Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG na son Haaland, Barca da Atletico na hamayya kan Bernardo Silva
Paris St‑Germain ta tuntuɓi Manchester City kan ɗanwasan gaba na Norway Erling Haaland, kodayake an fi alaƙanta ɗanwasan mai shekara 25 da komawa Spain idan har ya zaɓi tafiya. (Teamtalk)
Aston Villa na don ɗauko ɗanwasan tsakiya na Wales Harry Wilson daga Fulham a wannan bazara, haka ma Everton na farautar ɗanwasan mai shekara 28. (Telegraph - subscription required)
Ɗanwasan baya na Argentina Cristian Romero da ɗanwasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, mai shekara 26, na cikin ƴanwasan da za su bar Tottenham a wannan bazara. (Athletic - subscription required)
Barcelona da Atletico Madrid na son ɗanwasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva, wanda yarjejeniyarsa a Manchester City ta kawo ƙarshe, haka ma Juventus da Monaco na farautar ɗanwasan mai shekara 31. (Teamtalk)
Carlo Ancelotti na son tsawaita yarjejeniyarsa ta shekara huɗu a matsayin kocin Brazil. (Movistar via AS - in Spanish)
Ɗanwasan Faransa da ya fi yawan ci wa kasar ƙwallo a raga Olivier Giroud, mai shekara 39, na fuskantar ƙalubale kan makomarsa a Lille inda ɗanwasan na gaba tauraronsa ke ƙara dusashewa. (L'Equipe - in French - subscription required)
Ɗanwasan gaba na Newcastle da Ingila Anthony Gordon, mai shekara 24, ya ce ba zai bari rade-raɗin da ake kan makomarsa ba ta ɗauke masa hankali yayin da ake alaƙanta shi da Liverpool da Arsenal. (Sun)
Golan Manchester City ɗan ƙasar Ingila James Trafford, mai shekara 23, ya fi son komawa Aston Villa maimakon Newcastle United a wannan bazara. (Football Insider)
Barcelona ta ƙarfafa tsarin darajar matasan ƴanwasanta bayan Paris St-Germain ta saye matashin ɗanwasan Spain mai shekara 18 Dro Fernandez kan fam miliyan 7. (RMC Sport - in French)
LA Galaxy na sa ido kan ɗanwasan Brazil Philippe Coutinho mai shekara 33 bayan Vasco da Gama ta amince ta kawo ƙarshen yarjejeniya da shi. (AS - in Spanish)