Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ya fi dacewa a fara buɗe-baki da dabino?
- Marubuci, Kate Bowie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global health
- Lokacin karatu: Minti 3
Miliyoyin musulmai ne a duniya suke azumi, inda kusan dukansu suke aiwatar da abu iri ɗaya da zarar rana ta faɗi - wato buɗe-baki.
A wannan watan na Ramadan, wanda wata ne na azumi da addu'o'i, Musulmai masu lafiya waɗanda suka cika sharuɗɗan azumi suna guje wa cin abinci da abin sha daga huɗuwar alfijir zuwa faɗuwar rana, wanda yana ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar.
Ana shawartar masu azumi su fara buɗe-baki da dabino, kamar yadda Annabi Muhammad ya buƙata, kuma an samu muhimmancin dabinon daga nassin Qur'ani da Hadisi.
Sai dai baya ga cin dabinon a matsayin bin tafarki da shawarar Annabin, akwai kuma wasu muhimmanci da hakan ke da shi ga lafiya.
Sinadarai masu gina jiki
Dabino na ɗauke da muhimman sinadarai masu gina jiki, wanda hakan ya sa ya zama abin buɗe-baki mai inganci bayan tsawon lokaci ba a ci komai ba.
"Da zarar ka yi buɗe-baki, jikinka zai fara neman sinadaran ƙarfafa jiki," in ji Shehnaz Bashir, wata ƙwararriyar ɓangaren abinci a Birtaniya da take azumin Ramadan.
Yanayin sukarin da dabinon ke da shi ne zai taimaka wajen daidaita sukarin jininka sama da abinci saboda abinci na daɗewa kafin ya narke.
Wannan ya sa dabinon ke fitar da sinadaran gina jiki cikin sauri, sannan jikin ya ƙara kuzari. Haka kuma akwai sinadaran B6 da A da K da iron a cikin dabino, wanda hakan ya sa jiki ke samun sinadarai masu gina jiki cikin ƙanƙanin lokaci.
Rage ƙishin ruwa
Duk da cewa yawanci dabino busasshe aka fi ci, amma ƴaƴan itacen na rage ƙishin ruwa.
Dabino na ɗauke da sinadarai masu daidaita ruwan jikin mutum kamar potassium.
"Mutane da dama suna fara buɗe-baki ne da dabino da ruwa, wanda abu ne mai kyau," in ji Bashir.
Rage cin abinci da yawa
Wasu na rage ƙiba a Ramadan, amma a wani ɓangaren kuma, azumi na sa wasu su ƙara ƙiba musamman idan mutum na cin abinci mai yawan gaske ko wanda ya wuce ƙima bayan buɗe-baki.
An fi so a ci dabino adadin mara a lokacin fara buɗa-baki, sai a yi sallar Magariba, kafin a sake cin abinci mai nauyi.
Da zarar jiki ya fara narka abinci, musamman mai ɗauke da sinadaran dusa, jikin na rage buƙatar cin abinci mai yawa.
"Jikin zai fahimci cewa ya riga ya samu abinci, saboda ya fara aikin narka abinci," in ji ƙwararriyar.
Narka abinci
Shaƙewa na cikin abubuwan da masu azumi suke fuskanta, saboda jiki na fuskantar sauye-sauye daga yanayin da ya saba na cin abinci da safe da kuma rana.
Dabino na ɗauke da sinadaran dusa, wanda ke sauƙaƙawa wajen yin bayan-gida.
Hukumar lafiya ta Birtaniya ta shawarci mutane su ci giram 30 na dusa a kullum.
"A lokacin azumin Ramadan, za a iya wayan gari da kwaɗayi, amma duk da haka idan mutum ya tsara yanayin cimakansa, zai samu haɗa cimakansa da kyau yadda zai samu isasshen sinadarin dusa da yake buƙata," in ji ta.
Me zai faru idan ban ci dabino ba?
Bayan watan Ramadan, yin azumi lokaci bayan lokaci na da kyau, ko ba komai, yana inganta lafiya.
Idan ba ka son dabino, akwai ɗaruruwan abubuwan da mutum zai iya ci a madadin dabino.
"Akwai nau'uka da dama, wasu ma na maƙulashe ne. Don haka sai mutum ya zaɓa wanda zai iya ci," in ji ta.
Idan kuma mutum ba zai iya cin guda ɗaya ba, sai a haɗa da dama a niƙe su a waje ɗaya.
"Za a iya haɗa dabino da madara da gyaɗa a niƙe a waje ɗaya a sha. Wannan ma zai kasance yana da sinadarai masu gina jiki sosai."