Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sultan Attahiru: Sarkin da ya bijire wa turawan mulkin mallaka a Najeriya
- Marubuci, Aisha Aliyu Ja'afar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 9
Shekaru 122 kenan tun bayan da turawan mulkin mallaka suka karɓe iko da arewacin Najeriya wadda ke ƙarƙashin ikon daular Usmaniyya da Shehu Usman Ɗanfodio ya kafa a 1804.
Sarki Muhammadu Attahiru I, shi ne Sultan na ƙarshe kuma na 12 a jerin Sarakunan Musulunci tun daga mujaddadi Shehu Usmanu Ɗan Fodio, kafin turawan mulkin mallaka su ƙwace iko da daular.
"Sarki Attahiru ya yi mulki na taƙaitaccen lokaci wato daga watan Oktoban 1902 zuwa 15 ga watan Maris din 1903. Kuma ya hau mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa Sarki Abderrahman Ɗan Abi Bakar a watan Oktoban 1902.
"A wannan lokacin turawa sun fara ƙwace iko da wasu sassan daular," in ji Dakta Abdullahi Hamisu Shehu, masanin tarihin daular Usmaniyya kuma malami a jami'ar Bayero da ke Kano.
Lokacin mulkinsa na cike da gwagwarmaya ta zuwan turawan mulkin mallaka waɗanda suka fara shiga arewacin Najeriya a shekarun 1890.
"Shehu Usmanu ɗan Fodio shi ne ya kafa daular tare da almajiransa da ƴan'uwansa, bayan gwagwarmayar jihadi a farkon ƙarni na 19.
"Jihadin ya haifar da juyin-juya hali na tsarin siyasa da tsarin rayuwa da zamantakewa, aka kuma ilimantar da mutane kan addinni, da tsarin Musulunci a arewacin Najeriya da kuma wani ɓangare na jamhuriyar Nijar." Kamar yadda dakta Abdullahi ya yi ƙarin haske.
Shigar Turawa Arewacin Najeriya
"Dama tun a baya turawa ikonsu ya taƙaita ne a bakin gaɓar ruwa, tun daga jihar Legas, amma daga baya suka samu suka tsallaka ta kogin Neja, inda suka kafa cibiyoyin kasuwancinsu a gaɓar a Bida da ke jihar Neja ta yanzu, kuma suka yi ta shigowa cikin ƙasar a hankali." In ji dakta Abdullah.
A ƙoƙarin kutsawa zuwa cikin sassan ƙasar wato arewacin Najeriyar daga bakin ruwa, turawan sun fito da wani salo mai kama da yaudarar sarakunan yankin.
"Abin da suka fara yi shi ne neman haɗin kan sarakuna ta hanyar yin yarjejeniya da za ta ba su damar shiga yankin domin yin kasuwaci. Sai dai abin da sarakunan ba su sani ba shi ne sanya hannun da suke ta yi, tamkar suna miƙa ikon su ne na gudanarwar mulki, wanda ya ba turawan damar shiga suka kakkafa iko."
''Dama tun a baya wasu turawan ƴan leƙen asiri sun shigo ta ruwa da ta ƙasa kamar su Mungo Park inda suka yi bincike da rubuce-rubuce kan yanayin fasalin ƙasa da yanayin siyasa da tattalin arziƙi da kuma albarkatun da yankin ke da shi, da ya sa suka dage sai sun kafa ƙahon zuƙa'' in ji dakta Abdullahi.
Sai dai masanin ya ce a wani ɓangaren kuma, ba turawan Birtaniya ne kaɗai ke da wannan sha'awa ta kutsawa da kama daular Usmaniyya ba, inda daga ɓangaren Nijar akwai turawan Faransa, daga ɓangaren Chadi ma akwai turawan Jamus da ke ƙoƙarin shiga su mamaye yankin.
''Tun da farko dama an zauna an yi kasafin ƙasashen Afrika inda aka rarraba su ga ƙasashen turawa, ita kasar Najeriya sai ta faɗa a kason Birtaniya''.
A shekarar 1890 turawan Birtaniya suka kafa tutarsu a Lokoja da ke jihar Kogi, wadda ke nufin duk ƙasar da ta kafa tutarta a wata ƙasa, to ta karɓi ikon gudarwar ƙasar kenan.
"Daga nan suka soma aika wasiƙu da yan aike zuwa daular Sokoto da manyan masarautun arewacin Najeriya cewa ga turawa nan za su shigo, inda aka nemi su sallama cikin ruwan sanyi ba tare da an yi yaƙi ba," in ji dakta Abdullahi.
Sai dai a wannan lokacin a arewacin Najeriya babu kimiyya ta yaƙi kamar makamai na zamani, su kuwa turawan suna da ci gaba inda suke da makamai kamar bindigogi, manya da ƙanana.
Sultan Attahiru ya yi turjiya
Sarki Attahiru ya ƙi amincewa ya miƙa wuya kamar yadda aka nema, wanda ya nuna wa turawa cewa lallai sai an yi yaƙi.
Da ma kuma Burtaniya ta shirya yaƙar daular ganin yadda turawan Faransa ke neman shiga daular ta ɓangaren Nijar domin mamaye yankin.
Sannan kuma akwai labarin cewa a daidai wannan lokacin Faransa ta fatattaki al'ummar daular Tokolo da ke tsakanin Senegal da Mali kuma ta ƙwace iko da ita.
''Amma kafin wannan lokacin masarautar Bida ta Nupe, tuni turawan sun mamaye ta sun kori sarakunansu, suna ta yi wa masarautun daular ɗauki ɗai-ɗai, tun daga masarutun kudancin daular zuwa na gabashi, waɗanda suka rage manyan masarautu ne kamar ta Sokoto da ta Kano da ta Hadejia.'' in ji Dakta Hamisu.
A yaƙin farko da aka fara gwabzawa tsakanin dakarun turawan da rundunar Sarki Attahiru, babu wanda ya samu nasara, bayan nan ne Sarki Attahiru ya kwashi kayansa ya nufi gabas domin yin gudun hijira.
"Akwai magannanu kan inda ya nufa, wasu masana tarihi na cewa ya yi niyyar zuwa ƙasa mai tsarki ne saboda ba su yi nasara ba, kuma ba za su zauna ƙarƙashin tsarin da ba na Musulunci ba, ko su zauna da waɗanda ba Musulmi ba su mulke su."
''Sannan kuma kuma akwai maganganun da suka shahara a lokacin cewa alamun ƙarshen duniya shi ne zuwan turawa, saboda haka duk Musulmai musamman malamai suna da tunanin turawa za su ƙaƙaba musu addininsu, su raba su da nasu, don haka kowa ya haɗa nasa-ya-nasa ya tafi.'' A kalaman dakta Abdullahi Hamisu.
Ina Sultan Attahiru ya nufa?
Dakta Abdullahi ya ce bayan sun kama hanya, an soma samun rarrabuwar kai tsakanin mabiyansa.
"Kan mabiyansa ya rabu gida biyu, wasu daga ciki ba su goyi bayan Sarki Attahiru ba na inda ya nufa, inda suka zame suka tafi wurare daban-daban, wasu kuma suka koma suka miƙa wuya ga turawan."
Bayan zagwanyewar mabiyansa, an bar Sultan Attahiru da mabiya ƙalilan inda suka nufi wurin wasu malamai da ke da'awar yaƙar turawa a lokacin.
"A lokacin, akwai wasu da suka soma da'awa da bayyana kansu a matsayin su ne Mahadi wanda zai bayyana a ƙarshen zamani, kuma ana ganin dama shi ne zai yaƙi turawa, kamar su Malam Hayatu daga yankin Gombe da Bauchi da Malam Jibril daga yankin Adamawa.
Kasancewar tawagar waɗannan mutane su ma suna yaƙi da turawa, sai Sarki Attahiru ya nufi inda suke domin a haɗa ƙarfi da ƙarfe ko za a samu nasara''.
Hakan ya sa daga wurin da Sultan Attahiru ya ci gaba da tafiya inda ya nufi yamma zuwa jihar Zamfara, inda ya yi mako uku, kuma talakawa da dama suka bi shi.
''Daga nan labari ya isa turawa cewa Attahiru na haɗa gagarumar tawaga da za ta iya dawowa ta yaƙe su, sai suka tura sojoji daga Zaria zuwa Zamfara su iske shi su kashe shi, sai dai ba su kai ga riskar sa ba''. in ji Dakta Abdullahi.
Daga nan ne Sarkin Musulmin ya tashi ya yi gabas zuwa yankin Gombe inda ya zauna a tsibirin Bima inda mabiyan Malam Hayatu da Malam Jibril da ke yankin suka shiga tawagarsa da kuma wasu talakawa da manoma, kuma ya ɗan daɗe a wurin.
"Ko a zaman nasa a wurin, ya ci gaba da hulɗar jakadanci da turawan inda suke ci gaba da cewa dole ne ya miƙa wuya ya sallama. Sarki Attahiru ya kuma rubuta wa Bauchi cewa yana neman a ba shi hanya zai tafi ƙasa mai tsarki, kuma a cewarsa ba faɗa yake nema ba."
Yadda Turawa suka kashe Attahiru a Mbormi
Duk da cewa Sarki Attahiru ya sanar da Turawa cewa shi ba yaƙar su zai yi ba illa dai yana neman hanyar da zai tafi zuwa ƙasa mai tsari ne amma ba su amince ba saboda ba su gamsu ba, suna ganin a hanyar zai iya ƙara tara mabiya ya koma ya yaƙe su, sai suka ci gaba da buƙatar ya miƙa wuya.
''A zamansu na Birma kusa da garin Mbormi da ke jihar Gombe, a nan ne sojojin Birtaniya, duk da dai akasarinsu baƙaƙen fata ne kusan su 1,000, da fararen fata sojoji 25, ɗauke da bindigogi da mashinga (machine gun), suka kewaye wurin da yake zaune da mabiyansa domin yaƙar su''.
Kuma bayan soma yaƙin ne a ranar 27 ga watan Yulin 1903, sojojin suka kashe shi a wurin, bayan harbin da aka yi masa a kai, kuma aka kashe ƴaƴansa biyu, tare da almajiransa da dama. Bayan kashe shi, Turawan sun kuma yanke kan Attahiru, suka ɗau hotunan Sarkin babu kai, suka baza su a baki ɗaya arewacin Najeriya domin nuna wa sauran sarakunan su gani don su miƙa wuya."
To sai dai duk da mabiyan Sarki Attahiru sun ga babu alamun nasara, ba su tsorata ba, inda suka yi turjiya aka yi ta kashe su.
"Tarihi ya nuna cewa a lokacin akwai waɗanda suka hau kan ganuwa suka ɗaure jikkunansu da juna ta hanyar amfani da igiya ta yadda babu yadda ɗayansu zai gudu," in ji wani mazaunin garin Mbormi, inda kabarin Attahiru yake a yanzu haka.
Masana na ganin wannan shi ne yaƙi "mafi muni a yaƙe-yaƙen karɓar mulkin masarautu da aka yi a Najeriya saboda an kashe mutane da dama." To amma ƙalilan da suka rage sun yi hijira zuwa ƙasa mai tsarki.
"Cikin waɗanda suka rayu har da ɗansa Muhammadu Bello wanda aka fi sani da Mai Wurno wanda ya ci gaba da jagorantar sauran mabiyan mahaifinsa da suka rage, inda suka nufi gabas zuwa ƙasa mai tsarki, sai dai an ce tafiyarsu a Sudan ta tsaya, inda da yawa daga cikin zuri'arsu ke ci gaba da rayuwa har zuwa yau,'' kamar yadda dakta Abdullahi ya yi ƙarin haske.
Mulkin mallaka ta hanyar sarakuna
Bayan kashe Sarki Attahiru, Turawan sun naɗa ɗansa Attahiru na biyu a matsayin sabon sarki.
''Idan turawa suka karɓi mulki a arewacin Najeriya, suna nazari ne kan su waye ke goyon bayansu, sai su naɗa su a matsayin sarakuna don su tabbatar da biyayya da aiwatar da tsare-tsarensu, saboda suna ganin idan ba su yi hakan ba kamar tsugono bai ƙare ba. Waɗanda kuma suka yi tawaye ko suka yi musu bore, ko da ba su kai ga yaki ba, sai turawan su tsige su,'' in ji dakta Abdullahi Hamisu.
Bayan kisan Sarkin Musulmin Attahiru, turawan sun kuma lissafa sarakunan da suka yi musu turjiya kamar Sarki Abubakar na Nupe da Sarki Ahamdu na Misau da kuma Sarki Alu na Kano inda aka garƙame su a kurkuku da ke Zungeru, wanda a lokacin nan ne hedikwatar turawa a arewacin Najeriya.
Daga nan sai turawan suka samar da tsarin daidaita masarautu, ko tattara su domin samar da manyan cibiyoyin gudanar da mulki, inda suka samar da gwamnan gwamnoni, wanda shi ne kamar shugaban ƙasa, a karkashin shi kuma akwai rasdan, sai shugabannin gunduma, sai kuma ofisoshi''.
Haka kuma sun samar da wasu sabbin masarautun dangane da abin da Birtaniya ke so ta aiwatar, wanda hakan ya ƙara yawansu da girmansu, kuma aka sauya wasu abubuwan kamar na siyasa da mua'amala da yadda ake karɓar haraji da wasu ayyukan.
Wannan tsarin ne kuma ya samar da wani tsari na mulkin jama'a ta hanyar sarakunan gargajiya da ake kira kira da turanci "Indirect Rule".
"Misali ba za ka ga turawa suna zuwa amsar haraji a gidanka ko kasuwa ba, ƴan'uwanka baƙaƙe za ka gani, amma a bayan fage suna gefe ko sama suna lura da komai, kuma an yi ta wannan tsarin tun daga lokacin har shekarar da Najeriya ta samu yancin kai a 1960.'' in ji Dakta Abdullahi.