Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne ke faruwa da jikinmu idan muna azumi?
A duk shekara miliyoyin musulmai na yin azumi daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana a tsawon kwana 30 na watan Ramalana.
A shekarun baya-bayan nan azumin na faɗowa ne a lokacin zafi a ɓangaren arewacin duniya.
A wannan shekarar azumin ya faɗo ne a lokacin da za a samu ruwan sama, inda aka ga jaririn watan a ranar 11 ga watan Maris.
Abin da ke nufin a wasu ƙasashen ranaku ba su da tsawo, kuma tsawon sa'oin yin azumin su kan kai 12 zuwa 17, kuma hakan ya danganta da inda mutum yake a duniya.
To ko hakan na da kyakkyawan tasiri ga lafiya? Ga abin da ke faruwa ga jiki idan ka yi azumi na tsawon kwanaki 30.
Mafi wahala - su ne ƴan kwanakin farko
Jikinka farat ɗaya baya shiga yanayi na azumi, sai bayan sa'oi takwas ko kusan hakan bayan abincin da ka ci na ƙarshe.
A wannan lokaci ne kayan cikinka ke kammala tsotse duka sinadaren da ke cikin abinci.
Da zarar hakan ya faru, sai jiki ya juya kan sukarin da ke adane a cikin huhu da kuma naman jiki domin samun kuzari.
Can ana ci gaba da azumin, idan sukarin ya ƙare sai jiki ya koma amfani da kitse domin samun kuzari.
Idan jiki ya fara ƙona kitse to hakan yana da kyau wajen rage ƙiba, da rage sinadaran cholesterol da kuma rage ciwon suga.
Amma raguwar da ake samu na sukarin da ke cikin jini na janyo rauni da rashin karsashi.
Mutum zai iya samun ciwon kai, jiri, tashin zuciya da warin baki.
Kuma a wannan lokacin ne kuma yunwa ta fi tsanani.
A kiyaye ƙarancin ruwa a jiki - kwana na 3-7
Yayin da jiki ya fara sabawa da azumi, yana narkar da kitse ya mayar da shi sukarin cikin jini.
Rage shan abubuwa masu ruwa-ruwa a lokacin yin azumi, ya kamata a maye gurbinsu idan an yi buɗabaki zuwa lokacin ɗaukar wani azumin, idan ba haka ba za ka iya samun matsalar ƙarancin ruwa a jiki.
Abincin da za a ci kuma yakamata ya ƙunshi sinadaran da suka dace, kamar mai ƙara kuzari da kuma ɗan maiƙo.
Yana da muhimmanci a ci abinci mai gina jiki mai kunshe da sinadaren da suka haɗa da sinadarin gina jiki da gishiri da kuma ruwa.
An fara sabo da shi - kwana na 8-15
A mataki na uku, za a ga abubuwa sun inganta saboda jiki ya saba sosai da yin azumin.
Dokta Razeen Mahroof, wani ƙwararren likita a asibitin Addenbrooke da ke Cambridge a Ingila ya ce akwai wasu tasirin.
"A rayuwarmu ta yau da kullum mun saba da cin sinadarin Calories, kuma wannan sinadari na hana jiki yin wasu ayyukansa da ya kamata, kamar gyaran kansa."
Ana samun gyaran idan ana azumi, jiki na samun damar yin wasu ayyukan na daban.
Don haka azumi na amfanar jiki wajen bashi sararin gyaran kansa da kuma kariya da yaƙi da cututtukan da ƙwayoyin cuta ke haifarwa."
Cire abubuwa marasa kyau daga jiki - kwana na 16 zuwa 30
A lokacin da watan Ramalana ya kai rabi, jiki ya riga ya saba sosai da azumin.
Hanji, huhu, ƙoda da fatar jiki za su shiga yanayi na share abubuwa marasa kyau daga cikinsu a wannan lokaci.
"Ta ɓangaren kiwon lafiya, gaɓoɓi za su koma cikakken aikinsu.
Tunani da mayar da hankali kan abu, na iya inganta, kuma za ka samu ƙarin kuzari," In ji Dokta Mahroof.
"Bai kamata jikinka ya koma kan sinadaren da ke gina jiki ba domin samun kuzari . Don a wannan yanayin ne ka ke shiga 'yanayin matsananciyar yunwa' kuma ya iya yin amfani da naman jiki domin samun kuzari. Hakan na faruwa idan aka ɗauki tsawon lokaci ana azumi na kwanaki da makonni."
"Da yake azumin watan Ramalana ana yinsa ne daga fitar alfijir zuwa faduwar rana, kana da isasshen lokacin da zaka iya maye gurbin abubuwan da jiki ke ɓuƙata na abinci mai gina jiki da kuma ruwa. Wannan yana kare naman jiki, yana kuma taimakawa wajen rage ƙiba.
Ko azumi na da kyau ga lafiyarmu?
Dokta Mahroof ya ce ƙwarai kuwa, amma akwai sharaɗi.
"Azumi na da kyau ga lafiyarmu saboda yana sa mu mayar da hankali kan me yakamata mu ci da lokacin da ya kamata mu ci abin. Sai dai duk da cewa yin azumi na tsawon wata guda bashi da matsala, ba shawara ba ce mai kyau a ci-gaba da azumi na wani dogon lokaci."
Ya bayar da shawarar cewa bayan Ramalana, yin azumi jefi-jefi ko kuma yin azumi na wasu ƴan kwanaki kana tsallake wasu kuma kana cin abinci mai jina jiki a ranakun da ba ka azumi, wani zaɓi ne mai kyau, maimakon yin azumi na tsawon watanni a jere.
"Azumin watan Ramalana, idan an yi shi yadda ya kamata zai bai wa jiki damar sake maye gurbin abubuwan da ya rasa a kullum, kuma hakan na nufin za a iya rage ƙiba ba tare da jiki ya koma yana amfani da naman jiki ba."