Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ruwan sanyi ko na ɗumi: Wanne ya fi dacewa wajen buɗe baki?
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 2
Buɗe-baki dai wani abu ne da al'ummar Musulmi ke yi a cikin watan Ramadan, inda ake saka abu a baki bayan kamewa daga sha ko cin abu daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Sai dai kuma, saboda tsarin halittar jikin ɗan'adam ba a fiya son mutum ya ɗauki tsawon lokaci kamar haka ba tare da shan ruwa ba, sai dai idan da dalili kamar na ibadar azumi.
Ana cin abubuwa da dama ko kuma na'ukan abinci a lokacin buɗe-baki domin jiki ya yi ƙwari da kuma kuzari.
Sai dai, wasu na fara wa ne da shan ruwa mai sanyi da zarar an ƙarya azumi.
Amma me ya kamata a fara yi lokacin buɗe baki, ruwan sanyi ko kuma mai ɗumi?
Kan haka ne muka tuntuɓi wani likita domin jin abin da ya fi dacewa a yi.
Ruwa mai ɗumi ya fi amfani
Dakta Hassan Ibrahim likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya ce abin da ya fi dacewa mai buɗe-baki ya yi shi ne shan ruwa mai zafi ko ɗumi-ɗumi.
Ya ce bai dace wanda ya ɗauki tsawon lokaci bai ci komai ba ya fara da ruwan sanyi kaɗai.
"Gara abu mai ɗumi-ɗumi shi ya kamata a buɗe-baki da shi, daga baya kuma za a iya shan ruwan sanyi. Ba a son ruwan sanyi ƙarara ya yi yawa saboda zai iya dakusar da wurin ƙishirwa," in ji Dr Biba.
Adadin ruwan da ya kamata a sha
Dakta Hassan Biba ya ce babu wani ma'auni na lita da ya kamata a sha na ruwa.
Ya ce jiki yana da abun da yake gejin kishirwan mu da yake sa mu sha ruwa.
"Wanda ya zo buɗe-baki bayan yin azumi zai zo a bushe don haka ake so ya sha ruwa mai ɗumi ko na sanyi kaɗan ba wai har lita ba. A hankali zai rika shan ruwan har ya ji ya wadata. Kada kuma a sha ruwa mai yawa don zai iya kulle wa mutum ciki," in ji likitan.
Ya ƙara da cewa ruwan da kowane mutum yake buƙata yana bambanta bayan yin azumi.
"Ana son mutum ya riƙa shan ruwa akai akai ko dare ne idan ya farka ya sha ruwa.
Wane lahani shan ruwan sanyi zai yi?
Likitan ya ƙara da cewa akwai yanayin da ruwan sanyin zai dakusar da wurin da yake jin ƙishirwa a jikin ɗan'adam.
"Za ka ji ka wadata idan kana shan ruwan sanyi. Hakan zai sa mai buɗe-baki ba zai samu wadataccen ruwa ba a jikinsa saboda baya shan isasshe.
Lamarin zai sa mutum ya ji nan da nan ya ƙoshi, wanda kuma hakan ba daidai bane ga lafiyarsa.