Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina Sheikh Abduljabbar Kabara yake?
Ƴan uwa da magoya bayan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda ke tsare a gidan yarin Kurmawa na Kano bisa tuhumar "ɓatanci" ga Annabi Muhammadu SAW, tuhumar da Malamin ya musanta kuma yake ƙoƙarin ɗaukaka ƙara, sun shiga ruɗani saboda rashin sanin halin da malamin ke ciki a yanzu haka.
Mabiya da iyalan Malamin dai sun shiga ruɗun a ranar Talata bayan da suka kai masa ziyara a gidan yarin amma sai suka tarar ba ya nan kuma ba su samu wata gamsasshiyar amsa ba daga jami'an gidan kason.
A ranar 15 ga watan Disambar 2022 ne dai wata babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi tuhume-tuhumen da aka yi masa.
'Mun ji cewa an mayar da shi Kuje'
"Mun sami labarin ɗauke Shaikh Abduljabbar daga gidan kurkuku na Kurmawa zuwa wani waje da ba mu sani ba. Daga baya mu ke jin raɗe-raɗin cewa wai an kai shi gidan yarin Kuje da ke Abuja," kamar yadda Malam Askia Nasiru Kabara wanda ɗan uwan Sheikh Abduljabbar ne ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ita ma ƙungiyar Mujamma'u Ashabil Kahfi Warraqeem, Najeriya wanda ta mabiya Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ce ta wallafa a shafin nata na Facebook cewa jami'an gidan yarin Kurmawa da ke Kano sun shaida musu cewa an ɗauke malamin nasu daga gidna yarin.
"A yau 14-10-2025 bayan shiga kai wa Maulana Amirul Wa'izina abinci da safe kamar yadda aka saba muka riski labarin cewa sakamakon wani bidiyo da aka saki da sunan masoya malam/ɗalibai na Maulana Amirul wa'izina suna bai wa gwamnati sati biyu idan ba ta sake shi ba za su ɓalle kurkukun Kurmawa su fito da shi.
Hakan ya janyo sama (gwamnatin tarayya) tai umarni ai masa transfer (sauya masa wuri) zuwa wani wajen na daban saboda dalilan tsaro sakamakon hakan tun Asubahin wannnan aana ta Talata .. aka zartar da wannan umarni wanda har kawo yanzu su ma hukumar gidan ta ce ba ta san inda aka nufa da shi ba," in ji ƙungiyar.
Me ya jawo sauyin?
Ƙungiyar ta Mujamma'u Ashabil Kahfi Warraqeem, Najeriya a shafin nata na Facebook ta ce hukumomin gidan yarin sun alaƙanta al'amarin da "wani bidiyo da aka yi cewa idan ba a saki Maulana ba to za a ɓalle gidan yarin a fito da shi."
Wani ni matashi ne dai da ake kyautata zaton magoyin bayan Sheikh Abduljabbar ne da ke zaune a wata ƙasa a Arewacin Afirka ya wallafa bidiyon a shafukan sada zumuta, inda yake yi wa gwamnatin Kano barazana idan ba ta fito da Sheikh Abduljjabar a mako biyu masu zuwa.
"Kun je kun yi sulhu kun yafe wa Lawal Triumph?...to za ku ga fushinmu mu ƴan ɗariku. Muna gaya wa gwamnatin jihar Kano sai mun nuƙurƙusa ta. Kai wallahi zai mun yi zanga-zangar da sai an kori Abba Gida-Gida daga gwamnan jihar Kano. Mun ba su sati biyu idan ba su sako Sheikh Abduljabbar ba na rantse da girman Allah sai mun fasa gidan yarin mun fito da Sehikh Abduljabbar. Za mu tada hankalin da wallahi sai an saka emergency (dokar ta-ɓaci) a jihar Kano...." in ji mai bidiyon.
Ana dai ganin wannan bidiyo da ke ɗauke da kalaman barazana da tunzura al'umma ba zai rasa nasaba da zaman da aka yi da Majalisar Shura ta Kano da Malam Lawal Triumph wanda shi ma aka zarge shi da kalaman ’ɓatanci" ga Annabi Muhammad SAW, waɗanda shi ma ya musanta.
Bayan zaman ne wani bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta ya nuna Malam Lawal Triumph ɗin yana neman afuwar dattawan Majalisar ta Shura inda yake cewa shi ɗansu ne kuma a kullum a shirye yake ya karɓi gyara daga wurinsu.
Martanin Ashabul Kahfi
Ƙungiyar ta Mujamma'u Ashabil Kahfi Warraqeem, Najeriya a shafin nata na Facebook ta yi alawadai da kalaman matashin wanda ta ce ba da yawunsu ya yi ba kuma ba abin da Sheikh Abduljabbar ya koyar da su kenan ba.
"Kowa ya san Maulana Amirul wa'izina da kiyaye doka da oda, kowa ya san kullum kiran malamin ga ɗalibansa shi ne zaman lafiya. Babbar hujja akan hakan shi ne abin da ya faru a kwanan nan na hana ɗalibansa fita zagayen takutaha da dakatar zagayen zikiri hatta ziyararsa sai da ya dakatar duk da doka ta ba shi damar haka.
"Duk ba don komai ba sai don gujewa abin da zai bayu (haifar) ga fitina, idan aka koma baya za a ga irin sakonnin da malamin yake bayarwa na a gujewa duk wani abu da zai bayu ga fitina." In ji Ashabul Khafi.
Martanin Ƴan uwan Sheikh Abduljabbar
Malam Askia Nasiru Kabara wanda ɗan uwan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ne ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa duk abin da ya sami ɗan uwan nasu to alhakin na kan hukumomi.
Ina so in yi amfani da wannan dama a madadin iyali da 'yan uwan Shaikh Abduljabbar in sanar da Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta ƙasa cewa duk abin da ya sami Shaikh Abduljabbar to su tabbata yana wuyansu.
Domin ba rami me ya kawo maganar rami?. Mun sani cewa hukumar kula da gidajen yari ta ƙasa tana da damar kai mutum duk inda ta ga dama, amma abin tambayar a nan shi ne me ya sa sai a wannan gaɓar aka ɗauke shi?" kamar yadda Malam Askia ya yi tambaya.
Abduljabbar na Kuje - Hukumar gidajen yari
Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa Sheikh Abduljabbar na gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Abuja.
"Shehun Malamin da kake magana a kansa yana ƙarƙashin kulawarmu. Kuma kamar yadda ka sani bisa dokar Najeriya, muna da damar sauya wa wani da muke tsare da shi gidan yari a duk lokacin da ya kasance yana fuskantar barazana ko kuma shi ya zama barazana ga zaman lafiyar al'umma," in ji Abubakar Umar, mai magana da yawun hukumar gidajen gyara hali ta Najeriya.