Lauyoyin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun ce har yanzu ba su samu wata amsa daga Hukumar yaƘi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ba kan buƙatar belinsa da suka gabatar, duk da cewa wa’adin awanni 48 na tsare mutum ba tare da tuhuma ba ya cika.
Mai taimaka wa El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan a shafinsa na X cewa
Sanawar ta ce "lauyoyin sun bayyana cewa har yanzu ba a nuna musu wata takardar umarnin kotu da ta ba da izinin ci gaba da tsare shi ba.
A cewarsu in ji sanarwar, wannan na zuwa ne bayan an miƙa shi daga hannun hukumar EFCC zuwa ICPC a daren 18 ga Fabrairu, bayan ya kai kansa ofishin EFCC da safiyar 16 ga watan domin amsa gayyatar da suka yi masa..
A makon nan ne kuma ake sa ran kotu za ta saurari wasu ƙararraki biyu da suka shafi lamarin.
Ɗaya daga cikinsu ita ce karar take hakkinsa na dan Adam da ya shigar kan Gwamnatin Tarayya da hukumomin bincike ciki har da hukumar ICPC, wadda za a saurara a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja ranar 25 ga Fabrairu.
A cikin ƙarar, yana neman kotu ta umarci a sake shi bisa beli, yana mai cewa tsare shi da aka yi ba tare da cika sharuɗɗan doka ba ya saɓa haƙƙoƙinsa a matsayin ɗanadam.
Ana kuma sa ran a rana guda za a gurfanar da shi kan tuhume-tuhumen da DSS ta riga ta shigar.
Lauyoyinsa sun jaddada cewa rashin amsa buƙatar belin da kuma rashin nuna takardar umarnin tsarewa na daga cikin abubuwan da suke ƙalubalanta a shari’a, yayin da suke jiran matakin kotu kan buƙatunsu.