Harry Kane zai koma Barcelona, Casemiro ya yi farin jini

Lokacin karatu: Minti 2

Watakila Wolves za ta rasa dan wasanta Mateus Mane a wannan bazarar, inda Liverpool, Manchester United da Arsenal ke sha'awar ɗan wasan na Ingila mai shekaru 18. (Caughtoffside)

Everton ta sanya ɗan wasan gaban Chelsea Liam Delap a cikin jerin manyan 'yan wasan da za ta nema a lokacin bazara. Ɗan wasan Ingilan mai shekaru 23 ya isa Stamford Bridge ne a lokacin bazarar da ta gabata daga Ipswich Town. (Football Insider)

Yayin da yake shirin barin Manchester United a ƙarshen kakar wasa, ɗan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekaru 33, n ajan hankalin Inter Miami, da Porto da Sao Paulo. (Sun)

A halin yanzu, damar da Aston Villa ke da ita ta riƙe ɗan wasan gaban Ingila Morgan Rogers, mai shekaru 23, ta dogara ne ga taka ledarsa a gasar Premier. Sau hudu kacal dan wasan mai shekara 22 ya buga wasa a wannan kakar baki daya. (Football Insider)

Lennart Karl zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Bayern Munich idan ya cika shekaru 18 a wannan Lahadi, wanda hakan zai kawo karshen fatan daukar ɗan wasan na Jamus da Liverpool, da Arsenal, da Manchester City, da Real Madrid da Paris St-Germain ke yi. (Teamtalk)

Xavier Vilajoana ya fara tuntuba kai yiwuwar daukar ɗan wasan gaban Bayern Munich da Ingila Harry Kane, mai shekaru 32, idan ya lashe zaɓen shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a watan gobe. (ESPN)

Ɗan wasan Argentina Tadeo Allende, mai shekaru 27, ya ƙuduri niyar zama ɗan wasan Inter Miami, bayan ya kafa kansa tare da 'yan wasan gaba na ƙasarsa Lionel Messi, mai shekaru 38, da Luis Suárez, mai shekaru 39, da kuma ɗan wasan tsakiya Rodrigo de Paul, mai shekaru 31. (Goal.com)