Malaman Musulunci masu yawan mabiya a shafukan sada zumunta a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 5

Matashiya:Wannan maƙala ba ta taskace waɗannan malaman a matsayin waɗanda suka fi sauran malaman mabiya na zahiri ko kuma suka fi tarin ilimi ba. Face kawai an yi la'akari ne da mabiya a shafukan sada zumunta.

Zamani da kuma fasahar sadarwa sun sa wasu malaman Musulunci a arewacin Najeriya samun ɗaukaka da yawan mabiya a kafafen sada zumunta ko kuma soshiyal midiya.

Hakan kuma ana ganin ba zai rasa nasaba da irin yadda malaman suka karɓi shafukan na soshiyal midiya wajen yin wa'azi da tunatarwa ba.

Hakan ne ya sa BBC ta yi duba da nazari kan shafuka uku - Facebook, Instagram da Youtube na kowane daga cikin malaman guda biyar, inda kuma daga nan muka tattara alƙaluman namu.

Kasancewar Facebook kafar da ta fi tara ƴan Najeriya da ma Afirka, mun ɗauki Facebook a matsayin mizanin farko wajen tantance wanda ya fi yawan mabiya.

Farfesa Isa Ali Pantami

Farfesa Sheikh Ali Isa Pantami ya kasance tsohon ministan sadarwa na Najeriya a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Duba ga shafinsa na Facebook, Sheikh Pantami wanda malamin addinin Musulunci ne da ke gudanar da wa'azozinsa a masallacin Annur da ke unguwar Wuse a birnin Abuja, yana da mabiya a shafinsa da suka kai Miliyan biyu.

A shafin Instagram kuma, shehin malamin yana da masu bibiyarsa 858,000.

Sai dai BBC kuma ta duba shafinsa na Youtube, malamin na da abokan hulɗa 91,700, ƙasa da abin da Sheikh Aminu Daurawa da Sheikh Tijjani Gurumtum suke da shi.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda shi ne shugaban hukumar Hizba a jihar Kano, shi ma malamin addinin Musulunci ne mai yawan mabiya a kafafen sada zumunta.

Nazarin da BBC ta yi a shafinsa na Facebook, malamin yana da mabiya miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas da ke bibiyar sa a shafin.

Sheikh Daurawa kuma yana da mabiya 178,000 a shafinsa na Youtube.

Sai dai kuma malamin ba shi da mabiya sosai a shafinsa na Instagram inda yake da mutum 2,300 da ke bibiyar shafin nasa.

Sheikh Ahmad Guruntum

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum, kamar yadda shafinsa na Facebook ya ce yana da mabiya da suka kai 944,000.

Sheikh Guruntum, wanda ke zaune a jihar Bauchi na ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci da karatunsu ke yaɗuwa sosai a ƙasar Hausa da maƙwafta.

A shafin Instagram kuma malamin na da mabiya 10,400, inda mutum 170,000 ke bibiyar sa a shafinsa na YouTube.

Sheikh Ahmad Gumi

Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ɗa ne ga marigayi Malam Abubukar Gumi fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a arewacin Najeriya.

Sheikh Gumi wanda likita ne kuma tsohon soja yana da ɗimbin masu bibiyarsa a shafukansa na sada zumunta, inda yake da mutum 790,000 a Facebook .

Haka nan kuma shehin malamin na da mutum 271,000 a shafinsa na YouTube wanda hakan ma ke nuna ƙarancin mabiyan a shafin.

Dr. Bashir Aliyu Umar

Sheikh Bashir Aliyu Umar wanda ke gudanar da wa'azinsa a masallacin Alfurqan da ke Kano yana da mabiya aƙalla 761,000 a shafin Facebook.

Haka nan kuma malamin na da aƙalla mabiya 29,500 a shafinsa na instagram, sai kuma mabiya aƙalla 8,6700 a shafinsa na YouTube.

Yana daga cikin malaman da wa'azinsu ke yaɗuwa ta shafukan sada zumunta.

Dr. Abdallah Usman Gadon Ƙaya

Dr Gadon Ƙaya, wanda ke zaune a birnin Kano yana da mabiya aƙalla 721,000 a shafinsa na Facebook yayin da yake da mabiya aƙalla 112 a shafinsa na Instagram.

A shafin YouTube kuwa malamin yana da mabiya aƙalla 84,000.

Muhammad Kabir Haruna (Gombe)

A nasa ɓangaren, sakataren ƙungiyar JIBWIS na Najeriya, Muhammad Kabir Gombe yana da mabiya aƙalla 590 a shafinsa na Facebook.

Sheikh Gombe na daga cikin malaman da ke yaɗa da'awarsu kai-tsaye a shafukansu na sada zumunta.

Farfesa Ibrahim Maqari

Farfesa Ibrahim Maqari wanda ɗan asalin birnin Zaria ne ya kasance babban limamin masallacin babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Sheikh Maqari Farfesa ne a harshen Larabci a jami'ar Bayero da ke Kano.

Duba ga shafin malamin na Facebook, BBC ta ga yawan masu bibiyarsa sun kai 555,000, waɗanda ke samu karatunsa da ma wallafe-wallafensa.

A shafinsa na Instagram kuma shehun malamin na da mabiya 496,000.

To sai dai Farfesan na da mabiya 4,470 ne a shafinsa na YouTube.

Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah

Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah malamin ne da shi ma a yanzu ake jinsa a arewacin Najeriya, inda yake gudanar da karatuttukansa a jihar Kaduna.

Da muka garzaya shafinsa na Facebook, mun ga yana da mabiya dubu 730, waɗanda suke bibiyar karatunsa ta kafar.

Da BBC ta zargaya shafin malamin na Intagram, ta samu yana mabiyansa guda 364 ne kawai zuwa yanzu.

Imam Junaidu Abubakar Bauchi

Sheikh Junaidu Abubakar Sadiq, malamin addinin musulunci ne da aka haifa a garin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 1992.

Yanzu haka yana cikin matasan malaman da suka jan hankali a kafofin sadarwa na zamani.

Da BBC ta leƙa shafinsa na Facebook, mun ga yana da mabiya dubu 628 da suke bibiyar karatunsa.