Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Malamai 10 da suka fi yin amo a arewacin Najeriya
- Marubuci, Usman Minjibir
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 10
Allah ya huwace wa arewacin Najeriya da manyan malaman addinin Musulunci masu yawan gaske, inda kowace jiha da birni da ma garuruwa ke da malamai masana fannoni a addini.
Duk da yawan malaman da yankin ke da su to amma an fi jin amon wasu a kan wasu saboda wasu dalilai da suka haɗa da taƙaddama ko yawan mabiya ko kuma tattaunawa da jama'a ke yi a kansu a soshiyal midiya da dai sauran su.
BBC ta yi nazari dangane da irin amon da malamai ke yi a tsakanin al'ummar yankin musamman a kafafen sada zumunta musamman tsakanin 2020 zuwa 2025.
Gargaɗi: Wannan ba ya nufin cewa su ne suka fi kowa ilimi ba ko kuma yin shura. Maƙalar ta mayar da hankali kan malaman da aka fi jin amonsu a soshiyal midiya a tsakanin 2020 zuwa 2025.
Sheikh Yahaya Masussuka
Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka malamin addinin Musulunci ne a arewacin Najeriya wanda ke da fahimtar Alƙur'ani zalla ko kuma da ake kira da Ƙur'aniyyun.
Sheikh Yahaya na ɗaya daga cikin malaman da ke amo a arewacin Najeriya musamman a kafafen sada zumunta inda wa'azozinsa ke mayar da hankali wajen rushe hadisai da ya ce suna taɓa ƙimar Annabi Muhammad SAW.
A baya-bayan nan ya yi suna da wata sara da yake kira da "Ritaya Dole", da ya ce ya ƙudiri aniyyar sanya wa koyarwar mabiya fahimtar "Salaf" ko kuma da ake kira Ahlussunnah, burki.
Wannan al'amari ne ake ganin ya ƙara rashin jituwar da ke tsakanin malamin da mabiya fahimtar Salaf ɗin inda suka yi ta musayar yawu a wa'azozinsu da soshiyal midiya.
A ƙarshen makon da ya gabata, Sheikh Yahaya Masussuka ya fara wata ziyarar da ya kira ta haɗin kai ga malaman ɗarika a birnin Kano da Bauchi.
Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka mutumin jihar Katsina ne amma ɗan asalin jihar Bauchi.
Sheikh Lawal Triumph
Sheikh Lawal Abubakar da aka fi sani da Malam Lawal Triumph matashin malamin addinin Musulunci ne da ke bin fahimtar Salaf ko kuma Ahlussunnah.
Malamin yana cikin matasan malamai a birnin Kano da ma arewacin Najeriya da ke da tarin mabiya sannan kuma yake yin amo a soshiyal midiya.
Batun da ya ƙara fito da Malam Triumph a baya-bayan nan shi ne wa'azinsa da ya yi kan mu'ujuzozin Annabi Muhammad SAW da ya ce ba su inganta ba, al'amarin da ya janyo zanga-zanga har ta kai ga gwamnan Kano ya kafa kwamitin da ya zauna da malamin domin kare kansa.
Sheikh Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Kabara na daga cikin malaman addinin Musulunci da suke amo a arewacin Najeriya har ma da ƙasashe masu maƙwabtaka dangane da fahimtarsa ta "tsaftace addinin Musulunci" daga "Hadisan ƙarya", kamar yadda yake bayyanawa a karatuttukansa.
Sheikh Abduljabbar na da mabiya masu yawa a faɗin Najeriya ta hanyar makarantarsa da ake kira Ashabul Kahfi.
A makon da ya gabata ne hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta sauya wa malamin gidan yari, inda ta ɗauke shi daga gidan yarin Kurmawa da ke Kano zuwa gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Hukumar ta ce ta yi hakan ne bisa dalilin cewa malamin yana fuskantar barazana.
Ana ganin cewa hakan bai rasa nasaba da wani bidiyo da ake zargin wani ɗalibinsa ne ya yi ba, cewa za su ɓalle gidan yarin na Kano su fito da malamin nasu kasancewar zaman da malamai suka yi da Sheikh lawal Triumph bai kai ga kamu da tsare shi ba, duk kuwa da cewa an tuhume shi da irin abin da aka tuhumi Sheikh Abduljabbar na "ɓatanci" ga annabi.
A 2022 wata kotun addinin Musulunci ta yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin "ɓatanci" ga annabi Muahhamd SAW, abin da malamin ya sha musantawa yana cewa shi kariya yake bai wa annabin.
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara na ɗaya daga cikin ƴaƴan fitaccen malamin addinin nan, marigayi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka.
Dr Ahmed Gumi
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na ɗaya daga cikin ƴaƴan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ya rasu shekaru fiye 30 da suka gabata, Sheikh Abubakar Gumi.
Dr Ahmad wanda bai taɓa ɓoye ra'ayinsa ba dangane da duk wani batu da ake tattaunawa, walau na addini ko kuma na siyasa, likita ne kuma tsohon soja.
Sheikh Gumi kamar mahaifinsa yana bin fahimtar Salaf ko kuma Ahlussunnah amma bisa mazhabar Malikiyya.
A lokuta daban-daban, Sheikh Gumi yana da fahimtar tantance hadisan gaskiya da na ƙarya, inda yake faɗin cewa "akwai hadisan bola", wani abun da ke janyo masa raddi daga malamai ƴan uwansa.
Batutuwan da a baya-bayan nan suka ƙara amon da malamin ke da shi a arewacin Najeriya su ne hana malamin shiga garin Makka domin yin Hajjin 2024, da kuma ziyarar da ya kai ƙasar Iran da rawar da ya taka a neman sulhu da ƴan bindiga.
Sheihk Ahmad Gumi ya yi shuhura a ra'ayin goyon bayan al'ummar Falasɗinawa da kuma neman haɗin kan Musulmai duk da banbancin fahimta da ke tsakani "domin tunkarar maƙiya Musulmai."
Sheikh Ibrahim Zakzaky
Malam Ibrahim El-zakzaky ya kwashe shekaru fiye da 40 yana "gwagwarmayar tabbatar da addinin Musulunci", kamar yadda yake yawan faɗi a wa'azozi da laccocinsa.
Sheikh Zakzaky wanda yake da fahimtar addinin Musulunci ta mahangar "iyalan gidan annabi", ko kuma mazhabar Shi'a kamar yadda ake kiran masu fahimtar, na ɗaya daga cikin malamai a Najeriya da suke da mabiya a faɗin duniya.
Babban al'amarin da ya ƙara amon malamin a Najeriya da wasu ƙasashen duniya shi ne gangamin buƙatar gwamnatin Najeriya ta sake shi daga tsarewar da ta yi masa na tsawon shekaru fiye da shida wato daga 2015 zuwa 2021.
Sheikh Zakzaky ya zargi sojojin Najeriya da yi "wa almajiransa kisan kiyashi" a 2015, duk da sojojin sun musanta inda suka ce "mabiyan malamin ne suka tare musu hanya." To amma kotu ta wanke malamin daga dukkan tuhume-tuhumen.
Malam Zakzaky na ɗaya daga cikin malaman addinin Musulunci a Najeriya da suka kwashe shekaru masu yawa na rayuwarsu a gidan yari, bisa saɓani da yake samu da gwamnatoci.
An haifi Sheikh Zakzaky a birnin Zazzau na jihar Kaduna, inda ya girma tare da yin da'awa amma a yanzu haka yana zaune a Abuja, babban birnin Najeriya, tun bayan sakin sa da aka yi a 2021 sakamakon wanke shi da kotu ta yi kan tuhume-tuhumen da aka yi masa.
Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe gidan malamin da ke unguwar Gyallesu a Zaria, wani abu da ake ganin shi ne dalilin zamansa a Abuja.
Duk da cewa babu alƙaluma dangane da yawan almajirai ko mabiya da kowane malami ke da su a Najeriya amma masu lura da al'amura na ganin cewa Sheikh Zakzaky ne ya fi kowa yawan mabiyan da suka yarda shi kaɗai ne jagoransu kuma a shirye suke a koda yaushe su karɓi umarni daga wurinsa.
Farfesa Ibrahim Maqari
Farfesa Ibrahim Maqari shi ne babban limamin masallacin birnin tarayya, Abuja sannan kuma farfesan Arabiyya ne da ke koyarwa a sashen Arabiyya da ke jami'ar Bayero Kano.
Sheikh Ibrahim Maqari mabiyin ɗarikar Tijjaniyya ne da ke shan suka daga ƴan ɗarikar tasa da kuma sauran masu banbancin fahimta.
Farfesa Maqari shi ma yana ɗaya daga cikin malaman da ba sa ɓoye fahimtarsu kan al'amuran addini ko na siyasa.
Manyan batutuwan da a baya-bayan nan suka ƙara wa Farfesa maƙari amo su ne burinsa na ƙoƙarin haɗin kan Musulmi inda ya fara ziyarar malamai da ke da banbancin fahimta da shi domin neman a haɗa kai tsakanin dukkannin ɓangarorin Musulmi. Wannan ya janyo masa suka har a cikin gida.
Ɗaya batun shi wanda Farfesa a cikin karatu ya bayar da fatawar cewa "mace za ta iya bayar da kanta" idan tana cikin tsananin yunwa domin samun abinci, wani abu da ya sa malamai suka yi masa ca a ka.
Farfesa Muhammad Sani Rijiyar Lemo
Farfesa Muhammad Sani Rijiyar Lemo na ɗaya daga cikin malamai da ke koyarwa a jami'a da kuma majalisi.
Shi ma kamar sauran malaman da ke bin fahimtar Salaf, ba ya shakkar bayyana ra'ayinsa dangane da al'amuran da suka jiɓanci addini musamman tauhidi.
Farfesa Rijiyar Lemo wanda ya ƙware a fannin Hadisi, ya kammala rubuta tafsirin Alƙur'ani wanda ya ƙara masa amo a duniyar Musulmai.
A baya-bayan nan malamin ya fuskanci raddi da martani daga malaman da suka samu saɓanin fahimta kan fitaccen malamin nan mai waƙe ɗan ƙasar Misrawanda ya rasu a 1294, Abu Abdallah Muhammad ibn Sa'id al-Sanhaji al-Busiri wanda ya rubuta littafin al-Burda.
Farfesa Rijiyar Lemo dai ya ce "shi Busiri ba malamin addini ba ne illa kawai mawaƙi ne" wani abun da ya janyo malamai suka yi masa ca.
Sheikh Nura Khalid
Sheikh Nura Khalid da ake yi wa laƙabi da "Digital Imam" shi ma malamin addinin Musulunci ne a Najeriya da ba shakkar faɗin ra'ayinsa dangane da batutuwan addini da na siyasa.
Digital Imam ya kasance limamin masallacin Apo da ke Abuja kafin a tuɓe shi sakamakon kiran da ya yi wa gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari na ta tausaya wa Talakawa, wani abu da aka ɗauka da suka maras ma'ana.
Burin Sheikh Khalid kamar yadda yake yawan maimatawa a wuraren karunsa da laccoci shi ne samun haɗin kan Musulmi da cimma zaman lafiya tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, da ake kira da "Interfaith".
Shehin malamin yana fuskantar suka daga malamai da dama kan batun "Interfaith".
Mabiya fahimtar magabata ta Salaf ko kuma Ahlussunna sun yi wa malam Nura Khalid ca a baya-bayan nan lokacin da aka gan shi wuraren Mauludin da ya gabata, inda suke ganin kamar ya sauka daga aƙidarsa ta asali da suka san shi da shi.
Sheikh Nura ya sha faɗin cewa Mauludi wuri ne na nuna son annabi Muhammad SAW.
Sheikh Aminu Daurawa
Malam Aminu Daurawa wanda shi ne shugaban Hizba a jihar Kano na ɗaya daga cikin malaman addinin Musulunci da ke da farin jini wurin masu sauraro da kallo.
Yana kuma ɗaya daga cikin malaman da ke da tarin mabiya a kafafen sada zumunta, inda mabiyansa suka zarce na kowane malami a arewacin Najeriya a 2024 kamar yadda wani bincike da jaridar intanet ta Prime Time News ta gano.
Sheikh Daurawa ya ƙware wurin yi wa masu sauraro ko kallo wa'azi ta hanyar wasu dubaru da suka haɗa da sanya karatu a ƙidayance. Misali, abubuwa 10 da ake so miji ya rinƙa yi wa mai ɗakinsa.
Daurawa Malami ne mai sassauci da ya san zamaninsa kuma yake bayar da fatawoyin da suka dace da zamanin mai tambaya.
Babban batun da ya ƙara masa amo shi ne wani bidiyo da ya bayyana a 2024 inda jami'an Hizba ke jefa wasu ƴan makaranta mata cikin motarsu, abin da ya janyo wa hukumar suka a faɗin duniya.
Farfesa Isa Pantami
Farfesa Isa Ali Pantami na ɗaya daga cikin malaman addinin Musulunci a Najeriya da suka samu damar shiga gwamnati a dama da su.
Sheikh Pantami ya yi ministan sadarwa na Najeriya daga 2019 zuwa 2023.
Duk da Pantami yana minista bai fasa karantarwa ba, inda yake tafsiri da azumi da kuma sauran karatuka a ranaku daban-daban a masallalcin Annur da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Masu bibiyar Farfesa Pantami sun shaida cewa Allah ya huwace masa kaifin basira wajen haddace lambar ayar alƙur'ani ko ta hadisin da yake batu a kai.
Farfesa na shan suka dangane da fatwoyin da yake bayarwa da wasu malaman musamman waɗanda suke da fahimta irin tasa ta magabata ko kuma Salaf, ke ganin ta sauka daga layi.
Babban abun da ya dauki hankalin ma'abota soshiyal midiya dangane da malamin shi ne fatawarsa da ya bayar cewa riƙe carbi ba bidi'a ba ne.
Pantami ya kawo ra'ayoyin malamai kusan guda huɗu dangane da riƙe carbi.
Bugu da ƙari, yawan kuka da shehun malamin ke yi kan batutuwan tausayi shi ma na ƙara sa mutane yin yamaɗiɗi da shi.