Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
A wannan mako, muna gabatar muku da maimaicin zantawarmu da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, wanda ya ce ya sha matuƙar wahala kafin ya haddace wata ayar Al-Ƙur'ani.
Wannan wani ɓangare ne na shirinmu mai taken "Ku San Malamanku".
Malamin ya ce ayar da ta fi ba shi wahala, wata aya ce a cikin Suratul Baqara, Iza Tadayantum..., wadda ita ce aya mafi tsawo a Littafi Mai Tsarki.
Ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa ya yi nazarin abubuwa kusan 61, da suke janyo yawan mutuwar aure a ƙasar Hausa.
Sheikh Aminu Daurawa ya ce hira da tambayoyi da ya yi wa zawarawa da 'yan mata da aurensu ya mutu na tsawon lokaci ne ya sa ya gano waɗannan dalilai.