Ana jiran sakamakon zaɓen birnin Abuja

Lokacin karatu: Minti 2

Ana ci gaba da dakon cikakken sakamokon zaɓen yankunan ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a Abuja babban birnin Najeriya, inda aka zaɓi ciyamomi da mataimakansu, da kuma jimillar kansiloli.

Zaɓen ya gudana ciki kwanciyar hankali, amma masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwa kan rashin fitowar mutane yadda ya kamata domin kaɗa ƙuri'a, wani lamari da aka saba gani a zaɓen ƙananan hukumomi a ƙasar.

Hukumar zaɓe ta Najeriya INEC ta sanar da aikewa da sakamakon zaɓe ta na'ura kai tsaye daga runfunan zaɓe, wani abu da aka daɗe ana cece kuce a kai a siyasar Najeriya.

Rahotanni sun ce shafin tura sakamakon zaɓe na hukumar da aka fi sani da IReV ya fara aiki yadda ya kamata, kuma sakamako na shiga daga lokaci zuwa lokaci.

A ranar Laraba shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar zaɓe ta 2026 da aka yi wa gyara, wadda ta samar da sauye-sauye a tsarin gudanar da zaɓe a Najeriya, kuma wannan ne karon farko da jama'ar ƙasar ke fatan ganin yadda gyaran da aka yi wa dokar zai inganta gudanar da zaɓe a kowanne mataki.

A game da ƴan ƙorafe-ƙorafen da aka samu na jinkirin fara zaɓen a wasu wurare da kuma sauran ƙalubale, Zainab Aminu Abubakar, jami'a a sashen yaɗa labarai na hukumar INEC ta ce hukumar dama akwai tanadin da doka ta yi na yadda za a magance dukkan ƙalubalen da aka gano a wannan zaɓe.

Ta ce ''Dama kamar yadda doka ta tsara, duk runfar da aka yi latti wurin bude ta, dama ana ɗan ƙara masu lokaci don gudanar da zaɓen su.''

Jami'ar hukumar zaɓen ta ce dama sun yi tanadi na musamman domin kai daukin gaggawa da kuma shawo kan duk wata matsala da ta taso, lamarin da ya bai wa hukumar nasara a zaɓen na ranar Asabar.

Amma daga ɓangaren jam'iyyun adawa, jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi zargin cewa an samu yanayi na tunzuru jama'a a wasu runfunan zaɓe, inda ta zargi ministan birnin Abuja, Nyesom Wike da jagorantar harzuƙa jama'a.

Jam'iyyar ta ce zagayen da ministan ya riƙa yi a runfunan zaɓe daban-daban na Abuja da sunan sanya ido kan yadda zaɓen ke gudana, wata hanya ce ta tunzura jama'a da tilastawa wasu zaɓen abinda ba su yi niyya ba.

Ana dai kallon zaɓen na babban birnin tarayya Abuja, a matsayin wani zakaran gwajin dafi ga jam'iyyun adawa da tagomashin jam'iyyar APC da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da kuma hoɓɓasar hukumar zaɓen ƙasar wajen gudanar da zaɓe mai inganci ƙarƙashin sabon shugabanta, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a badi.