Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai bambanta zaɓen Najeriya mai zuwa da waɗanda suka gabata?
Ƴan Najeriya na sa ran ganin sauye-sauye a hanyoyin gudanar da zaɓukan ƙasar a zaɓen 2027 da ke tafe nan da shekara guda.
Ana sa ran ganin sauye-sauyen ne bayan fara aiki da sabuwar dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyaran fuska.
A makon da ya gabata ne shugaban ƙasar da ya sanya hannun kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026, in da aka samar da manyan gyare-gyare, wadanda za su shafi tsarin gudanar da zaɓukan ƙasar.
Sauye-sauyen na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafen ƴan ƙasar, kan wasu dokokin zaɓen ƙasar da suke ganin ba su dace da yanayin ƙasar ba.
An dai kai ruwa rana a majalisar dokokin ƙasar kafin amincewa da sabbin dokokin, lamarin da ya kai ƙungiyoyin fararen hula shirya zanga-zangar matsin lamba ga majalisar dokokin ƙasar domin amincewa da sakamakon.
An ɓullo da sauye-sauyen masu yawa a tsarin zaɓen ƙasar, kama daga kan fitar da ƴan takara zuwa yakin neman zaɓe da ma tattara sakamako.
Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin akwai sauye-sauye da za a gani a tsarin zabukan kasar masu zuwa.
Sauye-sauyen da za a gani
Dr Kabiru Sa'id Sufi Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan ala'amuran siyasar ƙasar ya ce akwai sauye-sauyen da za a gani a tsarin zaɓukan Najeriya masu zuwa sakamakon gyaye-gyaren dokar zaɓen ƙasar kamar haka:
Tsarin fitar da ƴan takara
Dr Kabiru Sufi ya ce saujyi na farko da za a gani bayan gyara dokar zaɓen shi ne hanyar da jam'iyyu ke bi wajen fitar da ƴan takara.
Sabon gyaran da aka yi wa dokar zaɓen ya cire amfani da wakilai da ake kira dalaget wajen zaɓar mutanen da za su tsaya wa jam'iyya takara a kowace kujera.
Sai dai masanin ya ce wannan sauyi ka iya zuwa da wasu matsalolin, domin kuwa ana iya samun mutanen da za su yanki katin jam'iyya fiye da daya ta yadda za su halarci zaɓukan fitar da gwanayen jam'iyyu daban-daban.
Haka ma akwai fargabar tayar da fitintinu a lokutan zaɓukan fitar da gwanin.
Raguwar shari'u a kotuna
Wani sauyin da za a gani a zaɓukan ƙasar masu zuwa shi ne raguwar kai ƙara zuwa kotuna, kamar yadda Dr Sufi ya yi ƙarin haske.
''Galibi shari'o'in da ake yi ana yin su ne kan batun sakamakon zaɓe, inda a baya ake ƙalubalantar zaɓukan a kotuna idan aka samu gazawar tura sakamako ta na'ura, amma yanzu da aka amince da hanyoyin biyu, zai sa masu ƙorafi su gamsu',' in ji shi.
Shirin INEC a kan lokaci
Sabuwar dokar ta yi tanadin bai wa hukumar zaɓen kuɗaɗen shirya zaɓuka wata shida kafin ranar zaɓen.
A cewar Dr Sufi hakan zai taimaka wa hukumar yin cikakken shirin tunkarar zaɓukan.
''A baya mun riƙa ganin yadda aka riƙa ɗage zaɓuka saboda rashin shiri daga INEC, kasancewa ba a ba ta kuɗaɗenta a kan lokaci ba, to amma yanzu da wannan doka, ba ma tunanin ganin irin waɗannan matsaloli na ɗage zaɓuka,'' in ji shi.
Ƙara kuɗin kamfe
Ƴan siyasa da dama sun jima suna ƙorafin taƙaita musu kuɗin da za su kashe a lokacin yaƙin neman zaɓe, wani abu da ke kange su daga gudanar da muhimman abubuwa a lokutan yaƙin neman zaɓe.
A yanzu sabuwar dokar ta yi tanadin cewa shugaban ƙasa zai iya kashe har naira biliyan 10 saɓanin biliyan 5 da aka amince masa a baya.
Haka ma gwamna zai iya kashe naira biliyan 3 saɓanin biliyan ɗaya da a baya aka amince masa.
Dr Sufi ya ce hakan zai taimaka wa yan siyasar gudanar da ayyuka da dama da suka shafi yaƙin neman zaɓe.
’Yan siyasar kan yi amfani da kuɗin ne wajen ɗaukar nauyin gangamin yaƙin neman zaɓe, kama daga motocin da za a ɗauka da kuɗin man fetur da na abinci ga mahalarta, da sayen wasu muhimman kayayyaki na yaƙin neman zaɓen.
Tilasta amfani da na'ura
Batun tilasta aika sakamakon zaɓe ta na'ura da amfani da na'urar VBAS wajen tantance masu zaɓe sun kasance abubuwan da aka riƙa ce-ce-ku-ce a kansu.
Dr Sufi ya ce maslahar da ƴan majalisa suka ɗauka ta haɗa hanyoyi biyu wajen aika sakamakon zaɓen za ta taimaka musamman wajen rage yawan rigingimun da ake samu tsakanin jam'iyyu musamman kan sakamakon zaɓe.
Sai ya ce kan batun tilasta amfani da na'ura wajen tantance sakamakon zai iya kawo ruɗani saboda galibi na'urorin kan samu matsala a ranakun zaɓukan ta yadda ba sa iya tantance wasu masu zaɓen.
''Sai dai a shawarci INEC ta yi wani shiri na horas da ma'aikatanta na wucin gadi amfani da na'urorin ta yadda za a yi gwajin na'urorin domin gano matsalolin da za a yi samu da su a ranakun zaɓe domin magance su'', in ji shi.
Raguwar matsalar sayen ƙuri'a
Wani sashen na sabuwar dokar zaɓen ya yi tanadin hukuncin tara mai yawa da ma ɗauri ga wanda aka samu da laifin sayen ƙuri'a a lokacin zaɓen.
Matsalar sayen ƙuri'a na daga cikin matsalolin da ake kuka da su a lokutan zaɓukan Najeriya.
Sabuwar dokar ta tanadi ɗaurin aƙalla shekara biyu da zaɓin tarar aƙalla naira miliyan biyar ga wanda aka samu da laifin.
Don haka ne Dr Sufi ya ce wannan zai taimaka wajen samun raguwar matsalar.
''Ai ya ma kamata a wajabta ɗaurin, wanda babu zaɓin tara domin kawar da wannan matsala da ta addabi zaɓukan Najeriya'', in ji masanin siyasar.
Dr Sufi ya ce tanadin hukunin ya yi kaɗan, saboda a cewarsa manyan ƴan siyasa ne ke aiko masu sayen ƙuri'ar, don haka idan aka saka tarar ƙalilan, za su biya domin fitar da mutanen da ka kama.