...Daga Bakin Mai Ita tare da Boyskido

...Daga Bakin Mai Ita tare da Boyskido

Wannan makon cikin shirin Daga Bakin Mai Ita mun kawo muka tattaunawa da mawaƙin Najeriya Adeyinka Dare, wanda aka fi sani da Boyskido.

Boyskido, wanda asalin harshensa shi ne Yarbanci kuma ɗan asalin jihar Oyo ne da aka haifa a garin Sokoto ya bayyana yadda ya kwaɗaitu da waƙar Hausa.

"Na fi daukar kaina a matsayin Bahaushe," in ji Adeyinka.