Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Iran ta ƙi miƙa wuya duk da jibge kayan yaƙin Amurka a Gabas ta Tsakiya?
- Marubuci, Jaroslav Lukiv
- Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Amurka Donald Trump ya kasa gane me ya sa har yanzu Iran ba ta "miƙa wuya" ba duk da ci gaba da jibge dakaru da Amurka ke yi a yankin Gabas ta Tsakiya, in ji jakadan shugaban Amurka na musamman.
Steve Witkoff ya shaida wa kafar talabijin ta Fox News a ranar Asabar cewa Trump na "ƙoƙarin sanin" matsayar Iran, bayan ya yi barazanar ɗaukar ƙwaryaƙwaryan matakin soji idan aka gaza cimma matsaya kan shirin nukiliya na Iran.
Amurka da ƙawayenta na Turai na zargin cewa Iran na ƙoƙarin ƙera makamain nukiliya, abin da ta musanta.
A ƙarshen mako, ɗalibai sun gudanar da zanga-zanga a jami'o'in Iran da dama - karo na farko bayan zanga-zangar da hukumomin ƙasar suka murƙushe a watan Janairu, lamarin da ya haifar da kashe dubban mutane.
A tattaunawarsa a da Fox, Witkoff ya ce: "Ba na son na yi amfani da kalmar 'fusata'... domin shi [Trump] ya san cewa yana da zaɓi daban-daban, amma yana matuƙar son sanin me ya sa suka ƙi... ban son na yi amfani da kalmar 'mika wuya', amma me ya sa ba su miƙa wuya ba.
"Me ya sa duk da wannan matsi, da kayan yaƙi na ruwa da muka tura, me ya sa ba su zo wurinmu sun ce, 'Ba mu son yin fito na fito, ga abin da za mu yi' ba?"
Jakadan na Trump ya ƙara da cewa: "Har yanzu abin ya zama mai wahala a kai su wannan matsayin."
A ranar Lahadi, ministan harkokin waje na Iran Abbas Araghchi ya ce yana ganin cewa har yanzu akwai hanyar warware taƙaddamar ta hanyar diflomasiyya "ba tare da an cuci wani ba". Ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS cewa masu shiga tsakani na tattaunawa kan abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa.
A bayanai daban-daban da suka yi, Araghchi ya ce Iran na shirya wani "daftarin yarjejeniya" kuma za a miƙa shi ga Witkoff a kwanaki kaɗan masu zuwa.
Jami'an Amurka da na Iran sun tattauna kan shirin nukiliya na Iran a wata ganawa a birnin Geneva na Switzerland ranar 17 ga watan Fabarairu. Bayan nan sun ce an samu ci gaba.
Kasar Oman - wadda ta shiga tsakani a tattaunawar - ta sanar cewa za a yi zagaye na gaba na tattaunawa "a Geneva, ranar Alhamis".
Ministan harkokin waje na Oman, Badr Albusaidi ya nuna kyakkyawan fatan ka cewa "za a ƙara ƙaimi wajen ganin an samu ci gaba wajen samar da yarjejeniyar" a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.
Amurka da Iran ba su ce komai ba kan batun.
Duk da rahoton cewa akwai ci gaba a Geneva, a ranar Alhamis Trump ya ce duniya za ta ji "ƙila a nan da kwana 10" ko za a cimma yarjejeniya da Iran ko kuwa Amurka za ta ɗauki matakin soji.
A makonnin baya-bayan nan Amurka na ci gaba da tura kayan yaƙi kusa da Iran da kuma Gabas ta Tsakiya.
Cikin kayan da aka tura har da jirgin yaƙi mafi girma a duniya, wato USS Gerald R Ford, wanda ya kama hanyar zuwa yankin.
An kuma tura jirgin ruwan dakon jiragen yaƙi na Amurka, wato USS Abraham Lincoln, tare da wasu jiragen ruwan yaƙi da kuma na sama.
A cikin Iran, BBC ta tantance bidiyoyin masu zanga-zanga na yin tattaki a jami'ar Sharif University of Technology da ke Tehran, babban birnin ƙasar a ranar Asabar. Daga baya an gan su suna taƙaddama da masu tattakin goyon bayan gwamnati.
Haka nan an bayar da rahoton gudanar da zanga-zangar a wasu jami'o'in na Tehran da ma wasu yankunan ƙasar.
Haka nan kafafen yaɗa labarai a Iran sun bayar da rahoton gudanar da zanga-zanga a jami'o'in University of Science and Technology da jami'ar Khajeh Nasir Toosi University a birnin Tehran, da kuma jami'ar Ferdowsi University of Mashhad a arewa maso gabashin Iran.
A ɗaya daga cikin bidiyon da BBC ta tantance, masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun riƙa ɗaga tuta mai alamar zaki da rana - wanda tambari ne na gwamnatin Iran gabanin juyin-juya-halin Musulunci na 1979 - a jami'ar Sharif University. Za a iya jin masu zanga-zangar na cewa "Javid Shah" ("Allah ja zamanin sarki").
Wani bidiyon da aka tantance ya nuna masu tattakin goyon bayan gwamnati na gangami a jami'ar ta Sharif University of Technology, inda suke ƙona tutocin Amurka da na Isra'ila.
Haka nan an ga yadda aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar adawa da kuma masu tattakin nuna goyon bayan gwamnati a jami'ar Amirkabir University of Technology.
Dalibai daga jami’o’i da dama ne suke yin gangami domin karrama wadanda aka kashe a watan da ya gabata.
Kafar dillancin labarai mai rajin kare hakkin bil’adama (Hrana) ta ce ta tabbatar da kisan akalla mutum 7,015 lokacin zanga-zangar, cikin su akwai masu zanga-zanga 6,508 da yara 226 da kuma mutane 214 masu alaka da gwamnati.
Lokaci na karshe da aka tantance akaliman shi ne ranar 15 ga watan Fabarairu.
Kamfanin yada labarai na Hrana ya ce yana bincike kan rahoton mutuwar karin mutum 11,744.
Hukumomin Iran a karshen watan da ya gabata sun ce sama da mutum 3,100 ne aka kashe - amma ta ce akasarin wadanda aka kashe jami’an tsaro ne da kuma mutanen da “masu zanga-zanga” suka far mawa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi bayan masu zanga-zanga a baya - inda a wani lokaci ya rika karfafa musu gwiwa ta hanyar alkawarin cewa “taimako na nan tafe”.