Muhimmancin shan ruwa ga lafiyar mai azumi

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Akasari, babbar matsalar da mai azumi ya fi fama da ita ita ce ƙishirwa, musamman a ƙasashen yammacin Afirka da yankunan Larabawa, inda ake samun zafin rana.

Yayin azumin watan Ramadana, mabiya addinin Musulunci kan shafe tsawon wuni ba tare da ci ko shan wani abu ba - tun kafin fitowar rana har zuwa faɗuwarta.

Sai dai kuma, saboda tsarin halittar jikin ɗan'adam ba a fiya son mutum ya ɗauki tsawon lokaci kamar haka ba tare da shan ruwa ba, sai dai idan da dalili kamar na ibadar azumi.

Yayin da a wasu ƙasashe kamar Chile da Australia ake yin azumin awa 10 zuwa 11, akwai kuma ƙasashe kamar Denmark da Rasha masu azumin awa 20 zuwa 22.

Alamu na nuna cewa ƙasashe kamar Najeriya, da Nijar za su gudanar da azumin bana cikin zafi, ganin yadda damuna ke ɗan yin jinkiri kafin ta kankama.

Wannan yanayi ya sa ƙwararru ke shawartar masu azumin da su kula da yanayin ruwan jikinsu a lokacin azumi domin gudanar da ibadar ba tare da galabaita ba.

Ruwan da ya kamata mutum ya sha a kullum

"Mafi yawan ruwan da mutum ya kamata ya sha a wurin da ya fi ko'ina zafi a duniya kamar tsakiyar Sahara shi ne lita biyu cikin awa ɗaya, amma fa hakan abu ne mai wuya," a cewar Hugh Montgomary, shugaban cibiyar bincike ta Institute for Sport, Exercise and Health da ke birnin Landan.

Abin da ya kamata a sani shi ne, kashi 60 na jikin ɗan'adam namiji ruwa ne, kashi 55 na mata ruwa ne, sannan kashi 70 zuwa 75 na jikin yara ƙanana duka ruwa ne, in ji Dr. Salihu Ibrahim Kwaifa, wani ƙwararren likita a birnin Abuja.

"Shi ya sa rashin ruwa a jikin ƙananan yara yake yin ta'adi da yawa," a cewar likitan.

Ya ƙara da cewa a kowace rana, ɗan'adam na zubar da ruwa kusan lita biyu da rabi ta hanyar fitsari, bahaya, da hawaye, da majina, da gumi, da tsananin zafi.

"Shi ya sa aka ce mazauna ƙasashen da ke da sanyi su dinga shan ruwa lita uku a kullum. Waɗanda ke ƙasashen masu zafi kuma su sha uku da rabi ko sama da haka."

Hukumar inshorar lafiya ta Birtaniya na bai wa mutane shawarar cewa su dinga shan ruwa isasshe da zai sa fitsarinsu ya yi haske tas.

Wani jerin shawarwari na abincin da ya kamata mutum ya ci a kullum da ta wallafa a shafinta ya ce ya kamata mutum ya sha ruwa ko wani abin sha kofi shida zuwa takwas a kullum.

Ta ƙara da cewa daga cikin abubuwan da suka kamata a sha akwai ruwa, da madarar da ba ta saka ƙiba, da lemuka marasa sikari, ciki har da shayi da gahawa (ko coffee).

Mutanen da suka kamata su sha dinga shan ruwa da yawa su ne:

  • Mai ciki ko kuma mai shayarwa
  • Wanda ke zaune a wuri mai zafi
  • Maras lafiya ko kuma mai jinya

Yaya mai azumi ya kamata ya yi kenan?

Ƙwararru na cewa shi ma mai azumi ba a cire shi daga yawan ruwan da wanda ba shi azumi ya kamata ya sha ba.

Dr. Kwaifa ya ce shi ma mai azumin zai sha ruwa lita uku ko fiye daga lokacin buɗe-baki zuwa lokacin sahur.

Amma ganin cewa tsakanin shan ruwa da sahur babu awanni masu yawa, ta yaya mutum zai iya shan ruwa lita uku kuma har ya samu wurin zuba abinci a cikinsa?

"Ana nufin duk abin da yake ɗauke da ruwa ne. Misali, kunu, da koko, da kunun zaƙi, da lemon zaƙi. Mai azumi zai lissafa da duka waɗannan a cikin yawan ruwan da zai sha," kamar yadda Dr. Kwaifa ya yi bayani.

Yayin da jiki ya fara sabawa da azumi, yana narkar da kitse ya mayar da shi sikari a cikin jini.

Kazalika, saboda rage shan abubuwa masu ruwa-ruwa a lokacin azumi, ya kamata a maye gurbinsu daga buɗe-baki zuwa lokacin ɗaukar wani azumin, idan ba haka ba za a iya samun matsalar ƙarancin ruwa a jiki.

Dabarun shan ruwan da ya kamata

Masu azumi da sauran mutane kan yi ƙorafin cewa shan ruwa da yawa na ƙulle musu ciki, ko kuma ya cika cikin ta yadda za a rasa wurin zuba sauran abubuwa.

Sai dai babu mamaki rashin sanin yadda ya kamata a sha ruwan ne ke jefa su cikin matsala.

Yana da kyau mai azumi ya tsara shan ruwansa daga buɗe-baki zuwa sahur. Misali, akasari yawan ruwan ledar fiyawata kan zarta 50CL. idan mutum ya buɗe baki da guda ɗaya, sannan ya ƙara ɗaya bayan sallar Isha ya sha lita ɗaya kenan.

Idan ya yi ƙoƙari zai iya ƙara biyu daga Isha zuwa lokacin kwanciya barci, wanda zai zama lita biyu kenan. Sannan ya ƙara biyu a taksanin kafin da kuma bayan yin sahur.

Ko da mutum ba shi shan ruwan fiyawata, zai iya samun wani kofi ya juye ruwan ledar a ciki domin auna yawansa, sai ya mayar da kofin a matsayin ma'auni.

Kwararriya kan harkokin abinci Bridget Belam ta ce yana da kyau a ci abinci mai nauyi lokacin sahur, kamar tsaba, tana mai cewa saboda a hankali suke narkewa ta yadda za su dinga bai wa mutum kwarin jiki a duka yinin.

Sai dai ta jaddada cewa: "Yana da kyau a sha ruwa isasshe, hakan zai sa a duka yinin mutum ba zai ji ƙishirwa ba sosai."

Belam ta nuna a kiyayi sahur da abubuwa masu gishiri.

"Abinci mai gishiri yana jawo ƙishirwa, kuma kamata ya yi sai an rasa wani abu za a ci abu mai gishiri. Doguwar rana ce da mutum zai daɗe yana jin ƙishi a cikinta."