Ku San Malamanku tare da Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya mazaunin jihar Kano a arewa maso yammacin ƙasar, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo ya ce ya rubuta tafisirin littafin Al-Ƙur'ani mai girma ne don fayyace ma'anoninsa da kuma hukunce-hukuncen da ke tattare da su.

Tafisirin shi ne irinsa na farko da aka buga da harshen Hausa, inda ya bambanta da na marigayi Sheikh Mahmud Gumi da marigayi Sheikh Nasiru Kabara ta wajen fito da hukunce-hukuncen ayoyin da kuma ƙarin bayani kan ma'anoninsa, da dangantakarsu da Hadisai.

Cikin watan Nuwamban 2020 ne Dr Rijiyar Lemo, wanda Malami ne a Fannin Koyar da Addinin Musulunci a Jami'ar Bayero ta Kano ya fitar da Tafsirin Al-Ƙur'anin wanda tuni aka fara fansar da shi a kasuwa.

Malamin na daga cikin malaman Najeriya da suke yawan rubuce-rubucen manyan littatafai da suke shiga duniya.

A lokacin da wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ya je don hira da shi a shirin ''Ku San Malamanku'' ya ga ɗumbin littattafai a tare da shi, kuma ya ce tun yana sakandare yake sayensu.

Littattafai nawa ya buga?

Dr Umar ya ce abubuwa biyu suka fi ɗaukar hankalinsa wajen karance-karancensa.

''Abu na farkon harshen Larabci shi karan kansa, kusan ina da sha'awar karanta littattafan adabi na Larabci.

''Abu na biyu littattafan Hadisi, sakamakon karanta littafin Sheikh Nasiruddin Albani ya ƙara min ƙaimin sha'awar ilimin hadisi.''

Malam ya ce tun yana makarantar sakandare ya fara rubuta littafi inda ya yi wani da ke magana a kan dole ne ga malami da ke karantarwa kan kafin ya dogara ga Hadisi to ya binciki ingancinsa, sannan ya dogara da shi a karantarwa ko a cikin wa'azinsa.

Dr Rijiyar Lemo ya ce bai san adadin littattafan da ya rubuta ba, wasu kuma ana kan hanyar buga su.

Daga ciki akwai Kitabu Iƙrab a shekarar 1995 lokacin yana digirinsa na biyu.

Malam ya ce hakan ya samo asali ne saboda ba abin da ya fi ba shi nishaɗi irin karatu da bincike, ''Ko a yanzu in dai ina gida to za ka same ni a laburarena wani lokacin har dare sannan na je na huta.''

Akwai Kitabu Zawabiduj Jurhi Watta'adhir na ɗaya da na biyu, wanda ya yi a matsayin kundinsa na digiri na biyu a shekarar 2000.

Sannan akwai irinsu Madrsatul Hadisiyya na ɗaya da na biyu, da Tahqiqu at tamyiz fi talkhisi ahadisi sarhil-wajiz daga na ɗaya zuwa na bakwai, wanda ya yi a matsayin kundinsa na digirin-digirgir.

Akwai Kitabu Nabiyyur Rahama da Tamamul Tauhid da littafin zamansu tare da Sheikh Ja'afar Mahmud Adam da sauransu.

Abin da ya fi ba shi wahala a fannin ilimi

Babban malamin ya ce babban abin da ya fi ba shi wahala a fannin ilimi shi ne maganar saki uku a kalma ɗaya.

Dr Rijiyar Lemo ya ce, ''Wannan mas'ala ce mai zurfin gaske.''

Ya ci gaba da cewa abu na biyu da ke ba shi wahala a fannin ilimi bai wuce masa'alar mace mai idda kan batun yin wanka ne kammala iddarta ko zuwan jini. ''Har zuwa yanzu wannan na da wahala don maganganun malamai a fannin na da faɗi,'' in ji malam.

Sannan malamin wanda ya yi haddarsa ta Al-Ƙur'ani a ƙasa mai tsarki ya ce Suratu An'am da Suratu Nahl da Suratu Isra ne suka fi ba shi wahalar haddacewa.

Wane ne Sheikh Dr Rijiyar Lemo

Malamin haifaffen garin Makkah ne a ƙasar Saudiyya, amma ya dawo Kano yana ƙarami.

Ya yi karatu a makarantar Masallaci ta Unguwar Kurna Asabe da makarantar Fukara'ul Musulumin, sannan ya yi ƙaramar sakandare a Aliya da ke Shahuci.

Daga nan sai ya je makarantar horar da malamai ta Arabiyya ATC.

Daga nan ya tafi Jami'ar Musulunci a Saudiyya a shekarar 1990 ya yi karatu a tsangayar ilimin Hadisi da nazarin Hadisi daga 1990-1994.

Ya yi digiri na biyu da digirin-digirgir duk a Saudiyya a fannin Hadisi. Ya koma Najeriya bayan kammala karatunsa a shekarar 2005.

Ko malam na mu'amala da Malaman Ɗariƙa?

Ganin cewa malam ɗan Ahlus Sunnah ne, BBC ta tambaye shi ko yana mu'amala da malaman sauran ɗariƙu?

Malam ya amsa da cewa Malaman Ɗariƙa ne suka fi koyar da shi musamman a sakandare, sannan mu'amalsarsu da shi tana da kyau. ''Ina girmama su tare da tuna alkhairansu.

''Na ƙaru da malamai da dama kamar marigayi Malam Sani Inuwa Kurna da marigayi Malam Musa Baƙin Ruwa da Malam Mahbub Abdulƙadir da Malam Hassan Bashir.

''Na tasirantu da su a karantarwa da ilimin da suke bayarwa.

''Ai ana samun mutane daga ɗariƙu daban-daban masu sassaucin ra'ayi ta wajen mu'amala da mutane,'' a cewar Dr Umar.

Me ya fi yi masa daɗi?

Malam ya ce galibi Hadisan da suke siffanta halayyar Manzon Allah SAW da ɗabi'unsa ne suka fi masa daɗi.

Sannan wani babban abin farin cikin da ba zai manta ba shi ne lokacin da aka ce an ɗauke shi zai je ya yi karatu a garin Madina da haɗuwa da manyan malamai. Samun wannan damar da bai taɓa kawo ta a ransa ba ita ta fi komai faranta masa rai.

Malamin ya ce babu abin da ya fi baƙanta masa rai a rayuwa irin ya ga ana wasa da ilimi ko a ana karan tsaye a harkar ilimi.

Limancin Sallar Juma'a a Masallacin Malam Ja'afar

A ranar da aka yi wa babban malamin Musulunci Sheikh Ja'afar Mahumud Adam kisan gilla ne Dr Umar ya yi limancin Sallar Juma'a na farko a Masallacin Ɗorayi.

"Lokacin an taru a ranar da aka kashe shi sai lokacin sallah ya ƙarato sai aka ce waye zai ja sallah sai duk ƴan uwa suka ce ni ne zan yi.

"Kwamishinan ƴan sanda ya tambaye ni kai za ka yi sallah? Na ce eh ni zan yi. A lokacin na haɗa abin da zan iya na hau mumbari na yi huɗuba. Dama na saba yin hudubobi na da ka saboda gudun zuwan irin wannan ranar," in ji shi.

Malamin ya bayyana kisan Malam Ja'afar a matsayin wata rana ta tashin hankali a rayuwarsa.

"Wanda yake tara da kai musamman a cikin abin da ya fi komai tsada wato da'awa ka wayi gari ka ji an kashe shi babu shakka akwai ɗaga hankali.

"Yadda na samu labarin kuwa iyalansa ne suka kira iyalina suke ce ga halin da ake ciki har an kai shi asibiti, kafin na je ma har ya rasu.''

Rai dangin goro

Malam ya ce abincin da ya fi so shi ne wake da shinkafa.

Sannan ya yi wasannin nishaɗi a shekarun ƙuruciya irin su wasan ƙwallo da sauran wasannin tsalle-tsalle, ''duk ƙaurina tabo ne na ciwon da nake a wajen ball. Amma daga baya karatu ya dauke hankalinmu."

Da aka tambaye shi ƙasar da yake sha'awar zuwa sai ya ce Indiya saboda abubuwan tarihi.

Malam yana da mata huɗu ƴaƴa masu yawa.