Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi
Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Dokta Ahmad Gumi a shirin Ku San Malamanku, sannn kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon:
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya mazaunin Kaduna Sheikh Ahmad Mahomud Gumi ya ce dalilin da ya sa yake yawan batun siyasa sosai a majalisinsa bai wuce ƙoƙarin dawo da mutane kan turbar da Musulunci ya shimfiɗa ba.
Malamin ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa cikin shirinta na musamman na Ku San Malamanku.
Dr Gumi, wanda ɗa ne ga shugaban ƙungiyar Izala na farko a Najeriya, Sheikh Mahmud Gumi, ya ce "Ina yawan maganar siyasa ne saboda Musulunci ya zo ne don shiryar da rayuwar mutane don haka ba yadda addini zai tafi ba tare da tsoma baki a kan al'amuran siyasa ba.''
Sai dai malamin ya ce hakan ba ya nufin yana da jam'iyyar siyasa, "siyasa a wajena ita ce koyar da mutane abu mai kyau a rayuwa da ƙoƙarin nuna wa mutane abin da ya dace su yi."
Ya ja hankalin malamai da su guji tsunduma kansu a siyasa in har ba su san ta sun fahimce ta sosai ba saboda idan suka yi hakan ɓarnar da za su yi sai ta fi haka.
Wane ne Dr Ahmed Gumi?
An haifi Sheikh Ahmad ranar 1 ga watan Oktoban 1960 ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai. A garin Kano aka haife shi a lokacin da mahaifinsa yake koyarwa a makarantar Koyon Harshen Larabci ta SAS da ke birnin.
Daga baya mahaifin nasa ya koma Kaduna bayan da aka ba shi matsayin mataimakin alƙalin alƙalai na Jihar Arewa.
Ya fara karatun addini a hannun mahaifinsa. Malam ya girma a Kaduna kuma a can ya yi dukkan karatunsa daga firamare har sakandare.
Sannan ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi karatun koyon likita da ya fara a shekarar 1982.
Bayan ya kammala ne sai kuma ya faɗa aikin soja inda aka tura shi asibitin sojoji na Yaba a Legas ya yi horon aikin likita na shekara daya, sannan ya yi horon soja a Jaji.
Ya yi karatun likitancinsa ne a ɓangaren aikin tiyata. Ya yi horo a fannin sojoji da suka ƙware wajen sauka daga jirgi da lema a Jaji. Ya bar aikin soja yana matsayin kyaftin.
Malam ya ce ya bar aikin soja da likitanci ne don ya cika burinsa na karatun Larabci da addinin Musulunci da yake da shi tun yana yaro.
Ya tafi Masar don ƙaro karatun addini a 1987 a Jami'ar Azhar. Daga baya ya samu shiga Jami'atu Ummul Qura da ke Makka a ƙasar Saudiyya.
Dr Gumi ya shiga Saudiyya a shekarar 1989 har zuwa shekarar 2011 bayan ya kammala karatu har zuwa digirin-digirgiri wato Phd.
Me ya sa ra'ayinsa ya sha bamban da na sauran malamai?
Malam ya ce a'a sai dai idan ra'ayin malamai ne ya sha bamban da irin ainihin abin da Musulunci ya zo da shi.
''A ƙoƙarin karkato da hankalinsu don dawowa kan hanya ne ya sa nake samun saɓani da malamai. Mutane sun ɓalle kowa ya zama limamin kansa da mazhabin kansa da rashin ganin girman na gabansa,'' a cewar malam.
Shehin malamin ya kuma yi magana kan rarrabuwar ƙungiyar Izala wanda ya ce tun yana Masar hakan ya fara faruwa, ''kuma tun mahaifina na da rai ake ta ƙoƙarin haɗa kansu. Ni ƙoƙarin haɗa kansu ma na yi ba raba su ba.''
Sai dai ya ci gaba da cewa "Amma ba mamaki a rarrabuwar kan ƙungiyar Izala, tun da ko Sahabban Manzon Allah SAW ma an samu rarrabuwar kai a tsakaninsu.''
Ya ƙara da cewa a lokacin da ya taso babu maganar rikice-rikice tsakanin bambancin addini. Duk a kan idonsu aka fara haka.
Ya yi kira da al'umma su dawo kan hanya ɗaya a daina bambance-bambance.
Wasu labaran da za ku so ku karanta
Tambayoyin da aka fi masa
Malam ya ce an fi yi masa tambayoyi kan azumi musamman ɓangaren ramuwar azumin mace mai ciki da shayarwa.
Sannan ya ce yana sha'awar karance-karance sosai.
Sheikh Gumi ya ce bai yi rubuce-rubuce da yawa ba saboda kusan kowane fanni an riga an yi rubutu a kai.
Amma ya ce babban rubutunsa shi ne wanda ya yi a digirinsa na uku. "Na yi bincike mai zurfi sosai a ɓangaren ƙiyasi, wanda shi ne ginshiƙin Fiƙihu, a kansa na yi digiri na uku, don haka na rubuta Risala a kansa.
An fara wallafa labarin a watan Nuwamban 2020, an sabunta a watan Maris ɗin 2024.