Attajirin da ya fara kasuwanci da jarin naira 20

Attajirin da ya fara kasuwanci da jarin naira 20

Yayin da ɗumbin mutane ke fafutikar yadda za su samu jari domin fara sana'a kuma su raine shi har ya bunƙasa, wani attajirin ɗan kasuwa a Abuja ya ce shi da N20 ya fara.

Alhaji Halliru Buhari ya ce ya kwashe shekaru masu yawa yana ririta jarin nasa kafin ya bunƙasa.

Cikin wata hira da BBC Alhaji Halliru ya ce ya fara kasuwancinsa ne a lokacin mulkin soji na tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo.

''Babban yayanmu ne ya ba ni naira 20 a matsayin jari, kuma wannan jari shi ne har yanzu nake riritawa'', kamar yadda ya shaida wa BBC

Ya ƙara da cewa dama a gidansu ya taso ya tarar ana harkar kasuwancin koli.

''Tun da farko na fara kasuwanci da mahaifina, daga baya na tasho Kaduna cikin gari wajen babban yayanmu inda ya bani jarin'', in ji shi.

Ya ce ya fara ne da yawo cikin gari yana tallan kayan kolin nasa a cikin tire, kafin daga baya ya riƙa zuwa garuruwan da ke gefen Kaduna irin su Zankuwa da sauran yankuna.

'A yanzu jarina ya haura naira miliyan 200'

Attajirin ya ce a baya ya shafe fiye da shekara takwas yana matsayin shugaban kasuwar Wuse da ke Abuja

Alhaji Halliru Buhari - wanda ke harkar ƴankunnen gwal ya ce sirrin kasuwancinsa shi ne ba ya fushi da kwastoma kuma zai faɗa musu gaskiya ko da mutum ba zai sayi hajarsa ba.

Ya ce a yanzu matan gwamnoni da manyan ƴansiyasa ne ke yi masa cikini a shagonsa.

Attajirin ɗan kasuwar ya ce yanzu ƙarfin jarinsa ya haura naira miliyan 200 ban da sauran kadarorinsa.

Ya kuma ce akwai mutum fiye da 100 a ƙarƙashinsa kuma kowanensu na da mahalli.

Daga ƙarshe ya bai wa matasa shawarar riƙe kasuwanci tare da haƙuri da juriya a harkar kasuwanci.