawo, wanda ya ba su damar yin duk abin da suka ga dama, '' a cewar Sanusi.
Jam'ian tsaro sun isa garin kwana ɗaya bayan harin, inda suka samu sassa da dama na Woro da Nuku, waɗanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kaiama sun zama kango.
An ƙona shaguna da gidaje, babura da aka yi watsi da su a jere a kan titi, sai kuma hayaƙi da ya ke shawagi a sararin samaniya.
Shagunan kasuwanni da a baya ke cike da mutane sun kasance babu kowa, a yayin da iyalai suka taru suna jajanta wa juna.
Daga nan kuma aka fara aikin binne gawarwaki, inda aka fara da nemo su daga dazuka.
Dauda, wani jami'i a yankin, ya ce ya raka sojoji tare da taimakawa wajen binne gomman mutanen da suka mutu.
''Ina cikin mutanen da suka birne gawarwaki 30, '' in ji shi. '' Ba mu taɓa fuskantar irin wanna bala'i ba a ƙaramar hukumar Kaiama.
Mazauna garin sun ce mutanen da aka sa haƙa kaburburan sun shafe kwana guda suna aiki, har suka gaji suka kasa aiki.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda ya ziyarci yankin a ranar Laraba da dare, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince a aika bataliyar soji yankin.
Usman na ganin maharan sun fito ne daga dazukan da ke kusa da gandun dajin Kainji Lake, inda ƴan bindigar ke ayyukansu.
Ya ce sojoji sun yi aiki a dazukan da ke kusa da ƙauyukan watannin da suka wuce domin tarwatsa ƴan bindigar.
Ƙauyuka da dama a Kwara na fuskantar barazanar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, waɗada ke yin sata, da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, kuma a baya-bayan nan ne suka soma shiga jihar.
Hakan ya sa alummomi da dama suka kafa ƙungiyoyin sa kai da ke kare ƙauyyukan.
A cewar ɗan majalisar yankin, mayaƙan sun yi ƙoƙarin kai hari ƙauyen a shakarar da ta gabata, amma ƴan sa kai suka fattatake su.
Wani abu da ya girgiza mazauna Woro da Nuku shi ne mayaƙan sun san gidajen ƴan sa-kan, inda suka je kai tsaye suka kwashe su jim kaɗan bayan sun ƙona gidan basaraken ƙauyen.
''Sun ƙona su ƙurmus... kusan su takwas.''