Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce fahimtar malaman Musulunci kan riƙe carbi?
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Wasu Musulmi na saƙala carbi a dantsen hannayensu wasu kuma ke rataya shi a wuyansu, inda wasu kuma suke riƙe carbin a hannunsu zuwa waɗanda ke saka shi a aljihu.
Ko ma dai a wane yanayi aka riƙe shi, Carbi, ga mutane da dama, ya zama wani ɓangare na rayuwarsu.
Carbi wanda ake yin sa da duwatsu ko kuma ƴaƴan itace, ya zama wani babban makami, ga masu riƙe da shi, wajen ambaton ubangiji a kodayaushe.
A kan samu me ƴaƴa 99 ko 33 ko ma mai dubu ɗaya ko fiye da haka - mai amfani da shi na samo daidai da buƙatarsa.
Zamani ya kawo nau'in Carbi iri-iri da ake kira "digital" da Turanci.
Me ake yi da carbi?
Carbi dai ba wani abu ba ne illa hanyar tantance lissafi ko kidayar yawan ambaton Allah ko zikiri da mai riƙe da shi ya yi.
"Kowa da irin abin da yake son yi. Wani ya fi son yin zikiri da yatsunsa musamman bayan kammala sallolin farilla. Wasu kuma na son yin zikirin da Carbi bayan sallar da ma sauran lokuta -keɓaɓɓu ko kuma gamagarin lokaci.
Wani zai ce maka idan babu carbi tare da shi yana sakaci wajen yawan ambaton Allah. Wani kuma zai ce maka shi ko babu carbi yana ambaton Allah." In ji Malam Shu'aibu Sani, wani ma sayar da Carbi a babban masallacin Abuja.
Kasashen Musulmi da dama na ƙera ko sassaƙa Carbi inda kuma suke shigar da su sauran ƙasashe ciki har da Saudiyya.
Ƙasashen Bangledash, da Indonesia da wani ɓangare na India.
Ra'ayoyin malamai kan riƙe carbi
Ga malaman da suke bin ɗarikar Sufaye a Afrika da suka haɗa da Tijjaniyya da Qadiriyya da Shazuliyya da Arusiyya da sauran su duka suna amfani da carbi.
Sai dai kuma a tsakanin malaman Salafiyya akwai banbancin fahimta dangane da riƙe carbi da kuma yin wani adadi na zikiri. Yayin da wasunsu suka sauya fahimtarsu a kan carbi inda yanzu suka sassauto cewa babu laifi a yi amfani da shi, amma amfani da yastu ya fi inganta, wasu kuwa har yanzu na da fahimtar cewa riƙe carbin ba shi da usuli a addini.
Sheikhul Islam da Al-Uthymeen
Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami a wani wa'azinsa na shekarun baya, an tambaye shi halasci ko rashin halascin amfani da tasbaha wato carbi a addinin Musulunci. Sai malamin ya bayar da amsa kamar haka:
"Magana a kan carbi maganganu ne guda biyu da malamai suka yi. Na farko suka ce bidi'a ne. Na biyu kuma suka ce halal ne. Kuma kowanne yana da dalili. Waɗanda suka tsananta akwai Sheikh Nasiruddeen Al-bani a cikin littafinsa na Silsilatul Ahadithul Dha'ifa Wal Maudhu'a juzi'i na farko hadith na 110. Shi dalilinsa shi ne annabi bai yi aiki da shi ba kuma sahabbai ba su yi ba." In ji Sheikh Pantami.
- Ra'ayin Sheikhul Islam Ibn Taymiyya
Sheikh Pantami ya kuma kawo ra'ayin Sheikhul Islam dangane da batun riƙe carbin.
"Sai kuma Shekhul Islam wanda ya yi maganganu guda biyu duka a cikin littafinsa na Majmu'ul Fatawa juzu'i na 22. Na farko ya ɗan tsananta maganar da ya yi a shafin na 187.
Na biyu kuma sai ya sassauta ya ce idan mutum ya riƙe shi a ɓangaren ƙidaya ba da nufin cewa riƙe shin ibada ba ne. Kawai yanayin tasbihi ne domin ka da ya manta. Ya ce to a nan ba za a ce bidi'a ba ne. Saboda haka ya sauƙaƙa."
- Ra'ayin Sheikh Al-Uthymeen
Farfesa Pantami ya kuma kawo ra'ayin Sheikh Saleh Al-Uthaimin kan riƙe carbin.
"An kuma tambayi Sheikh Saleh Altamimi Al-Uthymeen, a cikin littafinsa na Alliqa'i Al-Maftuh juzu'i na uku shafi na 30 a kan mas'alar carbi. Sai ya ce shi a fahimtarsa ba zai ce riƙe carbi bidi'a ba ne. Amma abin da ya amince shi ne yi da ƴatsa ya fi falala....ya ce yi da yatsu ya fi falala amma idan kana tsoron ka da ka manta sai ka riƙe carbi to ba laifi ba ne.
Dalilinsa kuma shi ne ya ce an samu a zamanin annabi wasu daga cikin sahabbai sun yi amfani da duwatsu wajen tasbihi inda suke ƙirgawa. Shi ne sai ya ce to ai carbi ma kamar ƙirgen ne da tsakuwa.
Saboda haka ya ce shi ba zai ce bidi'a ba ne tunda sahabbai an samu sun yi amfani da tsakuwa amma kuma ya ce annabi ya yi irshadi da amfani da yatsu inda annabin ya fada wa sahabbai cewa idan da za ku yi amfani da hannunku da ya fi falala amma bai ce kun yi bidi'a ba."
'Abin da ya sa nake riƙe carbi'
"Carbi yana saka ni na tuna da ubangiji wato na yi zikiri kamar Istigfari da Salatin Annabi. Ka ga ko tasbihin bayan sallar farilla, idan ban yi amfani da carbi ba to sai na rinƙa manta lissafin. Sannan idan yana hannuna na kan manta da komai idan ba zakiri ba," in ji Malam Muhammad Muhammad, wani mai amfani da carbi a Abuja.
Saɓanin wasu da ke amfani da carbi na latsawa, Malam Muhamamd ya ce "ai ni na fi jin daɗin wannan carbin mai ƴaƴa. Kullum yana aljihuna."
'Na fi amfani da "digital" carbi'
Ahmad Idris, shi ma matashi ne a Abuja wanda a koyaushe yake riƙe da carbinsa na latsawa wanda idan ba mutum ya kula sosai ba to zai iya cewa ƙawanya ce a yatsansa.
BBC ta tuntuɓe shi dalilin da ya sa yake riƙe carbin. Sai ya ce:
"Ni mutum ne mai son zikiri a duk inda na tsinci kaina. Kuma wannan carbin da kake gani a yatsana da shi nake yin lissafi duk da cewa ba ni da wata lambar da nake son cimma amma dai koyaushe a cikin zikirin nake.
Idan ban riƙe shi ba akwai yiwuwar zan sha'afa da yin zikirin."
Dangane kuma da tambayar da aka yi masa na me ya sa ya fi amfani da "digital" carbi, sai ya ce "idan na riƙe carbi mai ƴaƴa zan ga kamar jama'a na kallo na ni kuma don Allah nake yi. Shi ya sa ba na iya riƙe wancan." In ji Ahmed.