Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabbin hanyoyin da malaman Musulunci a Najeriya ke yaɗa wa'azi
Malaman addinin Musulunci a Najeriya kan gabatar da wa'azi a tsawon watan azumin Ramadan.
An ɗauki lokaci mai tsawo malaman na gudanar da wa'azinsu galibi a masalallatai, inda ɗimbin mutane ke halarta domin su saurara.
Sannu a hankali, zuwan kafafen yaɗa labarai irin su radiyo da talbijin sun taimaka wajen yaɗa wa'azin malaman.
Sai dai bayan lokaci mai tsawo, zuwan sabbin fasahohin zamani sun sauya yadda malaman ke isar da wa'azin nasu.
Akwai hanyoyi da dama na shafukan sada zumunta da malaman ke amfani da su wajen isar da karatunsu, waɗanda a wasu lokutan ma kan taimaka musu wajen tara makudan kuɗi, a cewar ƙwararrun masu amafni da shafukan.
A cikin wannan muƙala mun duba irin sabbin hanyoyin da malaman ke amfani da su wajen isar da wa'azin da kuma alfanun da hakan ke kawo musu.
Kai-tsaye a Facebook
Galibi a yanzu manayan malamai kan yi amfani da tsarin yaɗa wa'azinsu kai-tsaye lokacin da suke yinsa a shafin Facebook.
Malaman kan yaɗa wa'azin, ko dai ta shafukansu ko kuma shafukan masallatai ko majalisunsu na karatu.
Akwai malaman da suke samun fiye da masu kallo 7,000 a lokaci guda, wani abu da ke nuna tasirin malaman a shafukan.
Mutane da dama ko almajiran malaman kan taimaka wajen yaɗa wa'azin a shafukan.
Dandalin Facebook
Baya ga yaɗa karatun kai-tsaye a shafin Facebook, akwai kuma malaman da ke wallafa bidiyon karatun nasu bayan sun kammmala.
Hakan na bayar da dama ga wadanda ba su samu damar gani kai-tsaye ba, su kalla daga baya.
Shafin Facebook ya kasance kan gaba cikin shafukan sada zumunta da aka fi amfani da su a Najeriya.
Shafin YouTube
Wata kafa da malaman a yanzu ke amfani da ita wajen yaɗa wa'azin azumi ita ce shafin YouTube,
Kamar dai yadda suke amfani da shafin Facebook, malamai da dama kan yi amfani da shafin YouTube wajen ɗora karatunsu a kai bayan kammala wa'azi, domin bai wa masu kallo damar saurara.
ta hanyar YouTube mutane da dama kan samu karatuttukan malamai da suke da muradin kalla daga duk inda suke.
Shafin TikTok
Shi ma shafin TikTok na daga cikin hanyoyin da ake yaɗa karatun malamai.
Dandalin TikTok shafi ne da matasa maza da mata suka fi yin karakaina a ciki, don haka ne wasu malaman ke amfani da wannan dama wajen aika karatunsu.
Galibi kuma wasu almajirai ko mabiyan malaman ne ke buɗe shafukan domin yaɗa karatun malaman.
Wane tasiri kafofin ke yi wajen yaɗa wa'azin?
Dr Aliyu Tilde mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya ce amfani da waɗannan hanyoyi ya taimaka wajen yaɗa karatun malamai zuwa wurare masu nisa.
Haka ma Dr Tilde ya ce lamarin ya kuma sauƙaƙa wa masu sauraron wa'azin malaman wajen samunsa da sauƙi.
Shi ma Abdullahi Salihu Abubakar da aka fi sani da Baban Sadiq ƙwararren mai binciken hanyoyin sadarwar intanet da kuma tasirinsu a ƙasashe masu tasowa, ya ce waɗannan kafofi suna taimakawa wajen sauƙaƙa yaɗa karatun malamai cikin sauri da kuma sauƙi.
''Yana bai wa malaman damar isar da saƙonninsu har zuwa wurararen da ba za su iya zuwa ba'', in ji shi.
Ya kuma hanyoyin na taimakawa wajen ƙara fito da malaman a idon duniya a kuma sansa a ko'ina a fadin duniya.
Wace riba malaman ke samu ta hanyoyin?
Akwai riba mai gwaɓi da masu amfani da shafukan sada zumunta ke samu ta hanyar ɗora abubuwa a shafukansu.
Don haka Baban Sadiq ya ce su ma malaman da ke ɗora karatunsu za su amfana da wannan riba.
''Za su iya samu, kasan waɗanann shafuka na biyan mutane ta hanyar la'akari da mutanen da suka kalli bidiyoyinsu ko hotunan da suka ɗora a shafukan'', in ji shi.
Ya ce su dama shafukan abin da suke buƙata shi ne samun mutane su shiga su kalli abubuwa a shafukan.
''Su waɗannan shafuka suna bayar da dama, iya adadin mutanen da ke kallonka, adadin kuɗin da za ka samu'', a cewar masanin kafofin sada zumuntar.
Ya ci gaba da cewa amfani da kafofin tamkar da abin nan ne da Hausawa ke cewa ba ni gishiri in ba ka manda.
''In dai ka kawo musu mutane masu yawa to lallai za su biya, kuma kuɗaɗe masu yawa, ya danganta daga shafi zuwa shafi'', kamar yadda ya bayyana.
Hanyoyin da za ku bi don samun tarin mabiya
Galibi dai manyan malamai ne suka mamaye waɗannan kafofi na sada zumunta wajen isar da wa'azinsu.
Yayin da ragowar malaman da ba su da mabiya ke fafituka a shafukan da masu kallo ƴan ƙalilan.
To amma Baban Sadiq ya ce akwai dabaru masu yawa da ya kamata malaman su bi domin inganta shafukan nasu domin samun ƙarin tarin mabiya.
Dabarun haɗar da:
- Samun ƙwararrun masu kula da shafukansu
- Samun ingantattun kayan aiki da za su ɗauki hoto da sauti mai kyau
- Samun abokai masu yawa a shafukan
- Yawan wallafa abubuwa a shafukan
- Yawan tallata bidiyon da za ku wallafa kai-tsaye kafin lokacin
- Sannan ka riƙa saka wasu suna tallata maka
Masanin shafukan sada zumuntar ya ce su waɗannan shafuka sai an ririta su, an rene su kafin a kai ga cin moriyarsu.
''Su mutane a shafukan sada zumunta, kamar yara ne sai ka jawo hankalisu sannan su zo shafinka'', in ji shi.