'Azumin Ramadan babu dabino lami ne'

'Azumin Ramadan babu dabino lami ne'

Hare-haren da ake kai wa jiragen ruwan dakon kaya a tekun Maliya na kawo jinkiri wajen isar kaya zuwa tashar ruwa ta Mombasa da ke Kenya – lamarin da ke haifar da tashin farashin kaya, kamar dabino, wanda ake amfani da shi wajen buɗe-baki a lokacin azumin Ramadana.

Hakan na nufin cewa da yawa daga cikin Musulmin yankin da ke azumi a wannan karo ba za su iya samun damar sayen ƴaƴan itacen ba.