Abu huɗu da suka faru a Kano bayan zargin Lawal Triumph da 'ɓatanci'

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da wani ɓangare na al'ummar jihar Kano suka gudanar da zanga-zangar lumana zuwa gidan gwamnati bisa zargin ɗaya daga cikin matasan malaman birnin Kano, Sheikh Lawal Triumph da yin "kalaman ɓatanci" ga Annabi Muhammad SAW), al'amura a Kano suka rincaɓe.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya yi wa dandazon matasan jawabi, ya nemi da su rubuto ƙorafe-korafensu a hukumance domin kafa hujjar ɗaukar mataki.

BBC ta yi nazari dangane da jerin abubuwan da suka faru tun bayan buƙatar gwamnan ta a gabatar masa da rubutaccen ƙorafi domin kafa hujjar ɗaukar mataki.

Ƙungiyoyi 8 sun shigar da ƙorafi

Wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Kano da aka fitar ranar 25 ga watan Satumba ta ce ofishin ya karɓi ƙorafe-ƙorafe daga ƙungiyoyi 8.

Yayin da wasu ƙorafe-ƙorafen ke zargin Sheikh Lawal Triump da ’ɓatanaci ga Annabi Muhammad, SAW', wasu na bayar da kariya ne ga Malamin inda suke nuna cewa "ana son yi masa sharri" ne.

Ga jerin ƙungiyoyin:

  • Safiyatul Islam of Nigeria‎
  • ‎Tijjaniya Youth Enlightenment Forum‎
  • ‎Interfaith Parties for Peace and Development‎
  • ‎Sairul Qalbi Foundation‎
  • Habbullah Mateen Foundation‎
  • ‎Imams of Juma'at Mosques under Qadiriyya Movement‎
  • ‎Committee of Sunnah Preachers, Kano‎
  • ‎Multaqa Ahbab Alsufiyya

An miƙa ƙorafe-ƙorafen ga Majalisar Shura

Bayan karɓar ƙorafe-ƙorafen ne kuma sai sakataren gwamnatin jihar ta Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, a madadin gwamnati, ya miƙa dukkannin ƙorafe-ƙorafen ga Majalisar Shura ta jihar Kano domin nazari sannan su bayar da shawara.

Majalisar Shura

Majalisar Shura ta Kano ta ƙunshi wakilai 12 daga ɓangarori daban-daban na addini da jagoranci kamar haka:

  • Wakilai uku daga ɗarikar Tijjaniyya
  • Wakilai uku daga ɗarikar Qadiriyya
  • Wakilai uku daga Salafiyya
  • Wakili ɗaya daga gwamnatin jihar Kano
  • Wakili daya daga fadar Sarkin Kano
  • Kwamishinan addinai na jihar

Mataimakin gwamna ya yi jawabi

A ƙarshen makon nan ne kuma Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a jawabinsa a wurin mauludin da Sheikh Bazullah Nasiru Kabara ya shirya, ya yi wani jawabin da wasu ke yi wa kallon ɗaukar ɓangare.

Mataimakin gwamnan ya yi hannunka mai sanda dangane da masu sakin baki a kan janibin Annabi Muhammad (SAW), inda ya ƙara da cewa "akwai siyasa a abin da ya faru a baya", wani abu da wasu suka fahimci cewa yana nuni da abin da ya faru da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda yanzu haka yake a gidan yari.

Martanin Gamayyar Ƙungiyoyin Ahlussunnah

Gamayyar ƙungiyoyin Ahlussunnah Wal-Jama'ah ta Kano sun mayar wa da mataimakin gwamnan na Kano marrtani dangane da kalaman da ya yi da suka ce na "ɓangaranci" ne.

A wani taron manema labarai da gamayyar ta yi ranar Litinin mai taken "Abin Ɓoye ya fito fili", malaman sun ce sun fahimci wasu abubuwa kamar haka daga kalaman mataimakin gwamnan kamar haka:

  • Ƙoƙarin siyasantar da aikin da malamai da alƙalai da kotun Shari'ar Musulunci suka yi na bayar da kariya ga annabi.
  • Sanya shakku kan ingancin fannin shari'a da alkalin kotun da ya yanke hukunci (kan Abduljabbar) wanda hakan bai dace ba ga shugaban da aka amincewa jagorantar al'umma.
  • Haddasa zato a zakutan al'umma da ke nuni da cewa gwamnati na da wata manufa ɓoyayya da ka iya kai wa ga sakin Abduljabbar ko kuma shafa wa wasu malamai kamar Sheikh Lawal Triumph kashin kaji da irin laifin da aka tuhumi Abduljabbar.