Man Utd na son Mac Allister, An yi wa Arsenal tayin Nico Williams

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na tunanin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister, mai shekara 27 daga Liverpool yayin da ɗanwasan ke son barin Anfield a bazara. (Star)

Manchester City ta fi son ta bayar da aron golanta James Trafford maimakon sayar da shi a bazara yayin da Leeds da Aston Villa da Newcastle ke ribibin ɗanwasan mai shekara 23. (Teamtalk)

Ana sa ran Nicolas Jackson na Senegal, mai shekara 24, zai koma Chelsea a bazara saboda yadda ba ya taka leda a Bayern Munich. (Times - subscription required)

An shaida wa Arsenal cewa ɗanwasan gaba na Spain Nico Williams, mai shekara 23, zai iya barin Athletic Bilbao a bazara. (Teamtalk)

Brighton na son ɗauko matashin ɗanwasa Said el Mala, mai shekara 19 daga Cologne ta Jamus. (Sky Germany)

Manchester United ta musanta tuntuɓar wakilin Jurgen Klopp bayan ya ce ƙungiyar ta tuntuɓe shi game da tsohon kocin Liverpool domin zuwa Old Trafford. (Sky Sports)

Real Madrid za ta ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekara 26 daga Borussia Dortmund a wannan bazara yayin da Barcelona ke farautarsa. (Fichajes in Spanish)

Manchester United na ci gaba da sa ido kan ɗanwasan Middlesbrough Hayden Hackney, 23, yayin da za ta shiga hamayya da Leeds da Tottenham da Everton da ke son ɗawasan tsakiyar na Ingila. (Teamtalk)

Galatasaray na son ɗauko ɗanwasan Inter Milan da Turkiya Hakan Calhanoglu, mai shekara 32. (La Gazzetta dello Sport in Italian)

Kocin Barcelona Hansi Flick na son ƙara ƙarfin bayansa ta hanyar ɗauko ɗanwasan baya na Borussia Dortmund da Norway Julian Ryerson, mai shekara 28. (Fichajes in Spanish)