Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wani ƙauyen Rasha ya rasa ɗaukacin mutanensa a yaƙin Ukraine
- Marubuci, Olga Ivshina
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian
- Lokacin karatu: Minti 4
Rayuwa ta yi wuya a ƙauyen Sedanka da aka fi sani da masu kamun kifi, da ke gabashin Rasha.
Dukkan gidaje na fama da matsalar ababen more rayuwa irinsu rashin ruwa, wuraren bahaya da kuma wurin jin ɗumi duk da ƙaruwar yananyi ko kuma sanyi a lokacin hunturu.
Ana iya kai wa ƙauyen ne kaɗai daga watan Mayu zuwa Oktoba mai cike da dazuka da itatuwa ta hanyar amfani da kwale-kwale ko kuma manyan ababen hawa. A lokacin sanyi kuma sai da jirage masu saukar ungulu ko kuma ababen hawa masu jure sanyi ko ƙankara.
Babu wadatattun ayyuka a ƙauyen kuma yawancin mutane na rayuwa ne ta hanyar kamun kifi da kuma noman abin da za su ci.
Sai dai ƙauyen Sedanka na fama da wata matsala a baya bayan-nan.
Kusan ɗaukacin maza ƴan shekara 18 zuwa 55 sun bar ƙauyen, a cewar mazauna garin, inda suka shiga yaƙin da Rasha take yi a Ukraine.
'Babu wanda zai sare mana itatuwa'
"Abin tashin hankali ne - an kashe mutanen mu da dama," a cewar Natalia wata ƴar ƙauyen da aka sauya sunanta saboda dalilai na tsaro, yayin wata tattaunawa da BBC.
"Mijinta yayata da ƴan uwana suna fagen daga.
"A kowane iyali, akwai wanda ya tafi yin faɗa."
Ƙauyen wanda ke kusa da tekun Okhotsk yana da nisan kilomita 7,000 da Ukraine.
Maza 39 daga ƙauyen sun saka hannu kan kwangilar yi wa Rasha yaƙi a Ukraine - al'ummar ƙauyen ba su fi mutum 258 ba.
An kashe mutumn 12 cikinsu sannan wasu bakwai sun ɓata.
"Dukkan mazan ƙauyen mu sun tafi yin faɗa," kamar yadda wasu mata suka faɗa wa gwamnan yankin lokacin da ya kai ziyara a watan Maris ɗin 2024.
"Babu wanda zai sare mana itatuwa don hura wuta lokacin sanyi," kamar yadda matan suka faɗa.
BBC tare da taimakon kafar yaɗa labaran Rasha Medizona da kuma masu bincike, sun gano cewa zuwa yanzu an kashe sojojin Rasha 40,201 a 2025.
A cewar bayanai da muka tattara, sun kiyasta cewa ɗaukacin alkaluman sojojin da aka kashe a 2025 zai kai 80,000, wanda zai kasance asara mafi girma da Rasha ta samu a Ukraine tun bayan kaddamar da mamaya ranar 24 ga Fabrairun 2022.
Alkaluman sun kunshi waɗanda aka rubuta cewa sun mutu a 2025 ko kuma a shekarar aka binne su, sai dai mu ƙara yin dubi ga batun ba.
An tabbatar da cewa waɗanda suka mutu a 2024 yanzu sun kai 69,362 - idan aka kwatanta da ɗaukacin waɗanda suka mutu a 2022 da kuma 2023.
Mun tabbatar da mace-macen ta hanyar amfani da rahotannin hukumomi da kuma bayanai da aka tattara - wanda ake ɗauka bayan mutum ya mutu - da kuma labaran gidajen jaridu, sakonnin kafafen sada zumunta daga ƴan uwa ko abokan waɗanda suka rasu da kuma bayanai daga makabartu.
Gabaki ɗaya, BBC ta gano cewa an kashe sojojin Rasha 186,102 a yaƙin Ukraine.
Sai dai, alkaluman mace-macen zai iya fin haka, saboda ba a ɗaukar bayanan yawancin waɗanda suka mutu a fagen daga.
Ƙwararru kan harkar soji sun ce bayanan mu suna wakiltar kashi 45-65 na ɗaukacin waɗanda aka kashe a Ukraine tsakanin mutum 286,000 zuwa 413,500.
Ita ma Ukraine ta samu asara da yawa.
A watan da ya gabata, shugaba Volodymyr Zelensky ya faɗa kafar yaɗa labarai ta France 2 cewa an kashe ƴan Ukraine 55,000 a fagen yaƙi a "hukumance".
Ƙari kuma shi ne an ruwaito cewa "ɗaruruwan mutane" sun ɓata, in ji shi, duk da cewa bai fi ainihin alkaluman ba.
Bisa ga kiyasi daga majiyoyi waɗanda BBC ta ƙara bin diddigi, mun kiyasta cewa ƴan Ukraine da aka kashe za su iya kai wa 200,000.
Ɗaya daga cikin mazan ƙauyen Sedanka da ya shiga yaƙi a Ukraine shi ne Vladimir Akeev mai shekara 45, wanda ya kasance mai farauta da kamun kifi - ya saka hannu kan kwangilar yi wa Rasha faɗa a 2024.
Sai dai bayan watanni huɗu, ya gamu da ajalinsa.
Masu makokinsa sun samu damar zuwa makabartar da aka binne shi ne kaɗai ta hanyar amfani da ababen hawa masu jure sanyi.
BBC ta gano cewa kashi 67 na waɗanda suka mutun sun fito ne daga ƙauyuka da kuma ƙananan garuruwa - waɗanda ke da al'ummomi kasa da 100,000 - duk da cewa kashi 48 na al'ummar Rasha na rayuwa a can.
Mutane kaɗan ne suka mutu daga cikin birane, inda Moscow ke da alkaluma mafi ƙankanta - inda ake samun mutuwar mutum biyar cikin maza 10,000 da aka kashe, ko kuma kashi 0.05.
A yankunan matalauta irinsu Buryatia da ke gabashin Siberia da kuma Tuva a kudancin Siberia, alkaluman waɗanda suka mutu na tsakanin 27 zuwa 33.
An kaddamar da wani mutum-mutumi a ƙauyen Sedanka a 2024 domin sadaukarwa ga waɗanda suka shiga yaƙi.
A bara, gwamnatin yankin ta sha alwashin ba da wata girmamawa ga ƙauyen saboda yadda mazan ta suka shiga yaƙi.
Ta kuma yi alkawarin ɓullo da wani shiri don taimakawa iyalan sojojin ƙauyen.
Sai dai har yanzu ƙauyen bai samu lambar girmamawar ba sannan babu wani tallafi da ya isa ga iyalai.
An gyara kwanon gidajen huɗu daga cikin sojojin, amma sai da aka yi ta yayata batun a kafafen yaɗa labaru.
An bayyana cewa ɗaya daga cikin gidaje biyar a Sedanka, wanda aka gina a zamanin tarayyar Soviet, na cikin matsala.
Jami'ai sun ce makaranta ɗaya tilo da ƙauyen ke da shi yana cikin babbar barazana, inda wasu bangonsa ke cikin barazanar rugujewa.
Duka wannan na zuwa ne a lokacin da ƙauyen ya yi asarar mutane masu jini a jika a yaƙin Ukraine.