Halin da dutsen da Annabi Musa ya yi magana da Allah ke ciki

    • Marubuci, Yolande Knell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shekaru da dama, masu ziyara dutsen Sinai na ziyarar tasu ne ta hanyar samun ɗan jagora daga cikin Larabawa mazauna yankin, inda su kan hau kan duwatsu suna kallon yadda wajen yake.

Amma a halin da ake ciki yanzu, wannan waje mai daraja sosai ga Yahudawa da kiristoci da kuma Musulmai na fuskantar barazanar sauya fasali saboda da shirin da Masar ke yi na mayar da shi wata babbar cibiyar yawon buɗe ido.

Wajen da jama'ar Masar suka fi sani da Jabal Musa, tarihi ya nuna cewa a nan ne aka yi wa Annabi Musa wahayi. Alƙur'ani da Baibul sun bayar da labarin cewa a kan dutsen ne Allah ya yi magana da Annabi Musa.

Hukumomi a Masar dai sun sha musanta cewa suna ƙoƙarin shafe wajen, amma duk da haka ana bayyana damuwa kan makomar wajen da Hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ware a matsayin wajen tarihi na duniya.

Wajen da ke tsakiyar daji ya ƙumshi wuraren ibada da tsaunuka da kuma kauyen da mutane ke zaune. A yanzu ana gina otel ɗin alfarma da manyan kantinan saida kaya da kuma gidajen zamani.

Asalin mazauna wannan yanki su ne larabawa ƙabilar Jebeleya waɗanda a yanzu an rushe gidajen su ba tare da biyan diyya yadda ya kamata ba, sannan aka tilasta masu haƙe kabarin ƴan uwansu daga wata maƙabarta da hukumomi suka ƙwace domin gina wajen ajiye motoci.

Ben Hoffler, wani marubuci ɗan Birtaniya wanda ya yi alaƙa ta kusa da mazauna Sinai ya ce an gabatar da ƙudirin sauya fasalin wajen a matsayin wani abu da ya dace da ƙoƙarin bunƙasa harkar yawon buɗe ido da samar da kuɗin shiga, amma a zahiri mutanen yankin ba su maraba da shirin.

Ya shaidawa BBC cewa "Wannan ba ci gaba bane, al'ummar Jebeleya ba su maraba da shi domin a ganin su, wani mataki ne kawai na biyan buƙatar wasu baƙi ba tare da la'akari da asalin jama'ar wajen ba.''

Al'ummar wajen da yawan su ya kai 4,000 sun ƙi yarda su yi magana kai tsaye game da ƙoƙarin zamanantar da garin su.

Kawo yanzu dai ƙasar Girka ce ta ke ɗaga murya a kan shirin na Masar saboda alaƙar da ta ke da ita da tarihin wuraren ibada da ke yankin.

Jayayya ta yi ƙamari tsakanin Athens da Alƙhahira, a cikin watan Mayu, bayan wata kotun Masar ta yanke hukuncin cewa cocin St Catherine tana cikin yankin da gwamnati ke ƙoƙarin sake wa fasali, duk da kasancewarta ɗaya daga cikin wuraren bauta na addinin kirista masu daɗaɗɗen tarihi. .

Bayan jayayya a kan batun na tsawon gomman shekaru, alƙalin kotun ya yanke hukuncin cewa cocin za ta mallaki ginin da take kai ne kacal, yayin da gwamnati ke da iko da haraba da sauran wuraren tarihi masu alaƙa da addini.

Archbishop Ieronymos II na Athens, kuma shugaban cocin Girka ya yi gaggawar fitowa ya nuna rashin amincewa da wannan hukunci.

"An ƙwace filin coci kuma za a sauya mashi fasali. Ana barazanar shafe wurin bauta mai daraja sosai.'' in ji sanarwar da ya fitar.

A wata hira da ya yi, Archbishop Damianos na cocin St Catherine ya bayyana lamarin a matsayin ''babbar barazana gare mu''.

'Kyauta ta musamman' ko rashin mutumta addini?

Masar ta fara shirinta na bunƙasa wuraren yawon buɗe ido ne a 2021. Shirirn ya haɗa da buɗe otel-otel da kafa babbar cibiyar shaƙatawa da kuma faɗaɗa ƙaramin filin jirgin sama da ke kusa da dutsen Sinai.

Gwamnati ta yi alƙawarin cewa shirin zai zamo ''Kyautar Masar ta musamman ga duniya da dukkan addinai''.

A bara, ministan gidaje na Masar Sherif el-Sherbiny ya ce ''aikin zai samar da wuraren shaƙatawa masu ƙayatarwa ga masu yawon buɗe ido, da zamanantar da wurin mai ɗimbin tarihi''.

Yayin da aikin ya tsaya a halin yanzu saboda rashin kuɗi, akwai wasu wuraren da aka kammala aikin sauya fasalin. Daga cikin su harda wuraren da suka shafi wuraren ibada masu daraja sosai ga addinai.

A 2023, Unesco ta bayyana damuwa kan aikin kuma ta buƙaci Masar ta dakatar da shi da kuma sake nazari a kan tasirin sa ga duniya.

Ba a aiwatar da shawarar ba.

A cikin watan Yuli, hukumar kare al'adu ta duniya ta aikewa Unesco wasiƙa tana neman a sanya cocin St Catherine da harabarta a cikin jerin wuraren tarihi masu fuskantar barazana.

Masu fafutuka sun kuma tuntuɓi sarki Charles a masayinsa na uban gidauniyar St Catherine inda suka nemi ya matsa lamba domin hana a shafe cocin. Sarkin ya bayyana wajen a matsayin ''Babban wajen tarihi na addini mai muhimmanci ga al'umma'.

Ba dai wannan ne babban aikin sauya fasalin wurare da ya fara shan suka a Masar ba, saboda yadda ake ganin hukumomi na yin facali da muhimmancin tarihi na musamman da wurare da dama na ƙasar ke da shi.

Sai dai gwamnatin na ganin irin waɗannan ayyuka a matsayin masu mhimmanci ga bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.

Fannin yawon idon Masar ya fara farfaɗowa daga koma bayan annobar Corona, sai kuma yaƙin Gaza ya taso. Gwamnatin ta sanar da ƙudirinta na samun masu ziyarar buɗe ido miliyan 30 kafin 2028.

A ƙarƙashin gwamnatocin Masar da suka gabata harkokin kasuwanci sun bunƙasa a Sinai, kuma ana ɗaukar matakai a kan yankin ne ba tare da tuntuɓar asalin al'ummar yankin ba.

Isra'ila ta mamaye yankin a 1967, lokacin yaƙin gabas ta tsakiya kuma sai a 1979 yankin ya koma hannun Masar. Asalin mutanen yankin suna ƙorafin cewa ana ɗaukar su kamar ba mutane ba.