Ya kamata Shugaba Buhari ya buɗe bodojin Najeriya - Ahmad Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta buɗe iyakokin ƙasar saboda a samu sauƙi a wahalhalun hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a ƙasar.

Babban malamin, wanda ke zaune a jihar Kaduna da ke arewar ƙasar, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a faron makon nan.

Malamin ya ce matsalar tattalin arzikin kasa abu ne mai wahala ƙwarai da gaske, inda ya ƙara da cewa dole sai gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace.

''Na farko dai bai kamata a kulle boda a lokacin da mutane ke buƙatar abinci ba. Barin boda a buɗe na bai wa manoman duniya damar kawo abincinsu kuma hakan zai sa abinci ya yi araha, domin kowa na so ya sayar.

''Yanzu misali a Thailand ga shi nan sun yi shinkafa jibgi guda amma tana neman ta ɓaci. Ka ga idan suka ga za ta ɓaci kafin akai ga hakan sai su kawo ta da araha. A Amurka mun gani har madara ake zubarwa. To ka kulle boda kuma ba ka da isasshe ba dole a yi ɓarna ai.''

To amma a na ta bangaren, gwamnatin ta ce ba za ta budo boda ba a wannan karon.

Sheikh Gumi ya ci gaba da cewa ya kamata gwamnati ta duba batun wutar lantarki tare da rage kuɗin da ta ƙara. ''Ai mun san cewa ruwan Allah ne da na dam suke taimaka wa wajen bunƙsar lantarkin nan.

''Ba wani makuɗan kuɗi ake kashewa a harkar ba, to don me za a tsawwalawa mutane da albashinsu ma bai taka kara ya karya ba.

''Don haka ya kamata a sake lale a tsarin, ba mutane za a ƙuntatawa ba,'' a cewarsa.

To sai dai a nata bangaren gwamnatin ta ce tana kashe makudan kudade duk wata wajen biyan masu samar da wutar, kasancewar kamfanonin rarraba wutar lantarki ba sa iya biyan kudin wutar da ake tura musu.

Ana yi wa Dr Gumi kallon wani mai yawan sukar gwamnatin Shugaba Buhari tun kafin ma shugaban ya ɗare mulkin ƙasar.

Maganganun nasa na zuwa ne a lokacin da ƴan ƙasar da dama ke tsaka da guna-guni kan halin da aka tsinci kai a ciki na hauhawar farashin wasu kayayyakin abinci da ƙarin kuɗin lantarki da na man fetur.

Tun a ƙarshen watan Agustan da ya gabata ƴan Najeriyar ke ce-ce-ku-ce a shafukan sada sumunta kan yanayin da ake ciki na hauhuwar farashin kayayyaki.

Sai dai ko a ranar Litinin ma hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS ta fitar da wani rahoto da ta ce annobar Covid-19 ta ƙara assasa matsalar ƙarancin abinci a Lagos da Kano da Ribas da Abuja.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake 'yan kasar da dama sun koka kan matakin.

A watan Maris din shekarar 2020 gwamnatin Najeriya ta ce 'yan kasar sun ga irin amfanin da rufe iyakokin ƙasar ya yi a fannin tattalin arzikinta.

Sai dai 'yan Najeriya musamman a arewacin ƙasar na bayyana takaici kan tsadar kayan abinci wanda suka yi tunanin a baya cewa ana iya samun rangwame la'akari da tsare-tsaren gwamnatin.

Ƙarin labarai masu alaƙa